Mahaifiyar da ta rasa 'ya'ya uku a jirgin da ya nutse da 'yan biki a Kwara

Dangin mutanen da suka mutu da waɗanda suka tsira a hatsarin jirgin ruwan da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 100 a jihar Kwara, da ke tsakiyar Najeriya sun fara bayani game da halin da suka shiga.

Wata mahaifiya da ta rasa 'ya'yanta, Aisha Mohammed, ta ce 'ya'yanta uku ne kuma 'yan mata da ke shirin yin aure, duk suka mutu a jirgin da ya nutse.

Matar ta ce 'ya'yan nata sun mutu ne, ana gab da zuwan aurensu.

A cewar shaidu akwai dangin da suka rasa makusanta har kusan goma.

Wasu da suka tsira sun yi bayani kan yadda wasu iyaye suka mutu lokacin da suka rirriƙe 'ya'yansu, suna ƙoƙarin tsamo su.

Matasa sun riƙa ninƙaya har suka kai gaɓa a lokacin da jirgin ya rabe gida biyu.

Mafi yawan matafiyan jirgin ba su da rigar hana nutsewa.

'Wasu uwaye sun nutse a ƙoƙarin kuɓutar da 'ya'yansu'

Ɗaya daga cikin mutanen da suka kuɓuta, Mohammed Hassan ya faɗa wa BBC cewa wasu daga cikin matan da suka mutu, sun taras da ajali ne a lokacin da suke ƙoƙarin ceto 'ya'yansu, ta hanyar riƙe hannayensu gam-gam, kuma suka ƙi saki har sai da suka nutse gaba ɗaya.

Shi ma wani mai suna Mohammed da ke cikin jirgin tare da 'yar'uwarsa ya ce "ɗan 'yar'uwar tasa mai shekara takwas ya mutu."

Ya zayyana kayan da ke cikin jirgin mai ɗauke kuma da mutane sama da 200.

"Akwai buhunhunan shinkafa da masara da gyaɗa da sumunti har 350 gaba ɗaya. Mutanen da ke cikin jirgin su 273 ne, ba su kai adadin buhunhunan shinkafar da ke ciki ba."

Wani basaraken yankin a Patigi, Liman Umar Muhammed ya ce iftila'in ya ƙazanta. Ya faɗa wa BBC Pidgin cewa wasu iyalan sun rasa makusantansu fiye da biyu a cikin jirgin.

"Akwai mutumin da ya rasa matansa biyu da 'ya'ya guda biyar, akwai kuma 'yan gida ɗaya su bakwai da suka rasu, har da waɗanda suka rasa makusantansu goma."

Ana ci gaba da aikin nema

Wani matashi ɗan sa-kai Umar Ahmed, wanda ya taimaka a aikin ceto ya shaida wa BBC cewa har yanzu suna ci gaba da aikin ceto a yanki. "Ana ci gaba da aikin neman gawawwaki da ceto masu sauran shan ruwa.

A cewarsa, suna gano gawawwakin da suka taso saman ruwa, inda ake fitar da su zuwa gaɓa.

Ya kuma ce a kwanakin da suka wuce, wasu mutane daga ƙauyukan da ke kusa na cikin ɗumbin masu aikin ceto a kogi.

A daidai lokacin da aka yi magana da shi, ya ce ba a samu tallafi daga hukumomin ba da agaji na gwamnati ba. "Tashin hankalin da al'ummar garuruwan yankin suka shiga yana da tsanani." In ji shi.

Tsawon fiye da kwana uku kenan yau, amma har yanzu al'ummomin yankin suna ci gaba da ƙoƙarin nemo makusantansu da ba a gani ba.

Alƙaluman da masu aikin ceto suka bayar a yankin, na nuna cewa mutum 144 ne suka kuɓuta a hatsarin jirgin kuma zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutum 106.

Ebo, ɗaya ne daga cikin ƙauyukan da aka fi samun mutanen da suka mutu. Mutanen yankin sun matafiya 61 ne daga ƙauyen Ebo suka mutu.

A cewarsu, akasarin mamatan mata ne da ƙananan yara.

Tinubu ya yi ta'aziyya

Tun da farko 'yan sanda a jihar Kwara sun ce fasinjoji kusan 300 ne a cikin jirgin ruwan da ya kife yana cikin tafiya a ranar Litinin.

Wata sanarwa da mai magana da yawun 'yan sanda, Mista Okasanmi Ajayi ya fitar, ta ce wani sashen jirgin daidai injinsa ne ya ɓarke, inda ruwa ya cika shi, har ya fara nutsewa.

“Cikin waɗanda suka mutu akwai mutanen ƙauyen Egbu su 61, sai mutum 38 daga ƙauyen Dzakan, ƙarin mutum huɗu daga Kpada ma sun mutum, akwai mutum uku daga jihar Kogi, inda ya sa jimillar mutanen da suka mutu ta kai 106," in ji shi.

Sai dai sarkin Patigi, yankin da hatsarin ya faru tun farko ya faɗa wa manema labarai cewa aƙalla mutum 150 ake fargabar sun nutse bayan kifewar jirgin a tsakiyar kogi.

Tuni dai Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin a kai kayan agaji da taimakon da ya wajaba nan take ga mutanen da suka kuɓuta da kuma dangi da iyalan waɗanda suka mutu a hatsarin jirgin ruwan Kwara.

Wata sanarwa daga daraktan yaɗa labarai ga shugaban Najeriyar, Abiodun Oladunjoye ta ambato Bola Ahmed Tinubu na cewa ya yi takaicin wannan hatsarin jirgin ruwa da ya kashe fiye da mutum 100 a jihar Kwara.

Ya kuma umarci gwamnatin jihar Kwara da sauran hukumomin gwamnatin tarayya da lamarin ya shafa su yi aiki tare don gano sanadi na kusa da na nesa da suka janyo aukuwar hatsarin jirgin ruwan.

Mai magana da yawun 'yan sandan, SP Ajayi Okasanmi ya ce nan gaba kaɗan za su wallafa sunayen mutanen da aka ceto.

Sai dai a cewar shugaban kwamitin aiwatar da shirin miƙa mulki a Patigi, Alhaji Mohammed Liman adadin fasinjojin da suka mutu a hatsari ya kai 110.

Ya ce: “Mutanen ƙauyenmu sun je ɗaurin aure ne kuma jirgin ruwan yana ɗauke da mutane kimanin 270.”

Wata sanarwa daga gwamnatin jihar Kwara ta ce jirgin na ɗauke da mutanen da suka fito daga garin Egboti na jihar Neja a kan hanyarsu ta zuwa Ƙaramar Hukumar Patigi a Kwara.