Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rashford ba ya son komawa Man Utd, Sterling ya ƙi zuwa Jamus
Marcus Rashford, mai shekara 28, ba ya son komawa Manchester United idan wa'adin zamansa ya kawo ƙarshe a matsayin aro a Barcelona kuma ɗanwasan na Ingila zai amince a rage masa albashi don ya ci gaba da taka leda a Spain. (Mirror)
Tsohon ɗanwasan tsakiya na Liverpool Xabi Alonso ana tunanin yana cikin mutum uku da ake sa ran za su gaji Pep Guardiola yayin da ake ganin wannan ce kakarsa ta ƙarshe a matsayin kocin Manchester City. (Telegraph - subscription required)
Ɗanwasan gaba Dayot Upamecano, mai shekara 27, na shirin sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da Bayern Munich. (Fabrizio Romano)
Ɗanwasan baya na Manchester United Tyrell Malacia, mai shekara 26 na fushi da daraktan wasanni Jason Wilcox kan toshe damarsa ta barin Old Trafford. (Mirror)
Malacia na shirin hawa jirgi zuwa Turkiya a Besiktas kafin Wilcox ya fada masa cewa dole ya ci gaba da zama a Manchester United. (Talksport)
Tsohon ɗanwasan Chelsea da Ingila Raheem Sterling, mai shekara 31, an yi masa tayin zuwa Union Berlin a kwanakin baya amma ya ki amincewa. (Florian Plettenberg)
Ɗanwasan gaba na Faransa Karim Benzema, mai shekara 38, zai bar Al-Ittihad zuwa Al-Hilal ta Saudiyya. Benzema ya ƙulla yarjejeniya da Al-Ittihad ta shekara uku bayan ya baro Real Madrid a 2023. (The Athletic)
Tottenham ta kasa cimma yarjejeniya da Monaco kan Maghnes Akliouche, mai shekara 23, amma tana fatan sake taya ɗanwasan na Faransa a bazara. (Teamtalk)