Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaya barazanar ficewar Chadi daga rundunar haɗaka za ta shafi yaƙi da Boko Haram?
- Marubuci, Armand Mouko Boudombo, Isidore Kouwonou
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalists- BBC News
- Aiko rahoto daga, Dakar
- Lokacin karatu: Minti 4
Masu tayar da ƙayar baya da sauran ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai kan yi amfani da yankin Tafkin Chadi a matsayin wani sansani na kai hari ga ƙasashen da suke kewaye da tafkin - Najeriya, Nijar, Chadi, Kamaru - amma barazanar da shugaban Chadi ya yi ta fitar da ƙasarsa daga rundunar haɗakar sojin mai shekara 10 ka iya haifar da babbar illa idan har Chadin ta fice.
Shugaban ya yi wannan barazana ne bayan da aka kashe sojojin ƙasarsa sama da 40 a wani hari na kwanan nan da ake dangantawa da mayaƙan Boko Haram, bayan da ya kai ziyara sansanin Barkaram - wani tsauni da ke yankin na Tafkin Chadi. Shugaban ya bayyana ƙudurin ƙasarsa na farautar maharan.
A lokacin da ya yi barzanar ficewa daga haɗakar sojin, Shugaba Deby ya ce ƙungiyar ta hadin gwiwar soji ba ta da wani kyakkyawan tsari na gudanar da ayyukanta tare mambobinta wajen yaƙar Boko Haram - saboda haka ne ya ce ƙasar na duba yuwuwar ficewa daga haɗakar da ke aikin tabbatar da tsaro a yankin da ya kasance wata cibiya da ƙungiyoyi masu makamai ke addabar ƙasashen huɗu.
Yunƙurin Chadi na ficewa daga haɗakar na nuna tarin matsalolin da ƙungiyar ke fuskanta - wadda Farfesa Oumar Ba na Cibiyar nazarin harkokin diflomasiyya da dabaru a Paris, Faransa ya gaya wa BBC cewa, ba ta da tasiri sosai.
Wace riba za a samu a haɗakar?
Haɗakar sojin ta ƙasashe huɗu wadda ke da babban ofishinta a Chadi tana da dakaru kusan 10,000 a shekarar 2022.
A 2018 lokacin da ƙungiyar take da dakaru 8,000, Chadi ta bayar da 3,000 - mafi yawa bayan Najeriya wadda ta bayar da 3,250. Kamaru na da 2,250, sai Nijar mai sojoji 200, yayin da Benin ta kasance ta ƙarshe da sojoji 150, kamar yadda wani rahoto na makarantar nazarin harkokin soji ta ƙasa da ƙasa da ke Kamaru ta fitar.
Ficewar Chadi daga haɗakar zai iya sa ta rasa kaso na biyu mafi girma na dakarunta a lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da addabar yankin.
Ceidik Abba, mai bincike a kan harkokin tsaro ya gaya wa BBC cewa idan har Chadi ta tabbatar da wannan barazana tata, hakan zai zama gagarumin koma-baya ga haɗakar ganin irin jajircewa da tallafi da gudunmawar Chadi a yaƙi da masu tayar da kayar bayan a wannan ƙungiya.
Abba, wanda ya rubuta wani littafi kan sanin yadda ƙungiyar Boko Haram take, (‘Pour comprendre Boko Haram’), ya ce a yau Boko Haram ƙungiya ce da ke barazana ga ƙasashen wannan yanki gaba ɗaya.
Saboda haka akwai buƙatar haɗa kai tsakanin ƙasashen wannan yanki domin yaƙar ta.
Idan kuma ba haka ba duk wasu ƙungiyoyi na ta'addanci ka iya kwararowa wannan yanki daga ƙasashe daban-daban inda za su riƙa kai hari kasancewar sun samu gindin zama a nan.
A wani rahoto na 2020 da ƙungiyar sasanta rikice-rikice a duniya (International Crisis Group), ta fitar ta ce sojojin Chadi sun taimaka sosai wajen hana faɗaɗar ƙungiyar Boko Haram a 2015 da 2016, kuma ta matsa wa ƙungiyar sosai.
Wasu hare-hare da ƙasar ta kai a 2017 da 2018 da kuma ƙara matsa wa ƙungiyar da ta yi a 2019, sun taimaka wajen rage illar ƙungiyar tare da ceto farar hula da yawa da ƙungiyar ta kama, ko suka maƙale a yankunan da Boko Haram ɗin ke da iko da su, kuma hakan ya bayar da damar kai kayan agaji.
Ƙungiyar mai nazari kan rikice-rikice a duniya ta ƙara da cewa Boko Haram ta ci gaba da tasiri ne saboda ba dukkanin ƙasashen da ke cikin wannan haɗaka ta soji ba ne suke aiki tuƙuru kamar yadda Chadi ke yi.
Ta ce kusan wannan ne ya sa mayaƙan Boko Haram ke iya tserewa suna komawa yankin wata ƙasar.
Amma fa idan har Chadi ta fice daga haɗakar ta soji to fa ita ma sai dai ta tashi da gaske wajen yaƙar Boko Haram daga yankunanta da kanta.
Abin da ya sa haɗakar sojin ke fama
A 2019, marigayi Shugaba Idriss Deby – mahaifin shugaban Chadi na yanzu - ya nuna damuwarsu a kan yadda wasu ƙasashe ba su bayar da isassun sojoji ga ƙungiyar ta haɗin gwiwa.
An ruwaito shi yana cewa dakarun Chadi ne ke yawancin aikin ƙungiyar yayin da su kuma sauran ƙasashen suka mayar da hankali kan cikin ƙasarsu.
Wannan ya sa har yanzu yankin na Tafkin Chadi ya ci gaba da kasancewa inda ƙungiyoyi masu makamai ke ci gaba da riƙe yankuna da kuma ƙaddamar da hare-hare daga can.
Har yanzu wannan matsala ta rashin bayar da haɗin kan da ya kamata a tsakanin dukkanin ƙasashen da ke cikin haɗakar sojin, ita ce Chadi ke ƙorafi a kai.
Ƙungiyar ƙasashen tana fama da katutun matsaloli misali - ''Akawi ƙasashen da suka ƙi bayar da zaratan sojojinsu suka bar su don tsaron cikin gida,'' in ji mai bincike kan tsaro, Abba.
Haka kuma ya ce ƙungiyar ba ta da isassun kayan aiki na sufuri inda take da 'yan ƙalilan ɗin jiragen sama masu sauƙar ungulu na ɗaukar dakarun da aka ji wa rauni da kuma sintiri - inda wasu ƙasashen ke cewa ba su da jirage isassu da za su bayar.
Baya ga kayan aiki, bayar da kason kuɗi ma abu ne da ya kasance matsala ga ƙungiyar, inda wasu ƙasashe ba su bayarwa a kan lokaci.
Abba na ganin matsalar ita ce: ''Ta yaya za mu tabbatar da cewa dukkanin ƙasashen sun bayar da haɗin kai da ƙuduri bai ɗaya?"