Ko taron Putin da Xi da kuma Kim Jong Un zai zamo barazana ga Amurka?

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Alexey Kalmykov
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Russian
- Lokacin karatu: Minti 6
Vladimir Putin ya sake komawa China, amma wannan karon bisa wata manufa ta daban.
A karon farko tun bayan mamayar Ukraine, shugaban na Rasha na ziyarar babbar aminiyarsa, ba wai saboda alaƙarsa da Shugaba Xi Jinping ba - sai don matsayinsa na shugaban duniya mai ƙarfin faɗa a ji da ake ganin yana gogayya da shugaban Amurka - ƙasar da ake ganin na da ƙarfin tattalin arziki da na soji, kuma ake ganinta a matsayin babbar abokiyar hamayyar China.
Wannan ziyara za ta zama nasara ga Putin bayan ya dawo daga Alaska, inda Trump ya yi maraba da shugaban na Rasha a wani yanki na Amurka.
Putin ya lallashi Trump da ya yi watsi da buƙatarsa na hana Rasha ta kai wa Ukraine hare-hare da kuma yin watsi da barazanar sabbin takunkumi kan Rasha.
A China kuma, Putin zai samu gagarumar tarba - fiye da shugabannin ƙasashen yankin 12 ne za su gana a birnin Tianjin na ƙasar China domin halartar taron kwanaki biyu na Ƙungiyar Haɗin Kai ta Shanghai (SCO).
Daga cikin masu halartar taron har da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un - wanda ake ganin a matsayin ɗan adawar ƙasashen yamma, da kuma firaminsitan Indiya, Narendra Modi, wanda dangantakarsa da China da kuma Amurka ke da matuƙar sarƙaƙiya.
Somin taɓi
A ranar Laraba a birnin Beijing, da yawa cikin shugabannin za su halarci faretin soji a wani ɓangare na bikin cika shekara 80 da kawo ƙarshen yaƙin duniya na biyu, da kuma tunawa da murnar "nasarar da ƴan China a yaƙin turjiyar zaluncin Japan.
Don haka ko abubuwan da za su faru a China cikin makon nan na nuna alamar ƙarfafa ƙawancen da ke adawa da Amurka a duniya?
Ƙawancen Rasha da Indiya da kuma China da ake yi wa laƙabi da ƙungiyar ''RIC'' - wata magayya ce mai ƙarfi da aka kafa da manufar rage wa ƙasashen yamma ƙarfi a fagen siyasar duniya.
Sai dai ƙungiyar ta RIC - da ta ƙwashe kusan shekara biyar ba a ji ɗuryarta ba - ta sake farfaɗo da kanta a daidai lokacin da ake tsaka yaƙin kasuwanci da Trump ke assasawa.
'Trump ba zai haɗa Putin da Xi faɗa ba'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ziyarar ta Putin zuwa China - da ba a saba gani ba - na da aniyar nuna wa ƙasashen yamma cewa "ƙawance mai ƙarfi" tsakanin Rasha da China na inganta, kuma yunƙurin da Amurka ke yi na hana alaƙa a tsakaninsu ba zai yi nasara ba, in ji wasu masana.
Ko da Trump ya sallamar wa Putin da Ukraine tare da cire masa takunkumai, Rasha ba za ta juya wa China baya ba, a cewar masanan.
Masu sharhi sun yi nuni da yadda tsohon sakataren harkokin wajen Amurka, Henry Kissinger, ƙarƙashin shugaban ƙasar Amurka Richard Nixon, ya yi nasarar fitar da China daga ƙarƙashin ikon tarayyar Soviet a shekarun 1970, a lokacin da dangantaka tsakanin Beijing da Moscow ta yi tsami.
To sai sun ce abubuwa sun sauya a yanzu.
Pierre Andrieu, ƙwararre kan dangantakar China da Rasha a cibiyar manufofin jama'ar Asiya, kuma wanda ya yi aiki a matsayin jami'in diflomasiyyar Faransa a Rasha da Tajikistan da Moldova, ya ce "Ta hanyar ƙara matsin lambar kasuwanci kan China, gwamnatin Trump na ƙara ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu ne kawai.

