Ƙauyen da mata suka kashe ɗaruruwan mazansu da guba a Hungary

    • Marubuci, BBC News Mundo
  • Lokacin karatu: Minti 4

A watan Disamban 1929, an gudanar da wata shari'a a kotun lardi da ke ɗan ƙaramin birnin Szolnok na ƙasar Hungary. Shari'ar ta mayar da hankali ne kan yadda wasu gomman mata daga wani ƙauye mai suna Nagyrev da ke kusa da birnin suka kasance ababan tuhuma bisa zargin sanya wa mazajensu guba da ganganci.

Jaridar New York Times ta rawaito a lokacin cewa kusan mata 50 ne ke fuskantar tuhumar dangane da zargin kisan mazansu ta hanyar amfani da guba a garin nasu.

Jaridar ta sanar da cewa tsakanin 1911 zuwa 1921, fiye da maza 50 ne suka mutu a Nagyrev, wanda gari ne na manoma da ke da tazarar kilomita 130 a kudancin birnin Budapest.

Matan da ake zargi su ne waɗanda ake kira da "angel makers'.

Rayuwa a Nagyrev

Nagyrev ya kasance ɗan ƙaramin ƙauye da mai yawan manoma da ke a bakin Kogin Tisza a yankin Kunsag mai girman da ake haɗa giya.

A wannan garin dai bisa al'ada a kan ƙulla aure tsakanin maza da mata, inda ake haɗa ƴanmata da mazan da suka girme su sosai. Kuma ana ƙulla auren ne a kan yarjejeniyar da ta jiɓanci ƙasa da gado sannan kuma ba a sakin aure.

A wannan lokacin ƙauyen na ƙarƙashin ikon daular Austro-Hungarian.

A wannan ƙauyen, ungozoma da ake kira Fazekas ita ce take duba marasa lafiya kasancewar babu likitoci a ƙauyen.

Wata ungozoma mai suna Maria Gunya wadda tun tana ƙaramar yarinya mahaifinta ke aiki tare da ƴansanda domin gano dalilan da ke haddasa mace-macen maza a ƙauyen.

Ta ce Fezakas ta samu labarai iri-iri daga wurin mata dangane da halin da suke ciki a gidan aurensu da suka haɗa da cin zarafi da fyaɗe har ma da duka.

Ta ƙara da cewa a duk lokacin mata suka koka dangane da mazajensu da ke shan giya waɗanda suke dukan su, sai ita Maria ta faɗa musu cewa "Ina da mafita, idan kuna da matsala."

Kuma mafi yawancin mafitar da take ba su ita ce amfani da sindari mai guba da ungozomar ke tace shi ta hanyar jiƙa guba mai daƙo da ake amfani da ita wajen kashe abubuwa kamar ɓera ko kuma ƙudaje.

Daga baya an gono kwalaben guba a wurin shaƙatawarta da ke cikin gida kamar yadda wani rahoton jaridar The Times ta Burtaniya ya rawaito.

Sammaci

A cikin ƴan shekaru sai kawai aka ga maƙarbartar ƙauyen ta fara cika.

Tsakanin 1911 da 1929 an binne kimanin mutum 50 a maƙabartar Nagyrev - da daman su mazaje da iyaye maza.

A hankali sai hukumomi suka fara zargin mutuwar ba daga Allah take ba kuma nan da nan suka fara gwajin dalilin mutuwar a kan gawarwakin.

Daga cikin mamata 50 da aka tono kuma aka yi gwaji a kansu, 46 na ɗauke da sinadarin guba wani abun da ya tabbatar da zargin amfani da guba domin kisa.

Kuma sai aka fara zargin ungozoma da ake kira da Fazekas.

A ranar 19 ga watan Yulin 1919 ne ƴansandan suka tunkari gidan Maria Gunya domin kama ta.

"Lokacin da ta fahimci ƴansanda sun tunkari gidanta hakan ya sa ta fahimci cewa asirinta ya tonu. Koda suka shiga gidan nata, sun tarar ta mutu - ta sha irin gubar da take da ita," in ji Ms Gunya.

Mutuwar farko

Rahotannin ƴansanda sun nuna cewa an fara samun mace-macen farko a ƙauye a shekarar 1911 daidai lokacin da Fezakas ta fara shiga ƙauyen. Lokacin ne aka fara gani mace-mace ta hanyar guba abin da ya ɗore har shekaru ashirin da suka biyo baya.

To sai dai da alama ba wai kawai ita unguzomar ce mai aikata laifin ba. A kusa da birnin Szolnok, an samu mata 26 da laifin kisan waɗanda aka yi wa hukunci a 1929. An yaneke wa mata guda takwas hukuncin kisa, sauran kuma an aika su gidan yari, inda bakwai daga cikinsu aka yanke musu hukuncin zaman gidan yari na rai da rai. Kaɗan ne daga cikinsu suka amince da laifin da ake tuhumar duk da cewa ba a iya fayyace dalilinsu da aikata kisan ba.

Dangane da dalilin da ya sa suka aiwatar da kisan, an samu tunanin da ke alaƙanta faruwar al'amarin da abubuwa da dama da suka haɗa da talauci da son rai da kuma zaman kaɗaici.

Wasu rahotannin ma na cewa mata sun auri masoyansu daga cikin fursunonin yaƙi ƴan Rasha waɗanda aka hukunta cewa za su yi noma a gonaki a lokacin da mazajen matan ba sa nan, wadanda suka kasance a filin daga lokacin yaƙin duniya na farko.

Kuma bayan dawowar mazajen nasu sai matan suka tsinci kansu a yanayin rashin ƴanci inda daya bayan ɗaya suka zartar da abin da suka yi.

Maƙwabtan Nagyrev

A wani gari mai suna Tiszakurt mai maƙwabtaka ma an samu mace-mace masu alaƙa da guba bayan yin gwaje-gwaje a kan gawarwakin da aka tono duk da cewa babu mutumin da aka hukunta bisa mace-mace.

Ƙididdiga ta nuna yawan mace-mace da aka samu a yankin sun kai 300.

Tsawon lokacin da aka kwashe da faruwar al'amarin ya sa yanzu haka an manta da faruwa kashe-kashen ta hanyar amfani da guba a Nagyrev. Sunan garin ba ya jefa fargaba a zuciyar al'ummomin da ke zaune a yankin.

Ms Gunya cikin ba'a ta ce halayyar mazajen garin ta "sauya sosai" tun bayan faruwar al'amarin.