Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutum uku da ke kan gaba a neman jagorancin INEC
Tun bayan da Farfesa Mahmud Yakubu ya ajiye muƙaminsa, ƴan Najeriya ke ta hasashe dangane da mutumin da zai maye gurbin tsohon shugaban hukumar zaɓen ta Najeriya wato INEC.
An naɗa Yakubu a matsayin shugaban hukumar ne a ranar 14 ga watan Nuwamban 2015, inda ya yi wa'adi biyu na shekara biyar-biyar.
An sabunta masa wa'adin ne a shekarar 2020, wa'adin da a yanzu ya ƙare bayan shekara biyar, wanda ya kama shekara 10 jimilla yana shugabantar hukumar.
Farfesa Yakubu ya miƙa ragamar jagorancin hukumar a ranar Talata ga babbar kwamishiniyar zaɓe ta hukumar, May Agbamuche-Mbu, wadda za ta yi riƙon-ƙwarya kafin a naɗa sabon shugaba na dindindin.
To ko wane ne zai zama shugaban hukumar na dindindin? Tambayar kenan da ke leɓɓan ƴan Najeriya.
A ranar Alhamis ne shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kira taron Majalisar Ƙasa domin ba shi shawara kan mutumin da za a zaɓa kafin daga bisani a miƙa wa Majalisar Dattawa domin tantancewa.
Jaridar Daily Trust ta ce wata majiya daga fadar shugaban Najeriya ta shaida mata cewa shugaban na son mutum ɗaya daga cikin wasu mutum uku ya jagoranci hukumar.
Mutanen kuwa su ne Justice Abdullahi Mohammed Liman da Farfesa Lai Olurode da kuma Farfesa Joash Ojo Amupitan.
Farfesa Joash Ojo Amupitan
Farfesa Joash Ojo Amupitan shi ne mataimakin shugaban jami'ar Jos ɓangaren gudanarwa da mulki.
Joash Ojo ya kasance Farfesa a fannin shari'a.
An haifi Farfesa Ojo a ranar 25 ga watan Afrilun 1967 a garin Aiyetoro-Gbede da ke ƙaramar hukumar Ijumu a jihar Kogi.
Justice Abdullahi Mohammed Liman
Justice Abdullahi Mohammed Liman ya kasance ɗaya daga cikin alƙalan Kotun Ɗaukaka ƙara ta Najeriya.
Justice Abdullahi wanda ɗan jihar Nasarawa ne, mai shekaru 66 ya zama lauya a 1984, inda kuma ya kwashe shekaru 25 a matsayinsa na alƙali.
Ana alaƙanta Justice Liman da yanke hukuncin manyan shari'o'i a Najeriya da suka ja hankali kamar dakatar da shari'ar da ta nemi a mayar da Sarki Sanusi a matsayin Sarkin Kano.
Farfesa Lai Olurode
Farfesa Lai Olurode na ɗaya daga cikin kwamishinonin zaɓe na hukumar INEC da aka naɗa a 2010, inda yake sa ido kan jihohin Oyo da Ogun da Ekiti.
Lai ya kwashe shekaru fiye da 40 yana koyarwa a jami'a.
Farfesa Lai Olurode masanin zamantakewa ne kuma ya kammala digirinsa a jami'ar Legas inda ya fita da sakamako mai daraja ta ɗaya, a 1990.
Matakan naɗa shugaban INEC
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi shimfiɗa dangane da yadda ya kamata a zaɓi shugaban hukumar zaɓe ta ƙasar.
Sashe na 154 na kundin ya fayyace hanyoyin zaɓen shugaban, inda kuma ƙaramin sashe na 3 ya yi cikakken bayani kan muƙamin.
"Domin amfani da damarsa ta naɗa wani a matsayin shugaba ko kuma mamba a Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ko Majalisar Alƙalai ta Ƙasa da Hukumar da ke sa kula da da'ar alƙalai ta ƙasa ko kuma hukumar ƙidaya ta ƙasa, ya kamata Shugaban ƙasa ya tuntuɓi Majalisar Ƙasa....kuma hakan zai tabbata ne bayan sahhalewar Majalisar Dattawa."
