Waɗanne ƙasashen Larabawa ne ke ɗasawa da Isra'ila?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Wakilan ƙasashen Isra'ila da Lebanon za su haɗu domin su tattauna a ranar Alhamis a birnin Washington, sannan su sake wata tattaunawar a ranar Juma'a a ƙarƙashin jagorancin Amurka.

Wannan na zuwa ne bayan wata tattaunawar da aka yi a ranar 23 ga wata Afrilu, wanda shugaban Amurka Donald Trump ya jagoranta.

Amma duk da yarjejeniyar tsagaita da Amurka ta jagoranta ta ranar 16 ga Afrilu, Isra'ila a Hezbollah sun cigaba da yaƙi, musamman a kudancin Lebanon. Haka kuma Isra'ila ta kashe kwamandan Hezbollah a ranar 6 ga Mayu a Beirut.

Da farko an tsara tsagaita wutar ce ta yi kwana 10, sannan aka tsawaita ta da mako uku domin ta ƙare a ranar 17 ga Mayu.

How did we get here?

Zagaye na uku n tattaunawar ne za a fara a ranar Alhami, wanda ma'aikatar harkokin wajen Amurka za ta jagoranta a Washington, sana bayan tattaunawar wakilan za su gana da shugabannin ƙasashensu kafin sake zama a ranar Juma'a.

A ranar 23 ga ce ɓangarorin biyu suka yi tattaunawar ƙarshe a fadar White House, inda bayan ganawar Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tsagaita wuta ta mako uku.

Ya kuma bayyana cewa zai gana da Firaministan Isra'ila Benjami Netanyahu da Shugaba Lebanon Joseph Aoun a Washington.

Sai dai har yanzu ba yi wannan tattaunawar ba. Shugaba Aoun ya ce dole a tabbatar da tsarin tsaro na musamman, sannan dole Isra'ila ta dakata da hare-hare kafin taron.

A ranar 14 ga Afrilu, wakilan ƙasashen Lebanon da Isra'ila sun yi ganawa ta farko a cikin shekara 30 domin lalubo hanyar kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila da Hezbollah mi samun goyon bayan Iran, inda aka amince a tsagaita wutar har na tsawon shekara biyu.

Ambasadan Isra'ila a Amurka, Yechiel Leiter da takwaransa na Lebanon, Nada Hamadeh Moawad sun gana a Washington a ƙarƙashin jagorancin sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, wanda shi ne karo na farko tun daga 1993.

Yaya batun Hezbollah?

An ƙirƙiri ƙungiyar Hezbollah ne a shekarar 1982, kuma ƙungiya ce mai ƙarfi musamman a kudancin Beirut da mabiya Shi'a suka fi yawa.

Akwai masu alaƙa da ƙungiyar sun kasance suna shiga ana damawa da su a harkokin gwamnati, kuma ko a gwamnatin yanzu akwai ministoci biyu.

Alaƙa tsakanin Hezbollah da gwamnatin Lebanon ta ƙara tsami ne tun bayan da yaƙi ya ɓarke a tsakanin Isra'ila a Iran.

Hukumomi a Isra'ila sun ce yaƙin Gaza ya matuƙar karya lagon Hezbollah, amma wasu bayanan sirri da jaridar Haaretz ta Isra'ila ta bankaɗo ya nuna cewa har yazu da ƙarfinta, kuma za ta iya cigaba da yaƙi musamman a kudancin Lebanon.

A makon jiya ne Isra'ila ta ce ta kahe Ahmed Ali Balout, wanda shi ne kwamanda sashen sojin Hezbollah mai suna Radwan a wani hari da ke kai a kudancin Beirut.

Daga bisa jami'in Hezbollah ya tabbatar da mutuwar, kuma harin ne a farko da Isra'ila ta kai tun bayan yarjejeniyar tsagaita da ka shiga a 16 ga watan Afrilu.

Haka kuma dakarun Isra'ila sun cigaba da rushe ƙauyuka a kudancin Lebanon, ina ƙasar ta ce burinta shi ne ta kare arewacin Isra'ila daga kutsen mayaƙan Hezbollah.

