An yi jana'izar shugaban mayaƙan Hamas da aka kashe a Gaza.
An gudanar da jana'izar shugaban mayaƙan Hamas Izzal-Din al-Heddad, a Gaza.
Ya rasu ne bayan wani harin da Isra'ila ta kai birnin Gaza a jiya Juma'a.
Al-Heddad mai shekaru 56 ya shafe kusan shekaru 40 a Hamas, inda ya jaronci sassa da dama na ƙungiyar.
Ana zaton matarsa da ɗiyarsa mai shekara 9 na daga cikin mutanen da Isra'ila ta kashe a harin.
Tun daga shekarar da tagabata Al-Heddad ke jagorantar mayaƙan Hamas, kuma rahotanni na cewa yana daga cikin shugabannin ƙungiyar da suka daɗe Isra'ila na nema.