Abin da ya kamata ku sani kan zaɓukan fitar da gwanin APC

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta fara gudanar da zaɓukan fitar da gwani na waɗanda ke son tsaya mata takara a zaɓukan 2027 da ke tafe.

Hukumar zaɓen ƙasar INEC ta ƙayyade ranar 30 ga watan Mayun da muke ciki a matsayin wa'adin ƙarshe na fitar da ƴan takara a kowace jam'iyya.

Tun da farko APC ta tsara fara zaɓukan fitar da gwanin a ranar Juma'a 15 ga watan Mayu, amma saboda wasu dalilai ta ɗage zuwa Asabar.

Jam'iyyar za ta fara zaɓukan fitar da gwanin ne da ƴan takarar majalisar wakilai na tarayya a ranar Asabar.

Hukumar zaɓen ƙasar, INEC ta tanadi hanyoyi biyu na fitar da ƴantakara ga kowace jam'iyya, kamar yadda sabuwar dokar zaɓen ƙasar ta 2026 ta tanada.

Hanya ta farko ita ce maslaha, wadda ƴantakara za su janye wa daya bisa amincewarsu da goyon bayan jagororin jam'iyya a kowane mataki.

Idan hakan ya gagara sai a je hanya ta biyu wato ƴartinƙe, wadda ƴan jam'iyya za su fita domin zaɓen wanda suke so ya tsaya wa jam'iyyarsu takara.

A baya idan maslahar ba ta samu ba, akan yi amfani da tsarin wakilai da ake kira dalaget, domin zaɓen ƴantakarar.

A ina za a yi zaɓen ƴartinƙen?

Dangane da wurin da za a yi zaɓukan kuwa Mallam Bala Ibrahim Daraktan yaɗa labaran jam'iyyar ya ce za a gudanar da su ne a kowane akwatin zabe.

''Ai zaɓen ka iya ce masa ƙaramin babban zaɓe, domin za a gudanar da shi ne a kowace akwai, sai in wurin da aka cimma maslahar fitar da ƴantakara'', in ji shi.

Mallam Bala ya ƙara da cewa duka zaɓukan na ƴanmajalisar wakilai da sanatoci da kuma na gwamnoni za a yi su ne a kowace akwati.

A makon da ya gabata ne dai jam'iyyar ta kammala tantance sunayen mutanen da za su tsaya mata takara a matakai daban-daban.

Bayanai na cewa APC ta tantance kimanin ƴantakara 2,500 da za su tsaya kujeru daban-daban ƙarƙashin inuwar jam'iyyar.

Daga ciki fiye da mutum 800 ne suka sayi fom ɗin takarar majalisar wakilai a jam'iyyar.

Bayanai na cewa manyan jiga-jigan jam'iyyar da gwamnoninta sun fi son amfani da maslaha wajen zaɓen ƴantakarar majalisar wakilan 360, amma kuma hakan bai samu ba, saboda mafi yawan ƴantakarar sun ƙi amincewa da matakin.

'Waɗanda za su yi zaɓen da yadda za a yi shi'

Mallam Bala Ibrahim ya ce waɗanda za su yi zaɓukan na fitar da gwani a APC su ne halastattun ƴan jam'iyya.

''Sai waɗanda suke riƙe da katin jam'iyya ne, kuma aka tabbatar suna biyan haƙƙoƙin jam'iyya ne kawai za su iya yin zaɓen'', in ji shi.

Ya ci gaba da cewa akwai masu tantance waɗanda za su yi zaɓen, kuma babban abin da za a yi la'akari da shi shi ne wanda ke riƙe da katin jam'iyyar.

''Domin akwai rajistar da ke ɗauke da sunayen ƴaƴan jam'iyyar da suka yi rajista a kowace mazaɓa, don haka duk wanda ya nuna katinsa, to za a tantance, kafin ba shi damar yin zaɓen'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Abin da dokar zaɓe ta tanada game da zaɓen ƴartinƙe shi ne kowane ɗantakara zai tsaya, sai waɗanda ke goyon bayansa su tsaya a bayansa, daga nan sai a ƙirga na kowane domin a tabbatar da wanda ya yi nasara.

Fitattun ƴanmajalisar da suka samu takara ta maslaha

Tuni dai wasu ƴantakarar suka samu damar samun takarar kai-tsaye ta hanyar amfani da hanyar maslaha.

Don haka su yanzu abin da ke gabansu shi ne shirye-shiryen fara yaƙin neman zaɓe, idan lokacin da INEC ta sanya don yin hakan ya cika.

Daga cikin fitattun ƴanmajalisar da suka samu takarar kai-tsaye ta hanyar maslaha akwai.

Kakakin majalisar wakilan, Hon. Tajudeen Abbas da ke neman wa'adi na biyar a majalisar, da mataimakinsa, Banjamin Kalu da ke neman wa'adi na uku da kuma Aliyu Muktar Betara daga jihar Borno da ke neman wa'adi na biyar da Abdulmumin Jibrin Kofa da Alhassan Ado Doguwa daga jihar Kano.

Saƙon Tinubu game da zaɓen fitar da gwanin

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi kira ga ƴan jam'iyyar tasa ta APC su fita domin kaɗa ƙuri'a a zaɓen fitar da ƴantakarar da za su wakilci jam'iyyar a babban zaɓen ƙasar, inda ya buƙace su da gudanar da zaɓen cikin lumana.

"Mun assasa APC ne domin ci gaban al'umma da haɓaka dimokuraɗiyya da sadaukarwa. Wannan sadaukarwar ta taimaka mana wajen zama tsintsiya, don haka akwai buƙatar mu cigaba da ɗabbaƙa ta," in ji shi.

Ya ce zaɓe na cikin manyan ginshiƙan dimokuraɗiyya, sannan ya yi kira da a gudanar da zaɓen fitar da ƴantakarar a matsayin ƴan'uwa.

"Dukkan ƴantakara da masu zaɓe dole su tabbatar da zaman lafiya, sannan su fifita muradun jam'iyyar da ma ƙasar baki ɗaya. Dole a kowace takara akwai wanda zai yi nasara, da wanda zai yi rashin nasara. Ina fata dukkansu za su dunƙule su yi aiki tare."

Tinubu ya kuma yi kira ga waɗanda za su yi nasara da su yi haƙuri su raka waɗanda suka yi nasarar, domin a cewarsa, " wanda ya yi nasara shi ne wanda ya yi haƙuri ya jira wani lokaci, ba wanda zai fasa kowa ya rasa ba."

Shugaban ya kuma ce waɗanda suka yi nasara ya kamata su ja kowa a jiki, "mu guji siyasa a mutu ko a yi rai wadda aka wuce lokacinta."