Pasalic ya koma Orlando City ta Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin karatu: Minti 1
Orlando City ta ɗauki ɗan wasan tawagar Croatia, Marco Pasalic ranar Laraba.
Mai shekara 24 ya koma Orlando daga HNK Rijeka kan yarjejeniyar kaka uku da cewar za a iya tsawaita masa zuwa karshen kakar 2028.
Pasalic ya ci ƙwallo 16 da bayar da tara aka zura a raga a karawa 68 tun daga 2023 zuwa 25 a ƙungiyar Rijeka.
Pasalic ya buga wa Croatia wasa biyar ya kuma wakilci kasar a gasar cin kofin nahiyar Turai da aka yi a 2024 a Jamus.
Orlando City za ta fara kakar bana ta tamaular Amurka da karɓar bakuncin Philadelphia Union ranar 22 ga watan Fabrairi.






