Dalilin da ya sa muka kai samame a Jihar Abiya - Sojin Najeriya

Rundunar Sojan Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa dakarunta sun far wa mazauna garin Amangu na Jihar Abiya da ke kudancin ƙasar, tana mai cewa ta kai samamen ne don neman sojanta da aka yi garkuwa da shi.

Cikin wata sanarwa kakakin rundunar sojin kasa, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya ce sun yi wa yankin tsinke ne sakamakon bayanan da suka samu cewa 'yan ƙungiyar tawaye ne na Indigenous People of Biafra (IPOB) suka sace sojan mai suna Saja Bassey Ikunugwan.

A ranar Laraba ne magoya bayan ƙungiyar ta IPOB suka zargi rundunar sojan da kai wa mazauna Amangu hari tare da iƙirarin cewa dakarun sun kashe fararen hula.

"Ganin irin girman zargin da ake yi mana, ya zama wajibi Rundunar Sojan Najeriya ta bayyana haƙiƙanin abin da ya faru yayin samamen," a cewar Janar Nwachukwu.

Ta ƙara da cewa ta yi nasarar kashe 'yan ƙungiyar uku a samamen da ta kai a sansanonin IPOB ɗin uku, amma an kashe mata soja ɗaya.

A watan Mayun da ya gabata ma sojoji sun zargi 'yan IPOB da fille kawunan sojoji biyu ango da amarya - Audu Linus da Gloria Mattew - a Jihar Imo.

Maharan sun kashe su ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa bikin aurensu na gargajiya.

'Yadda muka kashe 'yan IPOB a samamen ceto sojan'

Rundunar sojan ta yi zargin cewa an yi garkuwa da Saja Bassey Ikunugwan ne a ranar 2 ga watan Nuwamba a lokacin da yake cikin hutun aiki a yankin Okwu-Ebem da ke Jihar Abiya a kudu maso gabashin ƙasar.

Rundunar ta ce washegarin wannan rana ne kuma sojoji suka yi wa dajin Amangu tsinke da zimmar ceto abokinsu bayan sun samu bayanan sirri cewa maɓoyar 'yan IPOB ce da kuma mayaƙanta na ƙungiyar Eastern Security Network (ESN).

Kazalika a ranar 4 ga watan Nuwamban, dakarun da aka tura Okon Aku na jihar ta Abiya suka gamu da mayaƙan IPOB, inda suka kashe ɗaya daga ciki tare da ƙwace bindigar AK-47.

Kwana ɗaya bayan haka dakarun suka sake kai irin wannan samame a kan dajin Amangu. Wannan karon ma, a cewar sojojin, sun kashe 'yan IPOB biyu da kuma ƙwace AK-47 ƙirar gida guda biyu, da harba-ruga huɗu, da ƙaramar bindiga ɗaya, da babur ɗaya, da sauransu.

"Abin takaici, soja ɗaya ya rasa ransa yayin waɗannan samame," in ji rundunar.

'Ba za mu saurara ba sai mun ceto sojanmu'

Duk da samamen da ta kai kan sansanonin IPOB da take zargi da sace sojanta, zuwa yanzu rundunar ba ta kai ga ganowa ko kuɓutar da Saja Ikunugwan ba.

Sai dai ta yi gargaɗin cewa ba za ta saurara da nemansa ba har sai ta kuɓutar da shi.

"Sojin Najeriya ba za ta bar kowane lungu da saƙo ba sai ta bincka wajen ceto sojan da aka yi garkuwa da shi," kamar yadda sanarwar ta jaddada.

Daga cikin kayayyakin da rundunar ta ce ta ƙwace daga hannun mayaƙan IPOB sun ƙunshi kyamarar tsaro ta CCTV biyu, da akwatin zaɓe na INEC, da na'urar tantance masu kaɗa ƙuri'a, da katin zaɓe.

Sauran sun haɗa da faifan lantarki na sola, da tutocin ƙungiyar, da wayar oba-oba, da wayoyin salula, da takardun taken ƙungiyar, da akwatin rediyo, da sauransu.