Emery zai ci gaba da horar da Aston Villa zuwa kaka biyar

Unai Emery

Asalin hoton, Getty Images

Kociyan Aston Villa, Unai Emery ya saka hannu don ci gaba da jan ragamar ƙungiyar Villa Park zuwa kaka biyar, kamar yadda mai buga Premier League ta sanar.

Ɗan kasar Sifaniya ya kai Aston Villa mataki na hudu a teburin Premier League a bana, hakan ya sa za ta buga Champions League a badi.

Emery ya sauya fasalin taka ledar Villa tun bayan da ya karbi horar da ƙungiyar a cikin Oktoban 2022 a lokacin da take da tazarar maki uku tsakani da ƴan ukun karshen teburi.

Mai shekara 52, ya koma Villa da burin kai ƙungiyar gasar zakarun Turai, wanda ya lashe Europa League hudu, bayan ƙwazon da ya yi a Sevilla da Villarreal.

Ya kuma dauki Ligue 1 a Paris St Germain, yana kuma da ƙwarewa kan yadda Premier League take, bayan da ya yi kaka daya a Arsenal a 2018-19.

Ya ja ragamar Villa zuwa mataki na bakwai a Premier League a 2023, yanzu kuma ta kammala a matsayi na hudu da za ta buga gasar Turai karon farko bayan 1983.

Kawo yanzu akwai masu horar da tamaula da yawa dake neman aiki, amma ƙungiyar Villa ta amince ta ci gaba da aiki da Emery zuwa lokaci mai tsawo.

Emery ya sanar cewar ""Ina murna da wannan yarjejeniyar da muka kulla, sannan da wannan nauyin da aka dora min na jan ragamar ƙungiyar.''

''Tun bayan da na koma Villa na samu mahukuntan ƙungiyar Wes (Edens) da Nassef bisa tsarin da ya dace na kai ƙungiyar matakin da ya kamata.

Villa ta kai quarter finals a Europa League a bana, sai dai Olympiacos ce ta yi waje da ita daga gasar ta zakarun Turai.