Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana nuna mana bambanci a Saudiyya – Alhazan Najeriya
Wasu Alhazan Najeriya sun yi zargin cewa an nuna musu bambanci a zaman da aka yi na Muzdalifa a lokacin aikin Hajjin bana a Saudiyya.
Wadanda BBC ta zanta da su sun ce akwai bambanci tsakanin abubuwan da hukumomin na Saudiyya ke tanadar wa alhazan Najeriya da wadanda ba ‘yan Najeriya ba.
Daya daga cikinsu, Abubakar Baban Gwale, ya ce “A filin Muzdalifa za ka ga a wurin wasu kasashen akwai shimfida, amma mu (Najeriya) babu shimfida, sai dai ka nemo kwali ka kwanta a kai.”
Dama dai alhazan na kokawa kan gazawar hukumomi wurin tanadar musu da abubuwan bukata yadda ya kamata.
Sun yi zargin cewa akwai karancin masu kula da lafiyarsu da kuma abinci.
Mahajjatan sun ce a duk lokacin da suka koma tantunan kwanansu daga wurin jifan shaidan (Jamrah) ba sa samun abincin da ya kamata.
Wata Hajiya da BBC ta zanta da ita ta ce a kullum shinkafa ake ba su, sannan ba a tanadi abinci na masu lalurar ciwon suga ba.
Bugu da kari ta ce babu tuwo, wanda shi suka fi bukata idan aka kwatanta da sauran abinci.
Shugaban hukumar alhazan Najeriya Alhaji Zikirullah Kunle Hassan ya tabbatar da matsalar.
Ya ce laifin na cibiyar da take kula da dawainiyar alhazai ce ta Saudiyya wadda ake kira Mu’assasa.
Ya kuma ce hukumar alhazan ta Najeriya ta rubuta koke kan batun.
Haka nan hukumar ta bukaci a biya Najeriya kudaden da ta bayar a bangaren abinci, kasancewar ba a samar da abincin da ya kamata ba.