Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wakilin Amurka ya isa Qatar domin tattauna tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
- Marubuci, Yolande Knell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East correspondent
- Aiko rahoto daga, Jerusalem
- Lokacin karatu: Minti 5
Wakilin gwamnatin Amurka, Steve Witkoff, ya isa birnin Qatar don shiga tsakani domin tattaunawa tsakanin Isra'ila da Hamas kan tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da ke fuskantar ƙalubale.
A wannan makon ne wakilan dukkan ɓangarorin suka fara tattaunawa a karon farko tun bayan da Donald Trump ya ɗare karagar mulki a ranar 20 ga Janairu. Kwana 42 na zango na farko na yarjejeniyar tsagaita ya fara aiki ne a yammacin ranar da ya karɓi mulki.
A zango na farkon ne Hamas ta saki Isra'ilawa 25 da ta yi garkuwa da su, da kuma gawarwakin mutum takwas, inda suka yi musayarsu da fursunonin Falasɗinawa 1,8000 da kuma wasu ƴan ƙasar Thailand guda biyar. Zango na farko ya ƙare ne a 1 ga watan Maris.
Isra'ila tana fata Amurka za ta shige gaba wajen tsawaita yarjejeniyar ne da wata biyu, inda take fata za ta fara ta hanyar sakin rabin waɗanda Hamas ke riƙe da su.
Ita dai Hamas ta yi watsi da buƙatar hakan, inda ta buƙaci a shiga zango na biyu na asalin yarjejeniyar, wanda a ciki za a kawo ƙarshen yaƙin tare da janyewar dukkan sojojin Isra'ila daga Gaza.
Sai dai duk da haka ta ce za ta shiga cikin wannan tattaunawar da za a yi da "zato mai kyau."
Tun farkon wannan watan ne Isra'ila ta dakatar da shigar da duk wani kayan agaji - ciki har da abinci da fetur zuwa Gaza, inda ta ce ta yi haka ne domin tursasa Hamas ta amince da tsawaita yarjejeniyar.
Haka kuma an yanke wutar lantarkin kamfanin ruwan sha da ke ba yankin, wanda hakan ya sa ruwan shan yankin ya yi ƙarancin matuƙa.
Domin haka ne ƴan Houthi da ke Yemen suka bayyana a ranar Talata cewa za ta koma kai hare-hare a kan jiragen Isra'ila da ke wucewa ta tekun ƙasar, inda suka yi barazanar jefa harkokin sufurin yankin cikin matsala.
Ana dai ta nuna damuwa kan hana shigar da kayayyakin agaji Gaza da Isra'ila, inda har wasu daga cikin ƙawayenta suka yi gargaɗin hakan zai iya karya dokokin ƙasa da ƙasa.
Wani mai gidan burodi ya ce rashin shigo da fulawa da gas, ya sa dole ya kulle gidan burodinsa, wanda ke samar da aƙalla burodi 2,000, sannan wasu ma sun daina aiki a kudancin birnin Khan Younis.
Wata ɗaliba, Abu Mukhimer ta ce bai kamata a tsawaita zango na farko na yarjejeniyar ba, "kamata ya yi a tsara yadda za a kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya," in ji ta, inda ta ƙara da cewa, "abun ya yi yawa."
Duk da cewa Amurka ba ta tabbatar ba, amma Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce a ranar 2 ga watan Maris, Witkoff ya bayar da shawarar tsawaita zangon farko na yarjejeniyar zuwa wani ɗan lokaci domin watan Ramadan da kuma bikin Yahudawa na Passover.
Netanyahu ya ce Isra'ila ta amince da tsarin, domin a sako rabin waɗanda Hamas ke garkuwa da za a sake su, sannan a saki sauran daga baya.
An yi amannar cewa har yanzu akwai Isra'ilawa 24 masu rai a hannun Hamas, da kuma gawarwaki 35. Daga cikin waɗanda suke da rai da wani sojan Isra'ila ɗan Amurka mai suna Edan Alexander mai shekara 21, da kuma gawarwakin wasu Amurkawa huɗu.
Ita dai Hamas ta zargi Isra'ila da kawo tsaiko a tsarin yarjejeniyar ta farko.
A wajen ƴanuwan waɗanda aka yi garkuwa da su, babban burinsu shi ne ƴanuwansu su dawo.
Tun daga ranar Asabar, wasu daga cikinsu suke zaman dirshan a ma'aikatar tsaro da ke Tel Aviv domin kira da a sako musu ƴanuwa.
Ofri Bibas ƴaruwar Yarden Bibas ta bayyana a safiyar Litinin cewa, "akwai ƴanuwana 59 da suke cikin mawuyacin hali," in ji Ofri, inda take bayyana sauran waɗanda ke hannun Hamas baki ɗaya.
"Yarden ta dawo da rai, amma Shiri da yaranmu suma sun cancanci a dawo da su da ransu. A lokacin bikin Passover, dole ya kasance yana gida, kuma hanyar da za a dawo da kowa gida ita ce a dakatar da yaƙin baki ɗaya."
A wata ƙididdiga da tashar Channel 13 ta yi, ta gano cewa shugaban Amurka ya fi damuwa da waɗanda aka yi garkuwa da su, sama da Netanyahu.
Har zuwa yanzu, da Israila da Hamas babu wadda ke nuna sha'awar komawa fagen daga.
Amma dai a ƴan kwanakin nan, Isra'ila ta kai wasu hare-hare. A ranar Talata, an kashe mutum huɗu a Wadi Gaza, inda ake kira da lungun Netzarim - yankin sojojin Isra'ila suka janya bayan yarjejenyar tsagaita wuta.
Da yake zantawa da BBC, mahaifin wani yaro da aka kashe, Arafat Hana, ya ce ɗansa Omar bai aikata laifin komai ba.
Ya ce suna hanyar zuwa wani sansanin ƴan gudun hijira, inda suka taɓa zama a baya domin kwaso wasu kayayyakinsu ne aka kashe masa yaron.
Sabuwar barazanar da ƴan Houthi suka yi zai iya jefa yankin cikin rikici bayan an ɗan samu sauƙi tun bayan tsagaita wuta a Gaza a ranar 19 ga Janairu.
Sun yi amfani da jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami wajen kai hari kan sama da jiragen dakon kayayyaki guda 100 a cikin wata 15 daga watan Nuwamban 2023. Wasu daga jiragen ma ba su da alaƙa da Isra'ila.
Ƴan Houthin sun ce suna so ne su tursasa "Isra'ila ta bari a cigaba da shigar da kayan agazi Zirin Gaza."
Amma dai har yanzu babu alamar an kai wa wani jirgin hari.
Harin na farko da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoban 2023 ya ci sama da Isra'ilawa 1,200, mafi yawansu fararen hula, sannan ta yi garkuwa da mutum 251. Yawancin ƙananan yara da mata an sake su a zango na farko na yarjejeniyar.
Ramuwar gayya da Isra'ila ta yi a Gaza ne ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutum 48,500, mafi yawansu fararen hula, kamar yadda alƙaluman ma'aikatar lafiyar Hamas ta nuna, wadda Majalisar Ɗinkin Duniya ke amfani da su.