Lokuta uku da ba za a manta da su ba tsakanin Barcalona da Bayern Munich

A

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Barcalona da Bayern Munich za su haɗu da juna karo na 12 kenan a wasan da za su buga a yau Laraba a gasar Zakarun Turai da misalin ƙarshe (20:00 BST).

Domin jin dadin wasan, mun samar muku bayanai kan haɗuwar don tuna muku da ƙoƙarin Lionel Messi da abin mamakin Thomas Muller.

Barcelona 0-3 Bayern Munich, 2022-23

A

Asalin hoton, Getty Images

Karo cikin kaka a jere, 3-0 Bayern Munich ta na cire Barcelona daga Champions Lig a matakin rukuni.

A wasa na biyar a rukunin C, Bayern ta yi wa Barcelona dukan kawo wuƙa bayan kwallon da Sadio Mane da Eric Maxim Choupo-Moting da kuma Benjamin Pavard suka ci.

Barcelona 2-8 Bayern Munich, 2019-20

a

Asalin hoton, Getty Images

Bayern Munich ta yi Barcelona zazzaga 8-2 har gida a watan kusa da na ƙarshe na farko a kakar 2019-20 da aka yi annobar Covid.

Kungiyar ta Jamus ta ci kwallo huɗu a ko wanne minti 45 na wasan, wanda a wasan akwai Lionel Messi, Luis Suarez da kuma Frenkie de Jong.

Thomas Muller da Philippe Coutinho duka sun ci kwallo biyu-biyu a wasan, wanda ya ba su damar cin kofin na shida a tarihi.

Barcelona 3-0 Bayern Munich, 2014-15

A

Asalin hoton, Getty Images

Lionel Messi ya ci kwallo biyu lokacin da Barcelona ta ci kwallo uku cikin minti 13 a wasan farko na kusa da na ƙarshe a gasar Zakarun Turai.

Sakamakon bai yi wa Pep Guardiola wanda zai koma Nou Camp daɗi ba, wanda tsohon kocin Barcelona a shekarar shi ta biyu a Bayern Munich.

Neymar ma ya ci kwallo ta uku a ƙarshen lokaci, abin da ya bai wa 'yan ukun gaban Barcelona Messi da Neymar da kuma Suarez damar cin kwallo 122 a duka gasanni a shekarar.