Aikin Hajji: 'Ba mu taɓa ganin shirin Aikin Hajji mai ƙarancin hada-hada kamar bana ba'

Ƙasa da mako guda a fara gudanar da aikin Hajjin bana a ƙasa mai tsarki, Hukumomin Saudiyya na ci gaba da shirye-shirye don aiwatar da wannan muhimmiyar ibada bana.

Mutum 10,000 ne kawai za su yi ibadar a bana, kuma waɗanda ke zaune a Saudiyya kawai, ciki har da 'yan ƙasar da kuma wasu da suke je Saudiyyan daga ƙetare.

An rage yawan masu zuwa ibadar aikin Hajjin ne saboda annobar korona wadda ta addabi al'ummar duniya.

Wani dan Najeriya mazaunin birnin Madina, Muhammad Ibrahim, ya shaida wa BBC cewa ko da yake al'amura sun fara kankama, amma babu hada-hada kamar yadda suka saba gani a shekarun baya.

Ya dai musanta raɗe-raɗin da wasu ke yaɗawa cewa kafin a zaɓi mutumin da ya dace don gudanar da Hajjin bana sai ya yi rantsuwa cewa bai taɓa yin aikin ba. "A'a ba wani rantsuwa".

"Idan suka ba ka takardar da za ka shigar da bayananka, da ka saka ma, za su gani. Ka taɓa yi, ko a'a. Ko kuma ya yanayin shekarunka ko kana da wata cuta babba...kamar hawan jini ko ciwon suga haka,"

Duk za su gani, in ji Muhammadu Ibrahim. Ya ƙara da cewa akwai ɗumbin mutanen da ba za su taɓa gudanar da Aikin Hajji ba, kuma sun sa rai a bana.

"Amma da wannan adadi na 10,000 wa za a ɗauka, wa za a bari? Ai sai wanda Allah Ya rubuta ne kawai zai yi Hajjin bana gaskiya," in ji shi.

Ya ce a iyakar saninsa ba wani fifiko da ake nunawa wajen zaɓar mutanen da za au yi Hajji, ba wani zaɓen sai manyan mutane, kawai dai sai mai tsananin rabo.

Sahun farko na maniyyatan da za su gudanar da ibadar ya sauka a birnin Makkah ranar Asabar, kamar yadda hukumomin kasar sukasanar.

Bayan cika ka'idoji, an tafi da su zuwa masaukansu da aka tanada, karkashin kulawar ma'aikatar aikin Hajji da Umara ta Saudiyya.

Za su zauna a nan tsawon kwana hudu, kafin fara gudanar da ayyukan ibada a ranar Alhamis 30 ga watan Yuli.

Sharuddan da hukumomin Saudia suka gindaya na aikin Hajji a wannan shekara.

  • Za a yi wa alhazan gwajin cutar korona kafin su fara aiki, sannan za a killace su bayan an kammala aikin.
  • Mazauna kasar da 'yan kasar 'yan kasa da shekara 65 ne kawai za su gudanar da aikin hajjin bana.
  • Ba za a bar utanen da ke fama da munanan cututtuka kamar su ciwon suga da ciwon zuciya su yi aikin hajjin ba.
  • Za a dinga sa ido kan yanayin lafiyar kowane mahajjaci.
  • Za a dinga gudanar da ayyukan matakan aikin hajji rukunu-rukuni na mutane kadan-dkadan saboda tabbatar da dokar yin nesa-nesa da juna.
  • Yawan wadanda za su yi aikin hajjin bana ba za su haura 10,000 ba.
  • Babu wanda zai je Saudiyya don yin aikin hajji daga wasu kasashen.
  • Za a bude asibiti na musamman a Makkah don ayyukan gaggawa.

A bana dai an yi tunanin cewa hukumomin Saudiyya za su haramta gudamnar da aikin Hajji a wannan shekara saboda yadda cutar korona ke cigaba da yaduwa kamar wutar daji, amma sai aka wayi gari a watan da ya gabata, hukumomin kasar sun bayar da wadannan sharudda ga masu gudanar da ibadar.

Karin bayani akan aikin Hajji

Aikin Hajji, daya ne daga cikin shikashikan Musulunci biyar, da ake wajabta wa Musulmai masu hali su yi ko da sau daya ne a rayuwarsu.

Ana gudanar da aikin Hajji ne a kwanaki biyar wanda ake farawa daga 8 ga Zul Hajji zuwa 12 ko 13 ga watan.

A duk shekara sama da mutum miliyan biyu da rabi ne ke gudanar da aikin Hajji a Saudiyya, wanda shi ne taro mafi girma a duniya.

Sai dai a bana annobar korona ta sauya al'amura, har ta kai ga hukumomin Saudiyya sun sanya wasu bakin ka'idoji