Ahmad Aliyu na APC ya lashe zaɓen jihar Sokoto

Hukumar Zabe ta Kasa reshen Jihar sokoto ta Ayyana Ahmed Aliyu sokoto na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.
Baturen Zaben Kuma Shugaban Jami'ar Tarayya ta Dutsinma a jihar Katsina Prof Armiya'u Hamisu shine ya Ayyana sakamakon Zaben.
Ahmed Aliyuya samu kuri'u 456,661, yayin da Sa'idu Umaru Ubandoma na jam'iyyar PDP ya zo da na biyu da ƙuri'u 404,632.
A shekarar 2019 Ahmad Aliyu ya kara da Aminu Tambuwal na PDP a zaben gwamnan jihar da aka yi.











