Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Ukraine ta zama cibiyar da mata ke renon cikin da ba nasu ba
- Marubuci, Sofia Bettiza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, World Service Global Health Reporter & BBC News Ukrainian
- Aiko rahoto daga, Kyiv
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Karina tana da juna biyu na watanni shida, amma jaririn da ke cikin mahaifarta ba nata ba ne.
Wannan matashiyar mai shekaru 22 daga gabashin Ukraine tana aikin renon cikin wasu (surrogacy). Tana dauke da cikin da aka samar daga ƙwai da maniyyin wasu ma'aurata daga China.
Tun tana da shekara 17, rayuwarta ta shiga rudani lokacin da garinsu Bakhmut ya zama ɗaya daga cikin wuraren da aka fi fafata yaƙi a farkon mamayar Rasha a ƙasar Ukraine. Yaƙin ya yi sanadin rusa gidaje da dama, ya maida garin cikin toka da ɓaraguzai.
Daga baya, ta koma Kyiv tare da mijinta, amma rayuwa ta ci gaba da mata wahala. Ba su da wani tsayayyen aiki, kuma ga su cikin tsananin talauci. Lokacin da take aiki a wani shago, tana samun kuɗin da bai isarta siyan ko da burodi da pampers ga yarinyarsu 'yar shekara ɗaya da rabi, sai ta yanke shawarar shiga aikin renon cikin wasu domin biyan buƙata.
Karina ta ce ba ta taɓa tunanin shiga wannan harkar ba, sai dai yaƙi ne ya tilasta mata. Yaƙin ya jawo asarar ayyuka, rugujewar kasuwanci, hauhawar farashin kaya, da kuma taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar Ukraine.
"Da farko, na ji haushi da takaici game da zama mai renon cikin wasu. Amma yanzu na riga na saduda da halin da nake ciki," in ji Karina Tarasenko, wadda ke zaune a kusa da birnin Kyiv a wani gida da kamfanin da ke kula da ita ya ba ta. Tana ɗauke da juna biyu na 'ya mace.
Za ta samu kusan fam 12,500 kimanin dala 17,000 kenan, wanda ya ninka matsakaicin albashi na tsawon shekara a Ukraine. Sai dai mafi yawan kuɗin za ta karɓe su ne bayan ta haihu.
A da an tsara za ta karɓi kusan fam 15,500 kimanin dala 21,000 , amma bayan ɗaya daga cikin tagwaye da take ɗauke da su ya rasu, an rage mata albashi kamar yadda aka aminta a cikin yarjejeniya tun da farko.
Duk da cewa da farko tana tababa, yanzu Karina na shirin ci gaba da aikin renon cikin wasu da dama muddin jikinta zai iya jurewa, domin ta tara kuɗin da za ta sayi gida.
Sai dai makomarta na iya canzawa nan ba da jimawa ba.
Kafin yaƙin Ukraine, ƙasar na daga cikin manyan cibiyoyin kasuwancin renon cikin wasu (surrogacy) a duniya, inda aka ce ita ce ta biyu bayan Amurka.
Masana sun shaida wa BBC cewa duk da yaƙin da ya kawo cikas, harkar renon cikin wasu a Ukraine ta kusa komawa kamar yadda take kafin yakin.
A yanzu haka, majalisar dokokin Ukraine na duba wani ƙudiri da zai tsaurara dokoki kan wannan lamari, inda zai taƙaita ko hana baƙi daga ƙasashen waje amfani da tsarin. Rahotanni na nuna cewa kusan kashi 95 na masu neman jarirai ta wannan hanya daga ƙasashen waje suke. Ƙudirin na samun goyon bayan yawancin 'yan majalisa.