Majalisar Ƙasa
Majalisar Ƙasa wani ɓangare ne na gwamnati da ke taka rawar bayar da shawara ga ɓangaren zartarwa wato Fadar Shugaban Ƙasa.
Majalisar ƙasar ta ƙunshi shugaban ƙasa wanda shi ne ke jagorantar majalisar da mataimakin shugaban wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar da kuma tsoffin shugabannin ƙasar da shugaban Majalisar Dattawa da shugaban Majalisar Wakilai da ministan Shari'a da kuma dukkannin gwamnonin jihohin kasar.
Muna son a kafa kwamitin da zai zaɓi sabon shugaban INEC - Jam'iyyun Najeriya
Jam'iyyun siyasa a Najeriya sun fara martani kan saukar shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Inec Farfesa Mahmood Yakubu daga mukaminsa bayan kawo karshen wa'adinsa na biyu
Kwamitin tuntuɓa tsakanin jam'iyyun Najeriya ya yi kiran samar da wani kwamitin da zai jagoranci nada sabon shugaban hukumar zaɓe ta Inec da kuma kwamishinoni.
A ranar Talata ne Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga muƙaminsa na shugaban hukumar zaɓen Najeriya tare da miƙa ragamar jagorancin Inec ga May Agbamuche kafin naɗa sabon shugaba.
Shugaban ƙasa ne kundin tsarin mulki ya ba damar zaɓen shugaban hukumar zaɓe bayan tuntubar majalisar ƙasa da ta ƙunshi tsoffin shugabanni da gwamnoni da shugabanannin majalisun tarayya.
Gamayyar jam'iyyun siyasar na Najeriya ya ce idan har ana son tabbatar da hukumar zaɓen a matsayin mai ƴanci kuma mai zaman kanta da kuma tabbatar da tsabtar tsarin zaɓe, akwai buƙatar sake tsarin zaɓen shugabannin hukumar.
Jam'iyyun siyasar sun ce akwai buƙatar samar da kwamiti na musamman mai zaman kansa wanda zai ƙunshi wakilan jam'iyyun siyasa da na kungiyoyin fararen hula da kuma kwamitin majalisun tarayya wanda za a ɗora wa alhakin zaɓen sabon shugaban hukumar Inec.
"Shugaban ƙasa ne yake naɗa shugaban Inec da kwamishinoni, kuma shugaban ƙasa shi ma ɗantakara ne, don haka idan har ana son zaɓe ya tafi yanda ya kamata, dole sai an canza yadda ake naɗa masu kula da aikin zaɓe," in ji Injiniya Yabagi Sani shugaban jam'iyyar ADP kuma tsohon shugaban ƙungiyar gamayyar jam'iyyun siyasa ta IPAC.
Ya ƙara da cewa, ya kamata a ce idan har za a zaɓi sabon shugaban zaɓe a tallata ga masu buƙata su nema.
"Idan aka yi talla, waɗanda suka nuna suna so kuma aka tace daga nan sai a miƙa sunayensu ga majalisa," in ji Yabagi Sani.
Jam'iyyun siyasar dai na ganin idan har aka samar da wakilci daga ɓangarori da dama wajen zaɓen shugaban Inec zai dawo wa hukumar zaɓen da martaba da darajarta.
Sun kuma buƙaci a samar da hukuma ta musamman da za ta hukunta masu laifin zaɓe, suna masu cewa yin hakan zai rage laifukan da ake aikata lokacin zaɓe musamman sayen ƙuri'u da satar ƙuri'a da kuma maguɗi.
Farfesa MahmoodYakubu ya jagoranci hukumar Inec na tsawon shekara 10, tare da gudanar da manyan zabukan kasar biyu na 2019 da 2015.
Ya sanar da ajiye muƙaminsa a ranar Talata kafin cikar wa'adinsa na biyu.