Abin da sabuwar dokar masarautun Adamawa ta ƙunsa

Gwamnan Adamawa

Asalin hoton, Ahmadu Umaru Fintiri/Facebook

Lokacin karatu: Minti 4

Majalisar dokokin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta amince da ƙudurin dokar kafa masarautu uku masu daraja ta ɗaya a jihar.

Amincewa da ƙundirin - wanda a yanzu ke jiran sa hannun gwamnan jihar, Ahmadu Finitiri - na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnan ya sa hannu kan wata dokar ta ƙirƙirar sabbin gundumomin hakimai 84 da aka yi ranar 4 ga watan Disamba.

A wata wasiƙa da gwamna da aika wa majalisar, a farkon mako ya buƙaci ƴanmajalisar su amince da ƙudirin naɗawa da cire sarakuna a jihar, wadda za ta ba gwamnan damar ƙirƙirar sababbin masarautu da naɗa sarakuna ko kuma cire su.

A cikin makon nan ne dai ƙudirin ya tsallake karatu na farko da na biyu a zauren majalisar jihar, inda yanzu ake jiran sa hannun gwamna domin ya zama doka.

Wannan na zuwa ne bayan salon da aka gani a wasu jihohin arewacin ƙasar, inda gwamnoni ke sauya dokokin masarautu domin ƙirƙirowa ko soke masarautun, wani abu da ake ganin yana rage ƙarfin gidajen sarauta masu daɗaɗɗen tarihi.

Abin da ƙudirin ya ƙunsa

Sabuwar dokar, za ta cire wa Lamiɗon Adamawa, Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, muƙaminsa na shugaban majalisar sarakunan jihar na dindindin, inda a yanzu muƙamin zai riƙa zagayawa tsakanin sarakunan jihar masu daraja ta ɗaya.

Dan majalisa mai wakiltar mazaɓar Numan, wanda ke cikin kwamitin da ya yi aiki kan ƙudirin, Hon. Mackondo Pwamawakeno, ya ce ƙudirin ba wani sabon abu ba ne, gyaran fuska kawai aka yi masa.

''Abin da kuma aka gyara mafi girma shi ne yadda za a riƙa zagayawa da muƙamin shugaban majalisar sarakunan Adamawa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kuma ya kare matakin, da cewa majalisar ta yi hakan ne domin tabbatar da adalci tsakanin sarakunan jihar.

''Idan a ce duk ni da kai matsayinmu ɗaya, kuma sai a ce ga muƙamin shugaban majalisar sarakuna, kullum kai ne za ka riƙe ni ba zan taɓa riƙewa ba, alhali matsayinmu ɗaya, an yi min adalci kenan?''

''Amma batun sauke basarake ko naɗawa ba sabon abu ba ne dama akwai shi tun asali, to ba sabon abu ba ne'', in ji shi.

Haka kuma ɗan majalisar ya ce ƙudirin ya kuma yi gyaran fuska kan yadda za a riƙa biyan albashin sakarakuna a jihar.

''A baya, ƙaramar hukuma ake tura wa kudin sarakunan da ke ƙarƙashinta ita kuwa ta aike da kudin majalisar sarakunan, wadda ita kuma za ta biya sarakunan, amma a yanzu an mayar da shi ƙarƙashin ma'aikatar ƙananan hukumomin wanda za ta riƙa biyan su sarakunan gargajiyar kai-tseye daga asusun gwamnatin jiha,'' kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Ya kare matakin ƙirƙiro sabbin sarakunan gargajiya masu daraja ta ɗaya da cewa ƙaruwar al'ummar jihar ce ta sa suka yi nazarin yin ƙudurin bai wa gwamna damar ƙirƙiro sabbin masarautun.

''Akwai wuraren da a baya babu jama'a, amma a yanzu sun zama manyan garuruwa to ka ga akwai buƙatar hakan, ba za mu ci gaba da amfani da dokokin 1960 zuwa 1980 ba har yanzu,'' a cewar ɗan majalisar.

Ya kuma ce doka ta bai wa gwamnan jihar damar ƙara masarautu matuƙar majalisar dokokin jihar ta amince masa.

Al'umma ne suka buƙaci hakan - Gwamnati

A nata ɓangare gwamnatin jihar Adamawan ta ce abin da majalisar ta yi na ƙirƙirar sabbin masarautun zai taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tsarin shugabanci da al'adun gargajiya a faɗin jihar.

Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou, ya shaida wa BBC cewa al'ummar jihar Adamawa da kansu ne suka bukaci hakan daga wajen gwamnatin jihar, sannan gwamnati ta yi nazari kan hakan kafin ta aika wa majalisar dokokin jihar.

Ya ce dokar ƙirƙiro sabbin masarutun ba ta je gaban gwamnan jihar ba, har yanzu tana a majalisar dokokin jihar, amma ya ce abu ne da al'ummar Adamawa suka nema da kansu.

''Ita kuwa gwamnati ta yi hakan ne domin kai gwamnati ko shugabancin kusa da muaten,'' in ji shi.

'Siyasa ce kawai'

Wani masani game da masarautar Adamawa, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya yi zargin cewa siyasa ce kawai ta sa aka ɗauki matakin.

''Duk wata hujja da za su faɗa koma-bayan siyasa, ba haka batun yake ba''.

Sai dai ya ce duk da rage wa wasu masarautun girman ƙasa, kamar yadda sabon ƙudirin ya tanada, hakan ba zai rage wa sarakunan waɗannan masarutun ƙarfin faɗa a ji a tsakanin al'ummomin masarautunsu ba.

A baya-bayan nan dai sauya dokar masarautun jihohi na neman zama ruwan dare a majalisun dokokin jihohin Najeriya.

A watan Mayu ne majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar gyaran masarutun jihar, inda gwamnan jihar ya ce ya mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano, kodayake har yanzu batun na gaban kotu, bayan dambarwar da ta biyo baya.

Haka ma a watan Yuni majalisar dokokin jihar Sokoto ta gabatar da wani ƙudirin gyaran dokar masarautun jihar, wani abu da shi ma ya ɗauki hankali a ciki da wajen jihar.