Hezbollah ta fara harba da rokoki da jirage marasa matuƙa zuwa Isra'ila ne bayan yaƙin ya ɓarke a raar 2 ga Maris.

A lokacin da aka sanar da tsagaita wutar a ranar 16 ga Afrilu, sai Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce raba ƙungiyar da makamai ne ya fi muhimmanci a batun shiga tsagaita wuta.

Ita dai Hezbollah ta yi watsi da wannan buƙatar, inda ta nanata cewa kamata ya yi makomar makamanta ta kasance ta hanyar tattaunawa bayan yaƙin.

Ita kuma Iran ta buƙaci a tsara hanyar tabbatar da dawwamammen zaman lafiya ne kafi a shiga batun tsagaita wuta, inda ta dage kan ƙin amincewa da shiga yarjejeniyar kamar yadda Trump ya tsara.

An kashe aƙalla mutum 2,896 aga farkon yaƙin zuwa yanzu, kamar yada ma'aikatar lafiyar Lebano ta bayyana, sannn an rab kusan mutum miliyan 1.2 da muhallansu, sai dai alƙaluman ba sa bambanta sojoji da fararen hula.

Ita kuma Isra'ila ta ce an kashe mata sojoji 18, da fararen hula huɗu a tsakankanin lokacin.

Me ya sa Isra'ila da Lebanon ba su alaƙar diflomasiyya?

Isra'ila da Lebanon sun kasance cikin yaƙi ne tun a 1948 lokacin da Lebanon ta shiga cikin ƙasahe Larabawa da suke adawa da samar da ƙasar Isra'ila.

Dalilan sun haɗa da:

Rashin yarjejeniyar zaman lafiya: Ba kamar Masar da Jordan, Lebanon ba ta shig yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila.

Yaƙi da tallafi: Yaƙin basasar Lebanon da sa hannun Isra'ila ya ƙara lalata dangantaka a tsakaninsu. Isra'ila ta mamaye kudancin Lebanon tun daga 1982 zuwa 2000.

Rawar Hezbollah: Tun a tsakankanin 1980s, Hezbollah ta kasance ƙungiya mai ƙarfi da take iya fuskantar Isra'ila daga Lebanon. Ira'ila na kallon ƙungiyar a matsayin babbar maƙiyarta, ita kuma ƙungiyar tana watsi da kasancewar Isra'ila.

Dokoki: A hukumance Lebanon ta ayyana Ira'ila a matsayin maƙiy, ita ma Isra'ila tana matsa lamba kan shigar ƴan Lebanon ƙasarta.

Waɗanne ƙasashe Larabawa ne ke goyon bayan Isra'ila da waɗanda ba sa yi?

Zuwa watan Mayun 2026, ƙasashen Larabawa shida ne suke da alaƙar diflomasiyya da Isra'ila:

Masar (1979)

Jordan (1994)

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (2020)

Bahrain (2020)

Morocco (2020)

Sudan (2020)

Babu ƙasar da ke cikin yarjejeniyar Abraham wato Haɗɗɗiyar Daular Larbawa da Bahrain da Morocco da Sudan da suka janye daga yarjejeniyar tu bayan ɓarkewar yaƙin Gaza a watan Oktoban 2023, duk da cewa akwai waɗanda suka nuna goyo baya da Falasɗinawa.

Waɗanne ƙasashen Larabawa ne ba su da alaƙa da Isra'ila?

Yawancin ƙasashen Larabawa har yanzu ba su da alaƙa mai kyau da Isra'ila. Su ne:

Lebanon

Syria

Saudiyya

Kuwait

Iraq

Qatar

Algeria

Libya

Yemen

Oman (wadda suke tattaunawa, amma babu alaƙa a hukumance)

Ƙasashen Larabawa da dama na bayyana rashin amincewa da Falasɗinu da mamayar Isra'ila a Gaza a matsayin dalilin rashin shiga diflomasiyya da Isra'ila.

Saudiyya ta fara yunƙurin samun maslaha da Isra'ila ke nan aka fara yaƙin Gaza, inda Saudiyya ta ce za ta cigaba da yunƙurin ne kawai bayan an samu maslaha kan amincewa da ƙasar Falasɗinu.