Manufar dokar ita ce ƙara kula da yadda ake gudanar da tsarin, wanda ake zargi da mayar da haihuwa tamkar wani nauyi da kuma cin gajiyar mata masu ƙaramin ƙarfi. Wasu 'yan majalisa na kuma ganin bai dace mata 'yan Ukraine su riƙa renon cikin baƙi ba a lokacin da yawan haihuwa ya ragu sakamakon yaƙin, duk da cewa jariran da ake haifa ta hanyar ba su da yawa idan aka kwatanta da jimillar haihuwa a ƙasar.
Mai fafutukar kare haƙƙin mata, Maria Dmytrieva, ta ce yaƙin ya ƙara yawan mata da ke cikin matsanancin hali, cibiyoyi na amfani da wannan yanayi wajen ɗaukar su aiki, yayin da masu neman jarirai daga ƙasashen Yamma ke nema a "arha".
Ta ce ya kamata a haramta wannan tsarin gaba ɗaya a Ukraine.
Ta kuma zargi cibiyoyin renon cikin da yin tallace-tallace kai tsaye ga mata talakawa, musamman ta kafafen sada zumunta.
A watan Janairu, an yi wani talla da aka ƙirƙira da AI da ke nuna wata mata da ke cikin wani yanayi mai wahala tsakanin sayen itacen ɗumama gida ko kayan yara, domin nuna matsin rayuwa a lokacin yaƙin.
Haka kuma a 2021, babbar cibiyar surrogacy ta Ukraine, BioTexCom, ta yi tallan samun rangwame ga wanda yake son ayi masa renon ciki.
Lokacin da BBC ta tambaye ta, BioTexCom ta kare tallar, tana cewa manufarta ita ce jawo hankali kan batun renon cikin.
Cibiyar renon cikin ta BioTexCom ta sha suka kan yadda take gudanar da ayyukanta. A shekarar 2018, ofishin masu gabatar da ƙara a Ukraine ya fara bincike kan shugaban kamfanin, Albert Tochilovsky, da wasu tsofaffin ma'aikata biyu bisa zargin laifuka ciki har da safarar mutane.
Masu gabatar da ƙarar sun ce an dakatar da binciken na wucin gadi domin samun haɗin kai daga ƙasashen waje da kuma tattara ƙarin bayanai.
Sai dai BioTexCom da Tochilovsky sun musanta zarge-zargen gaba daya, inda suka ce a ko da yaushe suna aiki ne bisa doka.
Ofishin masu gabatar da ƙara bai bayyana cikakken bayani kan zargin safarar mutanen ba, amma BioTexCom ta shaida wa BBC cewa matsalar ta shafi rashin daidaituwar DNA tsakanin wasu iyaye da wani jariri ne. Kamfanin ya ce ma'aikatansa ba su da laifi, kuma suna zargin matsalar ta faru ne yayin karɓar maniyyi a wata ƙasa daban.
Kamfanin ya ce yana taimaka wa mutane su cika burinsu na zama iyaye, yayin da yake bai wa mata damar samun kuɗi ta halal tare da samar musu da kulawar lafiya da masauki da abinci.
Karina ta ce tun farko ta tuntubi BioTexCom domin ta reni cikin wasu, amma daga baya ta fasa bayan ta ji ma'aikatan cibiyar sun yi mata mu'amala cikin rashin kulawa a farkon ganawarsu.
Ana watsar da yara
Akwai kuma lokutan da ake barin jariran da aka haifa ta hanyar renon cikin wasu bayan iyayen da suka nemi haihuwar sun canza ra'ayi.
A Ukraine, doka ta ɗora wa iyayen da suka nemi a haifa musu yaro alhakin kula da shi bayan haihuwa, kuma haramun ne su yi watsi da shi saboda kowace irin matsala. Sai dai aiwatar da wannan doka tsakanin ƙasashe na da wahala.
Wei mai shekara biyar yanzu yana fama da matsananciyar lalurar ƙwaƙwalwa bayan an haife shi da wuri a shekarar 2021 ta hannun BioTexCom. Yanzu haka yana rayuwa a wata cibiyar gwamnati ta kula da yara masu nakasa a Kyiv.
