Juventus ta ƙwallafa rai kan Tonali, wataƙila Lewandowski ya bar Barca

Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan tsakiya na Newcastle United da Italiya Sandro Tonali, mai shekaru 25, shi ne babban dan wasan da Juventus ke son saya a kakar wasa ta bana. (Gazzetta dello Sport)

Barcelona na tunanin bayar da dan wasan gaba na Poland Robert Lewandowski, mai shekaru 37, wanda kwantaraginsa za ta kare a lokacin bazara, ko ta tsawaita zamansa da kakar wasa guda bisa sharadin rage masa albashi. (ESPN)

Dan wasan Scotland Scott McTominay da Napoli za su yi tattaunawa kan tsawaita zaman ɗan wasan mai shekaru 29 har zuwa bayan 2028, inda ƙungiyar ta Serie A ke son tabbatar da cewa ɗan wasan tsakiya ya sabunta zamansa har zuwa 2030. (Gazzetta dello Sport)

Dan wasan Colombia Jhon Duran, mai shekaru 22, zai koma Zenit St Petersburg a matsayin aro bayan ya ƙare zamansa na kakar wasa a Fenerbahce daga Al-Nassr. (Talksport)

An ruwaito Leeds United na zawarcin sabon mai tsaron gida a lokacin bazara. An fahimci cewa Daniel Farke bai ji daɗin cinikin Lucas Perri da ya yi a lokacin bazara ba, wanda ya koma Elland Road a watan Yulin 2025 kan £13.9m. (Teamtalk)

Dan wasan gaban Tottenham mai shekaru 22, Alejo Veliz, wanda ke zaman aro a Rosario Central, zai koma kulob din Bahia na Brazil a lokacin bazara kan yarjejeniyar Yuro miliyan 9 (£7.8m) tare da ƙarin kuɗi. (Fabrizio Romano)

Atletico Madrid ta nuna sha'awar ɗan wasan tsakiya na Spain mai shekaru 23, Gabri Veiga, kwanaki kadan kafin rufe kasuwar musayan yan wasan kwallon kafa, amma Porto ta yi watsi da tayin (Fabrizio Romano)