Mene ne tasirin matakin Dangote na daina sayar da man fetur da naira?

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Larabar nan ne matatar man fetur ta Dangote ta sanar da cewa ta dakatar da sayar da man fetur da kuɗin Najeriya wato naira.

Kamfanin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya aika wa dillalan man fetur kuma ya wallafa a shafinsa na X.

Sanarwar matatar ta zo ne a daidai lokacin da ake samun takun-saƙa tsakaninta da kamfanin mai na Najeriya, NNPCL.

Matatar ta yi ƙarin bayani da cewa an ɗauki matakin ne saboda kaucewa rashin daidaito da ake samu tsakanin ribar da kamfanin ke samu da kuɗin da yake sanya wa masu sayen ɗanyan mai wanda a yanzu galibi da dala suke ciniki.

Kamfanin ya kuma ƙara da cewa bisa wannan dalilin, wajibi ne ya sauya kuɗin da yake sayar da man domin ya yi daidai da kuɗin da yake sayen ɗanyen mai na wani ɗan lokaci.

A watan Oktoban 2024 ne yarjejeniyar da aka ƙulla da NNPCL ta sayarwa da matatar Dangote ɗanyen man fetur da naira ta soma aiki.

Sai dai a farkon watan Maris ne, NNPCL ya ce yarjejeniyar da ya ƙulla da matatar Ɗangote ta tsawon wata shida ce wanda hakan ke nufin wa'adin yarjejeniyar zai cika a ƙarshen wannan watan - wani abu da masana ke ganin zai ƙara janyo a samu ƙarin buƙatuwar dala a Najeriya.

Abin tambayar a nan ita ce, ta yaya wannan mataki da matatar ta Ɗangote ta ɗauka zai shafi darajar naira da kuma shi kan shi man fetur ɗin da kuma hanyoyin da ya kamata a bi domin rage tasirin da matakin ka iya haifarwa.

Domin warware zare da abawa, BBC ta tuntuɓi Farfesa Ahmed Adamu masanin tattalin arzikin man fetur a Jami'ar Nile da ke Abuja.

Me matakin ke nufi?

A cewar masani Farfesa Ahmed Adamu matakin na Dangote da zai janyo a riƙa rububin dala wanda hakan zai sa darajar kuɗin Najeriya - naira ta ƙara durƙushewa.

"Idan naira ta durƙushe, hauhawar farashi za ta ƙaru kuma za a iya ganin farashin mai ya ƙaru." in ji Farfesa Ahmed.

Ya ƙara da cewa babban abin da ke gwada farashin mai a gidajen mai ko zai yi sama ko ƙasa, shi ne darajar naira - idan naira ta yi ƙasa, farashin mai a gidajen mai zai yi tsada, idan naira ta samu tagomashi, farashi zai yi sauƙi a gidajen mai.

Hakan kuma a cewarsa, ya nuna cewa za a sake samun ƙarin shigo da man fetur daga ƙasashen waje saboda shi ma Dangote zai ƙarke wajen shigo da ɗanyen mai daga ƙasashen waje - za a iya komawa gidan jiya na shigo da komai Najeriya daga ƙasashen waje.

"Akwai kuma kuɗin dakon jirgin ruwa wanda shi ma zai ƙara tsadar kuɗin litar man fetur ke nan." in ji masanin.

Me ya kamata a yi?

Ganin yadda masanin ya yi hasashen yiyuwar komawa gidan jiya wajen shigo da man fetur da ma faɗuwar darajar naira, lamarin da wasu ke ganin tamkar mayar da hannun agogo baya ne, BBC ta tambayi masanin ko akwai hanyar da za a bi a samu sauƙi?

Ya ce hanya ɗaya ce tilo, wadda kamar yadda Hausawa suke cewa hanyar aka bi aka hau, ta ita za a sauko.

Ya ce, "abin da ya kawo faɗuwar naira, da shi za a yi amfani. Wato a daina buƙatar dala," in ji shi, inda ya ƙara da cewa a Najeriya ake samar da ɗanyan man, kuma a Najeriya ake tacewa, "me ya kawo maganar dala?"

Sai dai ya ce kasuwancin man fetur da dala ake yi saboda kasuwa ce ta duniya, domin a cewarsa, "babu wanda zai je wata ƙasa ya ce zai yi kasuwancin fetur da naira. Shi kansa Dangote naira ba za ta masa amfani ba sai dai idan ɗanyan man zai saya a Najeriya, idan ya je wata ƙasa ba za a amince ba. Dole dalar ake buƙata. Don haka matuƙar za a cigaba da amfani da dala, naira za ta cigba da durƙushewa."

Farfesa Ahmed Adamu ya bayyana cewa abin da yake gani shi ne ya kamata "NNPCL da Dangote su samu fahimtar juna a kuma samar da tsarin da za su daidaita don a dawo da yarjejeniyar saboda tsarin zai yi tasiri wajen farfaɗo da darajar naira da kawo arhar mai da rage hauhawar farashi."

Ya ce ko da ba za a riƙa na Dangoten adadin ɗanyen man da ake ba shi a baya ba wato lita miliyan 50, zai yi kyau a ba shi wasu adadi, "ko kuma su shiga tsarin ba ni gishiri in ba ka manda."