Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tunawa da Gimbiya Diana shekara 25 bayan rasuwarta
Ana yi wa Diana, tsohuwar gimbiya a masarautar Birtaniya laƙabi da "wacce ta fi kowa yawan ɗaukar hoto a duniya."
A yayin da take cika shekara 25 da mutuwa, mun yi waiwaye kan rayuwarta a cikin hotuna, ta hanyar zaƙulo wasu hotunanta masu ban sha'awa.
An haifi Diana Frances Spencer ranar 1 ga watan Yulin 1961 a Park House kusa da Sandringham, Norfolk, Ingila.
Ita ce ƙaramar ƴar Viscount and Viscountess Althorp.
Bayan mutuwar auren iyayenta a shekarar 1969, tana yawan yin tafiye-tafiye tsakanin gidajen iyayen biyu a Northamptonshire da Scotland.
Diana ta yi karatun firamarenta a makarantar Riddlesworth Hall a Diss da ke Norfolk, sannan daga bisani ta koma makarantar kwana ta West Heath a kusa da Sevenoaks a Kent a 1974.
Ta bar West Heath a 1977 sannan ta wuce makarantar Institut Alpin Videmanette da ke Rougemont a Switzerland, inda ta bari a shekarar 1978.
Bayan kammala karatunta sai ta fara aiki a Landan, da farko a matsayin mai renon yara, da aikin girki, daga bisani kuma ta koma aiki wata kamarantar yara ta Young England Kindergarten da ke Knightsbridge a Landan.
An fara yaɗa jita-jitar cewa ta zama budurwar Yariman Wales.
A wannan gaɓar ne idanun duniya da na kafafen yaɗa labarai suka koma kanta.
A ranar 24 ga watan Fabrairun 1981 ne aka sanar da baikon Yarima Charles da Lady Diana Spencer a Fadar Buckingham.
A wancan lokacin an kashe fam 30,000, (wato daidai da fam 36,000 na yanzu) da kuma tsadadden zobe mai daiman 14 a jikinsa.
An yi ta zancen zoben baikon nata saboda tsadarsa kuma a yanzu Catherine, Duchess ta Cambridge ce ke amfani da shi.
An yi wa auren nasu laƙabi da "bikin da ya fi kowane a ƙarnin", an ɗaura auren Lady Diana da Yarima Charles a Mujami'ar St Paul Cathedral ranar 29 ga watan Yulin 1981, aka kuma watsa shi kai tsaye a talabijin, inda miliyoyin mutane daga faɗin duniya suka kalla.
A matsayinta na ƴar shekara 20 a lokacin, babu abin da ya rikitata sai sanda za ta faɗi jerin sunayen mijin nata.
Mahaifinta Earl Spencer ne ya yi mata rakiya zuwa dandamalin da aka ɗaura auren.
Rigar aurenta wacce David da Elizabeth Emanuel suka ɗinka tana da tsayin kamu 25 kuma an yi ta da wani tsadadden leshi ne.
Mutum 600,000 ne suka yi dafifi a hanyar zuwa cocin daga Fadar Buckingham don kallon wucewar ango da amaryar.
Ma'auratan sun yi ta ɗagawa cincirindon mutanen hannu daga saman benen fadar (kamar yadda ake iya gani a hoton nan na sama) tare da ƴan yara da suka yi mata ƴan amarya da kuma Gimbiya Elizabeth II.
Diana ta daɗe tana fatan yin aure a babban gida.
A cikin shekara ɗayar farko ta aurenta ne ta haifi ɗanta na fari ranar 21 ga watan Yunin 1982, Prince William, wanda shi ne na biyu a jerin wadanda za su iya gadar sarautar.
Ta yi wa ƴaƴanta tarbiyya bisa irin tsarin da masarauta ta yarda da shi.
A ranar 15 ga watan Satumban 1984 ne aka haifar wa William ƙani.
An saka masa suna Henry, amma an fi saninsa da Yarima Harry.
Ba a ɗaukarwa jikokin gidan sarautar malamai na musamman don koyar da su ba, an saka su ne a makarantun da sauran yara ke zuwa.
Diana ta zama abar so a wajen ƴaƴanta maza biyu.
Prince Harry ya ce Diana ta kasance "ɗaya daga cikin iyaye marasa dattako", kafin ya ƙara da cewa: "Ta nuna mana soyayya, wannan kam babu haufi a ciki."
A ziyararta ta farko zuwa Amurka, gimbiyar ta yi rawa da wani ɗan fim John Travolta a Fadar White House.
Diana ta ci gaba da yin fice da suna. Ta fara jan hankalin mutane da irin adonta, inda aka dinga mayar da hankali kan suturar ƙawa da take sakawa.
An yi ta ganinta a al'amuran da suka shafi aiki a hukumance, kuma ayyukan jin ƙan da ta dinga yi sun jawo mata soyayyar mutane da kuma mamaye kanun labarai a faɗin duniya.
Ta taka muhimmiyar rawa wajen dinga nuna muhimmancin mutanen da ke fama da cutar Aids. Jawabanta sun dinga ƙalubalantar halayyar nuna bambanci.
Shan hannun da ta dinga yi da masu ɗauke da cutar Aids ya tabbatarwa da mutane cewa babu wata illa a yin hakan.
Yarima da Gimbiyar Wales sun sha aiwatar da wasu al'amura tare kuma sun yi tafiye-tafiye tare.
Sai dai a shekarun 1980 an fahinci irin zaman doya da manjar da suka fara yi.
Wata tafiya da suka yi zuwa Indiya a 1992, an ga Diana ita kadai ta yi hoto zaune a gaban ginin Taj Mahal, ginin da ake alaƙantawa da soyayya.
Hakan ya nuna cewa duk da ma'auratan suna tare, amma zaman doya da manja ake yi.
A tsawon rayuwarta, Diana ta kasance tana da kyakkyawar alaƙa da Mother Teresa, wata fitacciyar malamar addinin Kirista ta ɗarikar Katolika.
Tsakanin mituwarsu kwana shida ne kacal.
Bayan shafe shekara shida ana zaman ƴar marina, a ƙarshe dai a ranar 28 ga watan Agustan 1996 sai Charles ya saki Diana.
A watan Yunin shekarar da ta biyo bayan hakan ne ta yi gwanjon rigunanta 79 da aka tallata a shafukan farko na wasu mujallu a faɗin duniya.
An sayar da kayan dala miliyan 4.5 aka kuma yi amfani da kuɗin wajen ayyukan jin ƙai.
A ranar 31 ga watan Agustan 1997, bayan kammala cin abincin dare a Ritz Paris tare da Dodi Al Fayed, ɗan hamshaƙin attajirin nan Mohamed Al Fayed, sai suka bar wajen cin abincin tare a motar limozin.
Masu ɗaukar hoto sun yi ta bin su a kan babura don son ɗaukar hoton gimbiyar da sabon saurayinta.
Rububin bin nasu ya yi sanadin da suka yi mummunan hatsari a wani titin ƙarƙashin gada.
Fiye da mutum miliyan ɗaya ne suka jeru a layi reras a hanyar zuwa wajen jana'izar zuwa Westminster Abbey.
Kamar yadda ake gani a hoton da ke sama akwatin gawarta ne ake ɗauke da shi sai masu biye da gawar mijinta Yarima Charles da ƙaramin ɗantaYarima Harry mai shekara 12 a lokacin da ɗan uwanta Earl Spencer, da babban danta Yarima William da kuma Duke na Edinburgh.
Shekara 25 bayan rasuwarta, har yanzu ana tunawa da ita cikin shauƙi a fadin duniya.