Asalin hoton, Reuters
Ƙasar China ta zama babbar mai sayen makamashin Rasha, kuma ita ce ƙasar da ke samar da motoci da sauran kayayyaki ga Rasha bayan ficewar kamfanonin ƙasashen yammacin duniya.
To amma dangantakar ƙasashen biyu ta ƙara ƙarfi ne tun bayan mamayar Ukraine.
"Duka ƙasashen biyu suna adawa da mamayar ƙasashen Yamma, kuma suna ƙalubalantar 'mulkin Amurka'. Duka ƙasashen biyu masu karfin nukiliya ne kuma membobi na dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, manufofinsu sun zo dai-dai," in ji Andrieu.
''Ta fuskar tattalin arziki, suna taimakon junansu. Rasha ƙasa ce mai ƙarfin albarkatun ƙasa, yayin da China ƙasa ke da masana'antu da fasaha, "in ji shi.
Amma ya yi imanin cewa, kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin shugabanninsu ita ce mahimmiya.
Putin da Xi suna da abubuwa da yawa iri guda. Sa'anni ne ta fuskar shekaru, (72), dukansu sun girma a ƙarƙashin tsarin gurguzu na zamanin Soviet, kuma sun daɗe suna mulki. Dukansu sun gina mulkin kama karya kuma ba sa jure wa suka.
Kafin mamayar Ukraine a shekarar 2022, Putin ya rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya da Xi kan "ƙawance mai ƙarfi, da haɗin gwiwa ba tare da shinge ba". Xi ya kira Putin a matsayin "masoyin aboki". Ya gana da shi fiye da kowane shugaban duniya, sama da sau 40.
'Wannan ziyara ce ta musamman'
Har ila yau, China na cin gajiyar riƙe Putin na "ɗan gajeren lolaci" da kuma hana shi sake komawa ƙasashen yamma, amma ƙasar China ba ta son Rasha ma ta ƙara ƙarfi, in ji Patricia Kim, wata ƙwararriya kan manufofin ƙasashen wajen China da huldar Amurka da China a cibiyar Brooking da ke birnin Washington.
Kim ta ce, "Sakamakon da ya dace da Beijing shi ne, ƙasar Rasha mai karfin da za ta iya tunkarar ƙasashen Yamma, amma tana da rauni da za ta ci gaba da kasancewa a a matsayin rumfar China."
"Rasha babbar ƙawa ce ga China, tana taimaka wa Xi wajen tabbatar da zaman lafiya a gida da ma ɗaukacin yankin Asiya ta Tsakiya," in ji Andrieu.
"Yana taimaka wa Beijing wajen tattara tallafi daga Kudancin Duniya''.
Shigar Narendra Modi

Asalin hoton, Pablo Porciuncula/AFP via Getty Images
Memba na uku na haɗaƙar ƙungiyar RIC - Indiya - na da dangantaka mai ƙarfi da China da kuma Amurka a gefe guda, don haka zai iya inganta duk wani fata na farfaɗo da ƙungiyar.
Xi da Modi sun gana a gefen taron SCO a birnin Tianjin - wanda shi ne karo na farko da Modi ya je China cikin shekara bakwai.
Ba kasafai ƙasashen biyu ke magana ba tun shekarar 2020 da aka gwabza faɗa kan iyaka tsakanin ƙasashen biyu kan yankin Galwan.
Amma batun tattalin arziki ya canza gaskiyar da ke faruwa a ƙasa.
Trump ya sanya haraji mai tsauri kan kayayyakin Indiya a matsayin ladabtar da Delhi na ci gaba da sayen man Rasha, wanda ya ɓata wa tsoffin abokan gabar.
Xi ya shaida wa Modi cewa, ya kamata ƙasashen China da Indiya su kasance abokan juna, ba abokan hamayya ba, yayin da Modi ya ce yanzu akwai "zaman lafiya da fahimtar juna" a tsakaninsu.
Ƙasashen biyu ba mafiya yawan al'umma a duniya kawai ba ne, har ma da kasancewarsu daga cikin mafiya ƙarfin tattalin arziki a duniya.
Modi ya bayar da sanarwar cewa zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Indiya da China - da aka dakatar tun rikicin kan iyaka shekaru biyar da suka gabata - za su ci gaba, kodayake ba su sanar da lokacin fara hakan ba.
Xi ya ce, "ya kamata dukkan ɓangarorin su tunkari dangantakarmu bisa manyan tsare-tsare da kuma dogon lokaci" kuma "abin da ya dace ne ɓangarorin biyu su zama abokai".
Me hakan ke nufi ga makomar ƙawancen?

Asalin hoton, Reuters
Masu sharhi sun ce idan aka farfaɗo da ƙungiyar ta RIC yadda ya kamata - wanda ƙasashen Rasha da China suka ce suna son ganin ya faru - tare da wasu manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki a matsayin mambobinta, zai iya daƙile ƙaruwar tasirin Washington, tare da sauran ƙawance irin su ƙungiyar Brics (wanda aka ƙirƙira a 2006 tsakanin Brazil da Rasha da Indiya da China da kuma Afirka ta Kudu).
To sai dai, Indiya aƙalla dole ne ta aiwatar da wasu sauye-sauye masu yawa, duk da gaskiyar tattalin arziƙin harajin Trump.
Har ila yau, dole ne ta cimma matsaya kan wasu manyan batutuwan amincewa da ƙasar China.
Masana sun ce Indiya na da sha'awar kiyaye manufofin ƙetare mai cin gashin kanta.
Hakanan ana ci gaba da tunawa da ƙazamin faɗan kan iyaka da China.
Kuma Indiya ta damu da dangantakar kut da kut da China ke da ita da tsohuwar abokiyar hamayyarta Pakistan.
Wannan na iya zama wata dama ta ƙwace biyayyar da Indiya ke yi wa Amurka, tare da yin muba'ayarta ga ƙawancen adawa da Amurka.











