Abin da ya sa ake shan wahala wajen tura kuɗi ta intanet a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Tun daga lokacin da aka fara shirin komawa amfani da sababbin takardun kuɗi a Najeriya mutane suka fara kokawa kan rashin ‘network’ a lokacin tura kuɗi ko kuma samun su idan an turo masu ta hanyar intanet.
Wasu lokutan akan samu jinkiri ne wurin aiwatar da sakon kudin, a wani lokacin kuma abin ma ba ya yiwuwa, saboda wasu manhajojin bankunan kasuwancin kasar ba su buɗewa.
Hakan ya jefa al’umma da dama cikin garari kasancewar babu isassun kuɗi a hannun jama’a tunda Babban Bankin Najeriya (CBN) ya janye kimanin kashi 80% na tsofaffin takardun kudin bayan sauya fasalin takardun naira 1,000, da 500 da kuma 200.
Ko mene ne sanadiyyar matsalar da ake fuskanta wurin hada-hadar kuɗin ta intanet?
Mustapha Muhammad Garba masani ne kan harkokin kuɗi kuma tsohon manajan ɗaya daga cikin ressan bankin Unity a Najeriya, ya ce dalilan sun hada da:
Yunƙurin CBN na aiwatar da abu biyu a lokaci ɗaya

Mr Garba ya ce “tun farko ya kamata mutane su gane cewa abu biyu ne CBN ke kokarin yi a lokaci guda ”wato sauya fasalin kuɗi (Currency redesign), da kuma aiwatar da tsarin hada-hadar kudi ba tare da amfani da kudade a hannun jama’a ba (Cashless policy).
A cewarsa kowanne daga cikin waɗannan tsare-tsare biyu na da nauye-nauyen da yake tafe da su, lamarin da ya kara matsi a kan harkar banki na kasar ta Najeriya.
Ya ce "mutane sun ɗauka kawai sauya kuɗin za a yi, wato ‘currency swap’, misali, idan ka kai N100m tsofaffi a baka N100m sababbi."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Amma sai CBN ya shigo da batun ‘cashless policy’, abin da ya sanya ake kayyade yawan kudin da mutum zai iya cirewa daga asusun ajiyarsa a kullum."
Mr Garba ya ce “wannan abu shi ne ya janyo matsalolin da ake gani game da online transactions (hada-hadar kudi ta intanet).”
“A baya CBN ya ce kusan kashi 80% na kuɗin Najeriya ba su a bankuna, ma’ana ana amfani da su ne ke nan a hannun al’umma, amma yanzu kusan kashi 80% ɗin ne aka mayar cikin bankuna, wadanda ke nan dole sai dai a yi amfani da su ta hanyar hada-hada ta intanet.”
Ya ce CBN ya yi gaggawar fara aiwatar da tsare-tsaren a faɗin ƙasar "inda an bi tsarin da tsohon shugaban Babban Bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi ya fitar na aiwatar da shirin mataki-mataki, da abin ya zo da sauki."
A shekara ta 2012 ne Sanusi Lamido Sanusi ya kaddaamar da shirin hada-hada ba tare da kudi a hannu ba a Najeriya, inda ya zaɓi biranen Lagos da Abuja da kuma Port Harcourt a matsayin inda za a fara aiwatar da kashin farko.
Cunkoso

Asalin hoton, Getty Images
A cewarsa kokarin al’umma na yin biyayya ga tsare-tsaren biyu na CBN ya tura mutane da dama amfani da tsarin hada-hadar kudi ta intanet.
“Cunkoson mutanen da suka koma amfani da tsarin na hada-hada ta intanet ya sanya an yi wa hanyoyin gudanar da hada-hadar yawa.”
Ya kara da cewa “tamkar hanya ce da mutum 10 ke bi a baya, yanzu kuma sai aka ce mutum 100 ne za su bi.”
Rashin shiri

Masanin ya ce “ya kamata mutane su sani cewa a tsarin aikawa da kudi daga wani banki zuwa wani, akwai abin da ake kira ‘interface’ wato wata gada ko sila ko kuma mahada da ke sadar da bankuna daban-daban.”
Misalin irin wadannan mahada su ne NIBSS (Nigeria Inter-Bank Settlement System), da RTGS (Real Time Gross Settlement), da NEFT (National Electronic Funds Transfer), da kuma Interswitch.
Ya ce “a misali, a baya mutum 100 ne kawai suke amfani da waɗannan kafafe, yanzu kuma lokaci ɗaya sai aka samu mutum 1,000,000 na amfani da su a lokaci guda.”
“Kuma hakan na zuwa ne ba tare da an inganta kayan aiki ko na’urori na fasahar sadarwa da wadannan kafafe suke amfani da su ba, to dole ne a fuskanci matsaloli.”
End of Ƙarin labaran da za ku so ku karanta:
Ta yaya za a iya warware matsalar?
Mustapha Garba ya ce “ba matsala ce da za a iya magancewa cikin gaggawa ba.”
Domin ana bukatar shiri ta hanyar inganta tsarin da ake kai a yanzu.
Ya kara da cewa “a wasu bangarorin ana bukatar samar da sababbi kuma ingantattun kayan aiki na fasahar sadarwar zamani, abin da ba za a iya yi a rana guda ba.”
Haka nan wasu bankunan dole ne sai sun fara amfani da tsare-tsaren hada-hadar kudi ta intanet ko manhajoji masu inganci da za su iya daukar nauyin cunkoson al’umma da a yanzu suke rungumar tsarin hada-hadar kudi ta intanet.











