Ziyarar da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya kai birnin Beijing a makon da ya gabata ta ƙara fito da irin tasirin da China ke da shi a yankin Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun nuna cewa Amurka na sanya ido sosai kan wannan al’amari, musamman dangane da yadda China ke hulɗa da Iran a lokacin da rikici ke ƙaruwa a yankin.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce yana fatan China za ta faɗa wa Iran abin da ya kamata ta sani.
“Ina fatan China za ta gaya masa abin da ya kamata a faɗa, wato abin da suke yi a mashigar Hormuz ya sa duniya ta ware su. Su ne ake gani a matsayin masu laifi a wannan rikicin,” in ji Rubio.
Shi ma Ali Wine, babban mai ba da shawara kan hulɗar Amurka da China a ƙungiyar International Crisis Group, ya ce Amurka ta fahimci cewa China za ta taka muhimmiyar rawa idan ana son dawo da Iran teburin tattaunawa cikin hanya mai ɗorewa.
“Ina ganin Amurka ta fahimci cewa idan ana son dawo da Iran kan teburin sulhu ta hanya mai ɗorewa na dogon lokaci, to lallai China za ta taka rawa,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, shugaban Amurka Donald Trump ya nuna kamar ba ya damuwa sosai da kusancin da ke tsakanin China da Tehran.
Ko da yake Amurka ta kakaba wa wani matatar mai da ke China takunkumi saboda safarar man Iran, Trump ya rage muhimmancin duk wata goyon bayan da China ke bai wa Iran yayin rikicin.