Ragin da NAHCON ta yi a kuɗin aikin Hajjin bana

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta sanar da yadda aikin hajjin bana zai kasance dangane da abin da ya shafi kuɗin kujerar aikin da lokacin da za a rufe karɓar kuɗin maniyyata.

Wannan dai ya biyo bayan ƙulla yarjejeniyar gudanar da aikin Hajji ta 2026 da hukumar ta yi a madadin Najeriya da hukumomin ƙasar Saudiyya, yayin wani biki a birnin Jeddah na Saudiyyar.

Shugaban hukumar alhazai ta Najeriya Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da mataimakin ministan Hajji na Saudiyya Abdulfatah Mashat ya wakilci Saudiyyar.

Hukumar alhazan Najeriya Nahcon ta ce yarjejeniyar hujja ce cewa Najeriya ta shiga jerin ƙasashen da za su gudanar da aikin ibadar a bana.

Kuɗin aikin Hajji

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta sanar da rage kudin kujerar aikin hajji, bisa umarnin shugaban ƙasa.

Farfesa Abdullahi Saleh Usman wanda shi ne shugaban hukumar ta NAHCON ya shaida wa BBC cewa ragin kuɗin ya faru ne bisa umarnin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

  • Shiyyar Bornon Yola:

Kuɗin aikin Hajjin bana ga mutanen yankin Maiduguri da Yola da ke shiyyar arewa maso gabashi da ta ƙunshi jihar Borno, Adamawa da Taraba da Yobe naira miliyan 7,579,20.96 saɓanin miliyan 8,327,125.59 wato an samu ragin naira 7748,104.63.

  • Jihohin arewacin Najeriya:

Sauran ɓangarorin arewacin Najeriya za su biya naira miliyan 7,696,769.76 wato sun samu ragin naira 760,915.83 daga 2025.

  • Alhazan kudancin Najeriya:

Alhazai daga kudancin Najeriya za su biya naira miliyan 7,991,141.76 saɓanin abin da suka biya a 2025 na naira 8,784,085.59 wato maniyyata za su samu ragin naira 792,943.83

Shugaban Hukumar Alhazan ta Najeriya, NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya ce an tsara sabon farashin kujerar aikin hajjin na bana ne a kan kowace dalar Amurka daidai da naira 1,443.

A watan Oktoba ne hukumar aikin Hajjin ta Najeriya ta sanar da kuɗin aikin hajjin shekarar 2026 to amma sai shugaba Tinubu ya umarce ta da ta rage kuɗin bisa la'akari da yadda tsadar rayuwa ke tafiya.

Yaushe za a rufe karɓar kuɗin hajjin?

Shugaban Hukumar Alhazan ta Najeriya, NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya ce za a rufe karɓar kuɗin hajjin bana daga ranar 21 ga watan Disamban 2025.

"Mun sanar da cewa 31 ga watna Disamba amma yanzu sun tabbatar mana cewa duk wanda bai biya kuɗinsa ba zuwa ranar 21 ga watna Disamban bana. Saboda haka muna jan hankalin maniyyata da a hanzarta a biya kafin lokacin ya ƙure."

Kujeru nawa aka ware wa Najeriya?

Duk da cewa hukumomin ƙasar ta Saudiyya sun tanadi wurin kwanan ƴan Najeriya 66,910 bayanai na nuna cewa akwai yiwuwar hukumar alhazan Najeriya ta iya samun ƙarin gurabe nan gaba.

"Sun fahimci cewa sun yi kuskure dangane da waccan magana. Kuma za su duba su waiwayi batun. Abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne maniyyata su hanzarta biyan kuɗin aikin hajjin na bana da za a rufe a rana 21 ga watan Disamban 2025.

Kenan yanzu za a iya cewa Najeriya za ta samu yawan kujeru daidai da yawan mutanen da suka kammala biyan kudin aikin hajjinsu a ranar 31 ga watan Disamban 2025," in ji Ahmad Mu'azu maitaimaka wa shugaban hukumar na musamman.

"Sannan kuma idan ka dubu tsarin da Saudiyya ke bi na rabon kujerun aikin hajji ga ƙasashen Musulmi za ka ga ba haka abin yake ba," in ji Ahmad Mu'azu.

Tsarin da Saudiyya ke bi na raba kujerun Hajji

Ahmad Mu'azu, mataimaki na musamman ga shugaban hukumar alhazan ta Najeriya ya shaida wa BBC cewa akwai ƙa'idoji da ƙungiyar ƙasashen Musulmi da Larabawa, OIC ta fitar da kuma ƙasar Saudiiyar ke la'akari da su.

"Abin da ake dubawa shi ne nawa ne yawan Musulmin kowace ƙasa?. Misali Najeriya bisa hasashen OIC a baya, yawan Musulmai ya kama miliya 95. To sai a ɗauki mutum ɗaya a cikin kowace miliyan ka ga kenan shi zai ba ka 95,000 daidai da yawan kujerun da aka ware mana a bara.

To ka ga batun cewa a bana an ba mu kujeru 65,000 zai yi wuya. Insha Allah za a kara mana lokacin da za mu zauna mu ƙarƙare al'amura a watan Nuwamba."

Ahmad ya kuma ƙara da cewa "mu ai yanzu ma muna fatan a sake waiwayar adadin Musulman Najeriya na yanzu saboda muna hasashen Musulmai a Najeriya sun wuce miliyan 120."