Wei ba ya iya zama da kansa ko riƙe kansa, kuma ba ya gani sosai. Likitoci sun ce zai buƙaci kulawa ta musamman har ƙarshen rayuwarsa.
Bayan iyayen da suka nemi a haife shi sun gano halin da yake ciki, sai suka ƙi zuwa su karɓe shi, kuma suka tsere ba tare da an sake jin duriyarsu ba. Mahaifiyar da ta reni cikin ma ta ƙi karɓarsa, domin a ƙarƙashin dokar Ukraine ba ta da alhakin yaron.
Jami'ar lafiya ta Ukraine, Valeria Soruchan, ta ce yara da dama da aka haifa ta wannan hanya ana barinsu, duk da cewa gwamnati ba ta da cikakkun alƙaluma.
Shugaban BioTexCom Albert Tochilovsky ya bayyana lamarin a matsayin "babbar masifa", yana mai cewa kamfanin na ɗaukar wani ɓangare na alhakin idan aka bar yara.
Sai dai babu wata doka da ta tilasta wa cibiyoyin renon ciki biyan kuɗin kula da irin waɗannan yara, kuma har yanzu BioTexCom ba ta bayar da gudunmawa wajen kula da Wei ba.
Saboda tsananin nakasar da Wei ke da ita, har yanzu babu iyalin da suka amince su ɗauke shi duk da cewa iyalai 15 sun duba bayanansa.
"An biya mana burimu na damar zama iyali"
Duk da cece-ku-cen da ake yi kan renon cikin wasu, wasu ma'aurata na ganin tsarin yana amfanar mutane.
Himatraj da matarsa Rajvir Bajwa daga London sun shafe shekara biyar suna neman haihuwa ba tare da nasara ba, har da gwajin dashen ciki sau biyu. Matarsa mai shekara 38 na fama da lalurar nakasa da aka kira da endometriosis da kuma multiple sclerosis, waɗanda suka sa samun ciki ya yi mata wahala.
Ma'auratan sun ƙi yin tsarin surrogacy a Birtaniya saboda dokar ƙasar ta ba uwa mai renon cikin ikon doka a kan jariri har sai an kammala wasu takardu. Sun ce hakan ya ba su tsoro saboda akwai lokutan da wasu mata kan canza ra'ayi su ƙi ba da jariri, ko da yake hakan ba kasafai yake faruwa ba.
Daga baya ne suka zaɓi Ukraine, inda suka biya kusan fam dubu 65 wajen amfani da kamfanin BioTexCom, kuɗin da ya yi ƙasa da na Amurka.
Sun samar da jariri ta hanyar dashen ciki wato IVF a London sannan aka kai shi Kyiv. A watan Yunin bara suka je Ukraine domin haihuwar ɗansu, amma suka shafe watanni uku a Kyiv suna jiran takardun tafiya yayin da hare-haren Rasha ke ci gaba.
Rajvir ta ce rayuwar ta kasance mai ban tsoro saboda yawan hare-haren bam da ake kai wa ƙasar.
Yanzu suna ganin tsarin ya canza rayuwarsu. Himatraj ya ce: "Sun ba mu abin da ba mu taɓa tunanin zai yiwu ba, sun sa mun samu iyali."
'Babu wanda ke tilasta mana'
Karina ma ta yi watsi da ra'ayin cewa renon cikin wasu cin zarafi ne ga mata.
"Babu wanda ya tilasta mana. Jikina ne kuma ra'ayi na ne... Zan samu lada saboda na taimaka wa wasu su samu farin ciki," in ji ta.
Ta ce tana adawa da sauya dokar saboda hakan zai rushe shirinta na sayen gida gaba ɗaya.
Da take kallon cikinta, Karina ta ce: "Na san wannan ba ɗiyata ba ce, amma ina sonta. Ina magana da ita. Idan tana motsi a ciki, ina gaya mata cewa iyayenta suna jiranta.
"Abin da kawai nake fata shi ne ta samu rayuwa mai kyau."