Ya za a yi da tsoffin kuɗin da za a sauya a Najeriya?

Takardun naira

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Laraba 26 ga watan Oktoban 2022 ne, Babban Bankin Najeriya ya sanar cewa zai sauya fasalin takardun manyan kuɗin ƙasar daga naira 200 zuwa sama.

Gwamnan bankin Godwin Emefiele ya ce za su yi hakan ne bisa buƙatar gwamnatin tarayya da kuma amincewar Shugaban ƙasar Muhammadu Buhari inda matakin, zai shafi takardar naira 200 da naira 500 da kuma naira 1000.

Bankin ya ce za a yi wannan sauyi ne domin rage yawan kuɗin da ke yawo a hannun jama'a da rage hauhawar farashi da kuma magance yin jabunsu.

A dangane da hakan ne bankin ya bukaci masu kuɗi a hannu su mayar da su bankuna cikin ƙasa da kwana 50.

Haka kuma CBN, ya ce ce sabbin kuɗaɗen da za a samar za su fara yawo a hannun mutane daga ranar 15 ga watan Disambar 2022.

Ya ƙara bayani da cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗaɗen har nan da ranar 31 ga watan Janairun 2023.

A shekarar 2014 Babban Bankin ya sauya takardar naira 100 domin murnar cikar Najeriyar shekara ɗari daya da Turawan mulkin mallaka suka haɗe kudanci da arewacin ƙasar a 1914.

Me zai faru bayan wa'adin da Bankin ya bayar ya ƙare?

Bayan wa'adin da bankin ya sa na 31 ga watan Janairun sabuwar shekara, mutane ba za su iya amfani da tsofaffin takardun kuɗaɗen ba kuma.

A bayanan da bankin ya bayar ya ce, dukkanin bankunan da ke da waɗannan takardun kuɗi a yanzu suna iya fara mayar da su CBN ba tare da ɓata wani lokaci ba.

Gwamnan bankin ya ce, duk bankin da ya fara kaiwa shi za a fara bai wa sabbin takardun.

Ya shawarci jama'a masu mu'amulla da bankuna waɗanda suke da kuɗaɗen a hannunsu da su fara kaiwa asusun ajiyarsu a bankunan domin a samu damar sauya su da wuri.

A sakamakon matakin ana sa ran dukkanin bankuna su bar cibiyoyinsu na tattara kuɗaɗe a bude daga Litinin zuwa Asabar, saboda wannan shi ne zai bayar da dama ga jama'a su mayar da kuɗaɗen a kan lokaci.

Domin hanzarta sauyin, Babban Bankin na Najeriya ya dakatar da cajin kuɗin da ake biya na ajiye kuɗaɗe a bankuna.

Tarihin kuɗin Najeriya

Takardun kudin Najeriya

Asalin hoton, OTHERS

  • 1880: Kuɗin farko na Najeriya shi ne na Shillings (Sulai) da Pence (Kwabo). Tsabar kuɗin wanda Babban Bankin Ingila ya samar shi ne na,

Sulai daya ( Kwabo 12) da 1 Penny wato Kwabo 1 da kuma 1/10, kuma bankin ƴan kasuwa mai suna Bank for British West Africa shi ne yake rarraba kuɗin har zuwa 1912.

  • Daga 1912 -1959: Hukumar samar da kuɗaɗe ta Afirka ta Yamma (West African Currency Board (WACB)), ta samar da takardun kuɗi da tsaba na farko ga kasashen Najeriya da Ghana da Saliyo da kuma Gambia. Kuma babbar takardar kuɗi ta farko ita ce, ta fan daya, yayin da sulai ɗaya shi ne tsabar farko babba a lokacin.
  • 1959: Babban Bankin Najeriya (CBN) ya samar da takardun kuɗin ƙasar na farko, yayin da ƙasar ta daina amfani da takardar kuɗi da tsabar da bankin kasuwancin na haɗakar Afirka ta Yamma WACB yake samarwa.
  • 1962: A wannan shekarar ne aka sauya yanayin kuɗin na Najeriya, ya nuna matsayinta na mai cin gashin kanta saɓanin a baya, lokacin da take ƙarƙashin mulkin Turawan Birtaniya. An sauya Kuɗin da ke ɗauke da rubutun ’FEDERATION OF NIGERIA‘, zuwa wanda aka rubuta ‘FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA’, a sama.
  • 1968: A wannan shekarar aka sake sauya takardar kuɗin saboda yadda aka saba amfani da su a lokacin yaƙin basasa.
  • 1973: An sauya sunan kuɗin Najeriya daga fan 1. An ɓullo da naira ɗaya wadda take daidai da sulai goma a matsayin babbar takardar kuɗin ƙasar. Yayin da ƙananan kuɗin da ake kira kwabo (kobo) guda ɗari ya zama naira ɗaya.
  • 1977: A wannan shekara aka ɓullo da sabuwar takardar kuɗi ta naira ashirin (₦20). A lokacin ta kasance takardar kuɗi mafi girma a ƙasar wadda Babban Bankin ya ɓullo da ita saboda bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar da kuma bai wa jama'a damar walwalar rike kuɗaɗe masu yawa ƴan kaɗan maimakon tilin takarda. A karon farko an sa hoton wani fitaccen ɗan ƙasar a kan takardar kuɗin.
  • 1979: An ɓullo da sabbin takardun kuɗi uku, na naira ɗaya da naira biyar da kuma naira goma (₦1, ₦5, ₦10). Domin mutane su iya ganewa tare da bambanta takardun an yi masu launi iri daban-daban. Sannan a bayan kowace takarda aka sanya hoton wasu abubuwa da ke nuna al'adun ƙasar.
  • 1984: An sauya dukkanin launin takardun kuɗin in banda takardar kobo 50 a cewar hukuma domin shawo kan yadda ake ficewa da kuɗin ƙasar waje a lokacin.
  • 1991: An sauya takardar kobo 50 da naira daya zuwa tsaba.
  • 1999: Domin abin da hukuma ta ce faɗaɗa harkokin tattalin arzikin ƙasar da sauƙaƙa cinikayya, aka ɓullo da takardun kuɗi na naira ɗaya da naira ɗari biyu da naira ɗari biyar da kuma dubu ɗaya ( ₦100, ₦200, ₦500 da ₦1000) a watan Disamba na 1999 da Nuwamban 2000 da Afrilun 2001 da kuma Oktoban 2005.
  • 2007: A matsayin wani ɓangare da sauye-sauyen tattalin arziƙi an bullo da takardar kuɗi ta naira ashirin ta leda a karon farko. Yayin da kuma aka sauya fasalin zanen naira hamsin da naira goma da naira biyar har da naira daya da kuma kobo hamsin, sannan aka bullo da tsaba ta kobo biyu.
  • 2009: Sakamakon irin amfanin da gwamnati ta ce ta gani dangane da sauya takardar kuɗin naira ashirin zuwa ta leda, sai ta sauya naira hamsin da goma da kuma naira biyar zuwa na leda. A yanzu dukkanin ƙananan takardun kuɗin ƙasar na leda ne.
  • 2010 da 2014: CBN, Babban Bankin Najeriya ya ɓullo da sabuwar takardar naira hamsin da ta naira ɗari domin bikin cikar Najeriya shekara 50 da zama ƙasa.