Kayatattun hotuna daga wuraren shakatawa daban-daban

Tsuntsun hussen mai launi daban-daban

Asalin hoton, Andrew Fusek Peters

Bayanan hoto, Tsuntsun hussen kenan, ya bude fuka-fukan shi masu ban sha'awa, ya yin da ake iya ganin wani haske a fuka-fukan da suka bashi launi daban-daban.
    • Marubuci, فانيسا بيرس
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, بي بي سي نيوز
  • Lokacin karatu: Minti 2

Wani mai daukar hoto ya kwashe sama da shekara 10 yana zuwa wuraren shakatawa da lambuna a Birtaniya, ya ɗauki hotunan dabbobi kyawawa da kayatarwa.

Mai daukar hoton mai suna Andrew Fusek Peter, ya ce cikin hotunan da ya dauka sun hada da damben tsuntsaye, da na dabbobi da duk abin da ya gifta gaban shi da suka shafi dabbobi ko tsuntsaye.

Asalin hoton, Andrew Fusek Peters

Bayanan hoto, Wasu Jajayen squirrels suna wasan doke-doke a Isle of Wight
Zomo na shayar da danta

Asalin hoton, Andrew Fusek Peters

Bayanan hoto, Mai ɗaukar hoton, ya laɓe a wani sako da ke gandun dajin domin ɗaukar wannan hoto da ke nuna Zomo na shayar da ɗanta
Daya daga cikin hotuna masu ban sha'awa na tsuntsaye da mai daukar hoton ya dauka

Asalin hoton, Andrew Fusek Peters

Bayanan hoto, Tsuntsaye masu launin jiki mai ban sha'awa da suka yi kama da ɗan iccen blackberries, an ɗauki hoton ne lokacin da suke faɗa kan abinci.
Tsuntsu ne mai dogon baki da launin fari da baki, amma idan ya tashi sana ya ratsa hasken rana, launuka daban-daban na bayyana a fuka fusan shi

Asalin hoton, Andrew Fusek Peters

Bayanan hoto, Ana kiran wannan tsuntsun da mai tsintar nau'in gyadar hazelnut
An ce Barewa da danta ta ke wasa a dawa, haka lamarin ya ke ga Dila, a wannan hoton ana iya ganin yadda Uwa da danta ke wasa

Asalin hoton, Andrew Fusek Peters

Bayanan hoto, Dila da ɗanta a Clapham da ke kudancin Londo
Ana samun launuka daban-daban a jikin kwaron Agwalo mai tashi sama, ya na kama da fara amma ya fi ta girman fuka-fukai

Asalin hoton, Andrew Fusek Peters

Bayanan hoto, Wannan kwaron Agwalo ne, yana kamanceceniya da fara
Wannan nau'in tsuntsu ya yi fice wajen tsinko abubuwa, a wannan hoton tsuntsayen ne sukai layi kowanne dauke da abinci a bakinsa, za su kai shekar su da k saman wata bishiya

Asalin hoton, Andrew Fusek Peters

Bayanan hoto, Tsuntsun da ake kira flycatcher ko ɗan tsinta
Wannan nau'in beran ya shafe kwanaki a lambun mai daukar hoto Andrew, ta haka ne ya samu damar daukar shi hoto lokacin da ya ke shinshina furanni

Asalin hoton, Andrew Fusek Peters

Bayanan hoto, Ɓera