Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yunƙurin rushe masallaci mai shekara 700 a China ya jawo zanga-zanga
- Marubuci, Nicholas Yong
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Masu zanga-zanga sun yi arangama da 'yan sanda game da yunurin rushe wata ƙoƙuwar masallaci a garin Yunnan na China, wanda Musulmai suka fi rinjaye.
Bidiyon da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna dandazon mutane a wajen Masallacin Najiaying da aka gina tun a ƙarni na 13 - aƙalla shekara 700 da suka wuce - a ranar Asabar, wanda ke garin Nagu.
Lardin Yunnan mai ƙabilu daban-daban a kudancin China, na da adadin mabiya addinin Musulunci mai yawa.
China ba ta bin wani addini a hukumance kuma gwamnati na cewa tana ba damar 'yancin yin addini. Sai dai masu lura da al'amura na cewa ana yawan samun murƙushe mabiya addinai yayin da gwamnati ke son ƙarfafa ikonta.
A garin Nagu, Masallacin Najiaying na da muhimmanci sosai, har ma an sabunta shi da wata ƙoƙuwa, da sabon rufi, da kuma wurin kiran sallah.
Sai dai kuma wani hukunci da kotu ta yi a 2020 ya ayyana ƙarin a matsayin wanda ya saɓa wa doka kuma ta umarci a rushe shi. Yunƙurin aiwatar da umarnin kotun ne ya jawo zanga-zangar.
Bidiyo da hotunan da BBC ta tantance sun nuna 'yan sanda na hana mutane shiga masallacin a ranar Asabar, inda wasu mazaje ke ƙoƙarin kutsawa tare da wasu kuma suna jifan 'yan sanda da duwatsu.
Daga baya kuma an ga 'yan sandan na janyewa bayan mutane sun shiga masallacin.
Rundunar 'yan sandan Tonghai, inda garin Nagu yake, sun fitar da sanarwa suna umartar masu zanga-zanga su miƙa wuya ga 'yan sanda nan 6 ga watan Yuni.
An kama gwammai daga cikinsu zuwa yanzu.
"Waɗanda suka yi saranda da kansu kuma suka amsa laifin tayar da hankali za su iya samun sassauci," a cewar sanarwar.
Har yanzu ba a fiya yin zanga-zanga ba a China, amma an gudanar da wasu da dama tun bayan ɓarkewar annobar korona sakamakon dokokin kulle tsaurara da gwamnati ta ƙaƙaba.
Hui na ɗaya daga cikin ƙabilu 56 da gwamnatin China ta san da zamansu kuma akasarinsu Musulmai ne 'yan Sunna. Akwai 'yan ƙabilar Hui 700,000 daga cikin miliyan 10 da ke faɗin China.
Masu lura da lamurra na cewa China na son ƙarfafa iko kan ƙungiyoyin addini a shekarun baya-bayan nan - da kuma yadda suke ayyukansu a cikin al'umma.
A 2021, Shugaba Xi ya ci alwashin ci gaba da "jaddada aƙidar Chinanci a kan addinai" (Sinicisation of religion) - sauya aƙidu na addini zuwa al'adun China.
A 2018, ɗaruruwan Musulman Hui a yankin Ningxia sun sha gwagwarmayar hana rusa musu masallaci da gwamnati ke neman yi. Sun yi nasara amma sai da hukumomi suka tilasta musu sauya fasalin gininsa daga siffar gine-ginen Larabawa.
A shekarar dai, an rufe masallaci uku a Yunnan saboda abin da gwamnati ta kira "koyarwar addini da ta saɓa wa doka".
Ana zargin China da take haƙƙin Musulman Uyghur da ke arewa maso yammacin lardin Xinjiang, inda aka rushe masallatai kuma aka hana ayyukan ibada. Gwamnatin ƙasar ta sha musanta zarge-zargen.