Mece ce ranar "Boxing Day" kuma daga ina ta samo asali?

Lokacin karatu: Minti 2

A ranar 26 ga watan Disamban kowace shekara wato washegarin ranar Kirsimeti, ita ce ranar "Boxing Day" wato kenan ita ce rana ta farko bayan Ranar Kirsimeti

"Boxing Day" - ta samo asali ne a lokacin mulkin Sarauniyar Ingila Victoria a shekarun 1800.

Sunan ya samo asali ne sakamakon ƙunshe kyauta da masu arziki ke yi a cikin akwati kafin su bai wa mabuƙata - 'box' na nufin akwati a harshen Hausa.

Ranar ba ta da wata alaƙa da wasan damben "boxing" da ake gudanarwa a faɗin duniya.

Boxing Day a al'adance, ita ce ranar da bayi kan yi hutun aiki sannan su karɓi kyautuka na musamman daga iyayen gidansu.

Haka nan, a ranar ce su ma suke zuwa gida domin bai wa iyalansu akwatunan kyautar.

Yadda ake gudanar da ranar a Turai

A yankunan Catalonia na Spain da Ireland na Birtaniya, suna yin bikin ranar ne da sunan "Saint Stephen's Day", wata rana da ke zuwa washegarin Kirsimeti domin tuna wa da wani waliyyi da ake kira da Saint Stephen wanda shi ne shahidi na farko Kirista a tarihi.

A ƙasashen Turai kuma kamar Hungary da Jamus da Poland da Netherlands, suna kallon Boxing Day a matsayin Ranar Kirsimeti ta biyu.

Su ma coci-coci sun taka rawa wurin ƙirƙirar Boxing Day. Sukan karɓi kuɗi daga masu bauta a tsawon shekara baki ɗaya domin bai wa mabuƙata a lokutan Kirsimeti.

Sukan ajiye kuɗin a cikin akwatuna kafin a buɗe su a Ranar Kirsimeti, sai kuma a bai wa mabuƙata kwana ɗaya bayan Kirsimeti wato Boxing Day.

Sai dai a yanzu ba a fiya amfani da akwatunan ba kamar da.

Yadda ake bikin ranar a Najeriya

Najeriya kamar sauran ƙasashen duniya, mabiya addinin Kirista da ma sauran ƴan Najeriya sakamakon ayyana ranar a matsayin ranar hutu ta biyu da gwamnatin ƙasar ke bayarwa.

Bisa al'ada dai ƴan Najeriya musamman Kiristoci kan yi amfani da ranar wajen hutawa inda suke cika dandalin shaƙatawa a biranen ƙasar.

Wasu kuma na mayar da hankali wajen ziyarce-ziyarcen ƴan uwa da abokan arziƙi da kuma yin musayar kyautuka a tsakanin mabiya da ma Musulmi da ke maƙwabtaka da su.