Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dokar tilasta wa masu zafin ra'ayin Yahudanci shiga soja na kawo ruɗani a Isra'ila
- Marubuci, Lucy Williamson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Gabas ta Tsakiya
- Aiko rahoto daga, Bnei Brak
- Lokacin karatu: Minti 5
Rikicin da ya kunno kai na ɗibar Yahudawa masu ra'ayin riƙau cikin rundunar sojan Isra'ila na kawo wa gwamnati barazana da kuma raba kan 'yan ƙasar.
Ra'ayin jama'ar ƙasar ya sauya sosai sakamakon shafe shekara biyu ana yaƙin Gaza, kuma ana ganin shi ne lokaci mafi haɗari ga siyasar Firaminista Benjamin Netanyahu.
Yanzu haka 'yanmajalisa na duba wani ƙudirin doka da zai soke tsarin keɓance Yahudawa masu ra'ayin riƙau waɗanda ake kira Haredi shiga rundunar soja, abin da da aka tsara tun daga lokacin da aka kafa ƙasar Isra'ila a 1948.
Sai dai Kotun Ƙolin Isra'ila ta ayyana keɓancewar a matsayin saɓa doka tun shekara 20 da suka wuce, abin da ya sa gwamnati ta fara tilasta musu shiga soja.
A shekarar da ta gabata an bai wa mutum 24,000 sammacin shiga soja, amma bai fi 1,2000 na 'yan Haredi ne suka kai kansu ba, a cewar rahoton da rundunar sojan da ta aika wa 'yanmajalisa.
Hankula sun fara tashi saboda 'yanmajalisa sun fara tattaunawa kan wani ƙudirin doka da zai tilasta wa mazan Heredi shiga aiki soja.
A makon da ya gabata ma sai da 'yansanda suka ceto wasu sojoji bayan wasu matasan Heredi sun kai musu hari lokacin da suka yi yunƙurin kama wani da ya ƙi amsa gayyatar shiga aikin soja.
Wannan kamen da ake yi ya sa aka ƙirƙiri wani tsarin tura saƙo mai suna "Black Alert" wanda 'yan Heredi za su dinga amfani da shi wajen aika saƙon ankararwa a tsakaninsu da kuma shirya zanga-zanga.
Kazalika, shirin shigar da ƙarin 'yan Heredi aikin soja ya jawo zanga-zanga iri-iri a Birnin Ƙudus a watan da ya gabata.
"Ƙasarmu ta Yahudawa ce," in ji Shmuel Orbach, ɗaya daga cikin masu zanga-zangar. "Ba zai yiwu ka yaƙi Yahudanci a ƙasar Yahudawa ba. Ba zai yiwu ba."
Amma har yanzu lamarin bai kai ga cibiyar ilimi ta Kisse Rahamim yeshiva ba ta masu ra'ayin riƙau, wadda ke Bnei Brak a birnin Tel Aviv.
"Ku zo da ƙarfe 1:00 na dare, za ku ga kusan rabin ɗaliban na karanta littafin Attaurah," kamar yadda shugaban yeshiva ya shaida mani. "Muna bai wa sojojinmu kariya ta hanyar karanta Attaurah a duk inda suke. Wannan ce rundunarmu."
'Yan Heredi na da imanin cewa addu'a ce ke kare sojojin Isra'ila kamar yadda tankoki da bindigogi ke ba su kariya. 'Yansiyasar Isra'ila na baya sun yarda da wannan, a cewar Rabbi Mazuz, amma ya ce yanzu ƙasar na sauyawa.
"Yanzu da yawan 'yanmajalisa da jami'an gwamnati na nisanta kansu daga addini. Suna kallon ɗaliban yeshiva a matsayin cima-zaune, wanda ba gaskiya ba ne," in ji shi.
Duk da sukar da masu ra'ayin riƙau ke yi, Tel Aviv na cikin garuruwan da suka fi bayar da sojoji masu a lokacin yaƙin. Matsin lambar da sojojin ko ta kwana da suka sha ta fito da matsalar fili game da yawan waɗanda ba su shiga aikin sojan.
Adadin 'yan Heredi ya ninka sama da sau ɗaya cikin shekara 70, inda yanzu suka kai kashi 14 cikin 100 na al'ummar ƙasar. Ya zuwa lokacin yaƙin Gaza, mazaje na Heredi kusan 60,000 ne aka ƙyale da ba za su shiga aikin soja ba.
Ƙuri'ar ra'ayin jama'a na nuna cewa mutane na ƙara goyon bayan saka 'yan Heredi cikin rundunar sojan Isra'ila. Wani bincike a watan Yuli na cibiyar Israel Democracy Institute ya gano kashi 85 cikin 100 na 'yan jam'iyyar Lukud ta su Netanyahu na goyon bayan a hukunta duk wanda ya ƙi amsa gayyatar shiga aikin soja.
Akasarin mutanen na ganin ya kamata a daina ba su alfarmomi, ciki har da ƙwace fasfo ɗinsu da hana su kaɗa ƙuri'a a zaɓuka.
"Nakan ji cewa akwai wasu da ke zaune a ƙasar nan ba tare da sun amfanar da ita komai ba," in ji ɗaya daga cikin sojojin ko-ta-kwana daga Tel Aviv.
"Ba na ganin ya kamata a ƙyale wani mutum ya zauna ba ya hidimta wa ƙasa ba duk irin addininsa," kamar yadda wata mai suna Gabby a Tel Aviv ta faɗa. "Idan a nan aka haifi mutum, ina ganin shashashanci ne ma a ce mutum zai koma karanta Attaurah kawai kodayaushe."
Wasu ma'abota addini cikin Yahudawan ma na goyon bayan kawo ƙarshen keɓance 'yan Heredi, kamar Dorit Barak da ke zaune a kusa da yeshiva.
"Raina yana ɓaci saboda masu ra'ayin riƙau da ba su shiga aikin soja," in ji ta. "Rashin adalci ne. Ni ma ina karanta Attaurah, amma akan ce "Safra da Saifa" a harshen Hebew [wato Littafi da Takobi] - abin da ke nufin Attaurah da bindigogi tare. Wannan ne abin yi har sai an samu zaman lafiya."
Ms Barak na gudanar da wani wurin tunawa da sojoji masu addini da marasa shi, waɗanda aka kashe a wurin yaƙi. Soja na ƙarshe daga yankin ya mutu a 1983 - wata alama da ke nuna sauyi a zamantakewar Isra'ila.
"Ta sauya gaba ɗaya," a cewarta. "Lokacin da nake yarinya, kusan rabin mutanen unguwar nan ba masu kula da addini ba ne, sai kuma 'yan kaɗan masu ra'ayin riƙau. Yanzu kusan kowa ya zama mai riƙaƙƙen ra'ayi, kuma tun 1983 ba a sake kashe soja ba saboda babu wanda ke shiga aikin soja."
Akwai rundunoni na musamman a 'yansanda da soja domin kula da masu ra'ayin riƙau da suka zaɓi shiga soja. Amma Netanyahu ya ayyana cewa nan da shekara biyu za a ɗauki 'yan Heredi 10,000 aikin soja, abin da ya bayyana da cewa "juyin juya hali ne".
Jam'iyyu masu ra'ayin riƙau na cikin ƙawancen jam'iyyu da suka kafa gwamnatin Netanyahu, da kuma yunƙurin kauce wa zargin cin hanci, wanda ya musanta. A madadin goyon bayansu, gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙyale su daga shiga aikin soja.
Wannan lamari ya jawo kifewar gwamnatin Netanyahu har sau biyu a baya.