Salah ya zama na takwas a yawan ci wa Liverpool kwallaye a tarihi

Liverpool ta yi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Manchester United a wasan mako na uku a gasar Premier da suka kara ranar Litinin a Old Trafford.

United ta fara cin kwallo ta hannun Jadon Sancho minti shida da fara tamaula, haka suka je hutu da kwallo daya a ragar Liverpool.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne United ta kara na biyu ta hannun Marcus Rashford.

Mohamed Salah ne ya zare daya na 10 da ya ci United, ya zama na farko a Liverpool da ya zura 10 a kungiyar Old Trafford.

Haka kuma na 159 da ya ci wa Liverpool kenan jumulla, hakan ya sa ya zama na takwas a jerin wadanda ke kan gaba a ci wa Liverpool kwallaye a tarihi.

Ya kuma hau kan Micheal Owen, mai 158 a raga na tara a jerin wadanda suka ci wa kungiyar kwallaye da dama.

Ya kuma yi wannan bajintar a karo na 258 da ya yi wa Liverpool wasanni, tun bayan da ya koma Anfield daga Roma a 2017.

Cikin kwallayen da ya ci har da 120 a Premier League da 34 a Champions League da hudu a FA Cup da daya a Community Shield.

Wanda ke gaban Salah a Liverpool a yawan cin kwallaye shi ne Sir Kenny Dalglish, wanda yake na bakwai mai 172 a raga.

Jerin wadanda ke kan gaba a yawan cin kwallaye a Liverpool

1 – Ian Rush – 346 goals

2 – Roger Hunt – 285

3 – Gordon Hodgson – 241

4 – Billy Liddell – 228

5 – Steven Gerrard – 186

6 – Robbie Fowler – 183

7 – Kenny Dalglish – 172

8 – Mohamed Salah – 159

9 – Michael Owen – 158

10 – Harry Chambers – 151

Liverpool tana da maki biyu a wasa uku da ta yi a Premier League, bayan canjaras 2-2 a gidan Fulham da 1-1 da ta yi da Crystal Palace a Anfield.

Ranar 27 ga watan Agusta Liverpool za ta karbi bakuncin Bourneemouth a wasan mako na hudu a babbar gasar tamaula ta Ingila.