'Abin da ya sa muka sa tarar naira 25,000 ga masu yin ƙazanta a titunan Kano'

Lokacin karatu: Minti 2

Ƙudirin haramci da saka tarar naira 25,000 ga duk mutumin da aka kama yana ba-haya ko fitsari ko zubar da shara da tofa yawu da majina a tituna da ƙarƙashin gadoji da gine-ginen gwamnati da ma wuraren taruwar al'umma al'umma, da majalisar dokokin jihar Kano ta amince da shi, na ci gaba da tayar da ƙura a jihar.

A ranar Litinin ne dai majalisar dokokin jihar ta amince da ƙudirin inda kuma za ta miƙawa gwamnan jihar domin sanya masa hannu wanda daga nan ne kuma zai zama zama doka.

Idan har gwamna ya amince da ƙudirin, duk wanda aka samu da laifi kuma ya gaza biyan tarar ta naira 25,000 to hakan ka iya kaiwa ga kotu ta tasa ƙeyar mutum zuwa gidan yari.

Abdulmajid Isa Umar Mairigar Fata ɗanmajalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano ya shaida wa BBC cewa "wannan wani ɓangare ne na ƙudirin dokar ƙawata birnin Kano amma sai jama'a suka fi mayar da hankali kan abin da ya shafi tofar da yawu da majina da ba-haya."

Ɗanmajlisar ya ƙara da cewa "ya kamata duk mai kishin jihar Kano ya tallafa wa al'amarin tsaftace da ƙawata birni da kewayen jihar Kano domin ba sai an faɗa ba jihar Kano na fama da shara da sauran nau'in ƙazanta."

Jihar Kano dai na fama da matsalar dalar shara da bahaya a fili wani abu da wasu ke ganin ba zai rasa nasaba da rashin ɗa'a a tsakanin al'umma ba.

To sai dai masu sharhi na ganin cewa ya kamata gwamnati ta samar da wuraren zuba shara da na bahaya kafin aiwatar da wannan doka.

Masu fashin baƙi na ganin lokaci ya yi da ya kamata gwamnati ta fito da shirye-shirye da za su sauya tunanin al'ummar dangane da abin da ya jiɓanci tsaftar muhalli wadda ke da alaƙa da lafiyar jama'a.

Da ma dai sabon kwamishinan muhalli na jihar, Dr Ɗahiru Hashim ya sha alwashin kakkaɓe shara daga birnin da kuma tsaftace da ƙawata jihar.