Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Netanyahu ke shirin mamaye Gaza baki ɗayanta
- Marubuci, Yolande Knell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem
- Lokacin karatu: Minti 4
Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu na shirin gabatar da ƙudirin sake mamaye Zirin Gaza a lokacin da zai gana da majalisar tsaron Isra'ilar, kamar yadda kafafen watsa labarai ke rawaitowa.
"Yaƙi ya wajaba. Za mu shiga cikakken yaƙi a Zirin Gaza - da karya lagon Hamas," kamar yadda kafafen watsa labaran cikin gida suka rawaito wani babban jami'i na faɗi.
Da suke mayar da martani ga tsarin, shugaban sojoji da sauran manyan sojojin ƙasar sun soki al'amarin kamar yadda jami'in da ba a bayyana sunansa ba ya faɗi; "Idan hakan bai yi wa shugaban sojin ba to ya yi murabus."
Iyalan waɗanda ake garkuwa da su a Gaza na bayyana fargabar cewa ƙudirin na Netanyahu ka iya jefa ƴan'uwan nasu kimanin 20 da aka yi yaƙinin suna da rai cikin haɗari kuma ya daƙile ƙoƙarin da ake yi na komawarsu gida.
Da dama daga cikin ƙawayen Isra'ila za su yi alawadai da shirin a ƙoƙarinsu na ganin an kawo ƙarshen yaƙin domin kawo ƙarshen wahalhalun da jama'a ke fuskanta.
A cikin Isra'ila akwai ɗaruruwan sojojin da suka yi ritaya da suka haɗa da tsoffin shugabannin hukumomin bayanan sirri da suka fitar da aike da wata wasiƙa ta haɗin gwiwa ga shugaban Amurka, Donald Trump, ranar Litinin inda suke kiran da ya ƙara matsin lamba ga Netanyahu ya kawo ƙarshen yaƙin.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka saka wa wasiƙar hannu tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta cikin gida, cif Ami Ayalon ya shaida wa BBC cewa ci gaba da ayyukan soji a Gaza ba sai haifar da wata nasara ba.
Akwai hasashen da ke nuna cewa labaran da ke fitowa daga kafafen watsa labarai na nuni da wani sabon salon yaƙi na tilasta mayaƙan Hamas su shiga sabuwar tattaunawa.
Sojojin Isra'ila sun ce tuni suke iko da kaso 75 na Gaza. To amma ƙarƙashin shirin sake mamayar, yanzu Isra'ila za ta mamaye ɗaukacin yankin - inda a hankali za a tankarar da yankunan da Falasɗinawa miliyan biyu ke tattare.
Babu tabbas abin da sake mamayar ke nufi ga fararen hula da kuma ayyukan Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙungiyoyi masu ayyukan jinƙai.
Kimanin kaso 90 na al'ummar Gaza mutum miliyan 2.1 na gudun hijra wasu ma ba sau ɗaya ba kuma suna zaune a cunkushe cikin mummunan yanayi. Ƙungiyoyi masu ayyukan jinƙai da jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya sun Falasɗinawa, inda suke zargin Isra'ila da daƙile ayyukan rabon tallafi da ake rabawa.
A baya-bayan nan sojojin Isra'ila sun ja baya da suka haɗa da wasu sassan tsakiyar Gaza saboda hasashen cewa har yanzu akwai waɗanda aka yi garkuwa da su na da rai. A bara Hamas ta kashe waɗanda aka yi garkuwar da su guda shida bayan da dakarun ƙasa suka kutsa zirin.
Har yanzu dai babu wani martani a hukumance amma kuma gwamnatin Falasɗinawa da ke jagorancin wani sashe na Yamma da Kogin Jordan, ta yi watsi da shrin mamaye Gaza da Isra'ila ke yi, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su shiga lamarin.
Falasɗinawa sun ce ministoci masu tsatstsauran ra'ayi na Isra'ila sun sha ayyana burinsu na mamaye Gaza domin gina sabbin muhalli ga Yahudawa ƴan kama wuri zauna.
A 2005 ne Isra'ila ta ruguje muhallai a zirin Gaza sannan ta janye dakarunta daga can.
Bisa taimakon Misra, Isra'ilar ta matsa lamba wajen hana damar shiga yankin.
Sabon tunanin mamayar na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun goyon bayan ƙasashen duniya na neman a kafa ƙasashen Isra'ila da na Falasɗinu a matsyain hanyar magance rikicin. Kuma hakan ya ƙunshi ƙasar Isra'ila da ke Yamma da Kogin Jordan da kuma ƙasar Falasɗinawa a zirin Gaza wanda gabashin birnin Ƙudus zai kasance babban birnin ƙasar.
Ana sa ran firaiministan isra'ila zai gana da ministoci da manyan soji domin yanke mataki na gaba. Gidan rediyon Isra'ila ya ce shugabannin na daf da tattauna shirin soji na farko domin yi wa sansanonin ƴangudun hijira ƙawanya inda za su aiwatar da hare-hare ta sama da ƙasa.
Netanyahu ya ce zai yi zama da majalisar tsaron ƙasar a makon nan.
Masu sharhi a Isra'ila sun nuna fargaba dangane da ƙalubalaen da sojojin ƙasar ke fuskanta.
Ma'ikatar lafiya ta Gaza dai ta ce kawo yanzu dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa 61,020 tun bayan fara yaƙi da bayan da Hamas ta kai harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023.