Ko taron Ecowas a Abuja zai samar da mafita ga Nijar?

Asalin hoton, Others
Ministocin harkokin wajen kasashen mambobin kungiyar Ecowas za su yi taro a yau Alhamis, karon farko bayan kasashen Nijar da Mali da Burkina da kuma Burkina Faso sun sanar da ficewarsu daga kungiyar, yayin da a bangare guda kuma shugaban kasar Senegal, Macky Sall ya dage babban zaben kasar.
Taron Ministocin zai iya zama sharar-fage ga taron da shugabannin kasashen kungiyar za su yi don tunkurar wadannan matsalolin.
Taron, kamar yadda wata sanarwar da kungiyar Ecowas din ta wallafa a shafinta na intanet ta nuna, taro ne na musamman da ya kunshi `yan kwamitin shiga-tsakani da majalisar tsaro a matakin ministoci, wanda sanarwar ta ce za su yi zama da nufin tattaunawa a kan halin da yankin Afirka ta yamma ya samu kansa a ciki ta fuskar tsaro da wasu matsaloli da suka jibanci siyasa.
Tun a ranar 28 ga Janairu ƙasashen Mali da Burkina Faso da Kuma Nijar suka sanar da aniyar ficewa ƙungiyar Ecowas.
Kuma a ranar Laraba ƙasashen uku da dukkaninsu sojoji ne suka ƙwaci mulki bayan kifar da gwamnatin farar hula sun jaddada matakin ficewa daga Ecowas kafin taron ƙungiyar.
Mali da Burkina Faso da Nijar sun fice ne sakamakon takunkuman kariyar tattalin arziki da Ecowas ta kakaba ma su bayan juyin mulki da sojoji suka yi.
Masana siyasa kamar Farfesa Jibrin Ibrahim na ganin ya kamata shugabannin kungiyar su yi kaffa-kaffa, su mai da hankali wajen lalamar 'ya'yan kungiyar idan ba haka ba garin gyaran gira a rasa ido.
Masanin ya ce ƙungiyar Ecowas tana cikin matsala sosai saboda ƙasashe huɗu daga ciki sun fita daga tsarin dimokradiyya, ga kuma Senegal ta shiga wani hali inda aka jefar da kundin tsarin mulkin ƙasar.
"Idan har za a asamu ƙasashe 5 cikin 15 suna cikin irin wannan matsalar, to ƙungiyar ma za ta iya rushewa baki ɗaya, kuma batun tsaro zai ƙara lalacewa," in ji farfesa Jibrin Ibrahim.
Duk da cewa tun da farko shugabannin kungiyar Ecowas din sun cije a kan matsayinsu na dakatar da kasashen da suka bijire wa demokuradiyyar tare da sanya musu takunkumi, Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce ba gazawa ba ce idan suka sassauta domin a samun maslaha.
"Dole ne Ecowas ta nemi hanyar da za a tattauna da su a nemi mafita, ba wai a nuna ma su ƙarfi ba, an bari sun fita kuma hakan matsala ce ga dukkan ƙasashen yammacin Afrika, saboda ƙarfinsu dukansu na raguwa, dukkan su suna cikin yunwa, saboda haka ɓaraka ba za ta iya gyara abin da ya lalace ba," In ji masanin.
Mene ne fatan ƴan Nijar ?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da cewa akwai mabambantan ra'ayi tsakanin al'ummar Nijar da masu goyon bayan sojoji da kuma akasin haka, amma kuma tasirin takunkumin Ecowas ya shafi kowa.
Kassoum Moukhtar, wanda tsohon minista ne a gwamnatin Shugaba Bazoum da sojoji suka kifar a Nijar ya ce akwai bukatar shugabannin CEDAO su rumgumin salon cizawa da hurawa, kuma wani matakin maimakon ya zama silar mafita zai kara jefa kungiyar yake yi cikin rudani:
"Takunkumin tsawon wata bakwai yana wa al'ummarmu ta Nijar azaba, saboda haka ya kamata su janye shi, idan sun lura za su ga koda suka saka takunkumin mutanen Nijar ba su daina goyon bayan sojawan ba haka ke nuna matakin da Ecowas ta ɗauka al'umma ba ta yarda da shi ba."
"Ya kamata ƙungiyar Ecowas ta kasance ta al'umma a bi hanyar da za a samu maslaha," cewar Kassoum Moukhtar.
Ƴan Nijar da dama dai na fatan su ji alheri, taron ya zama dalilin janye wa ƙasarsu takunkumin Ecowas
"Muna fatan wannan zama ya zama Alheri ga mutanen Nijar saboda an wahala, kuma talaka shi ke ji a jikin shi," cewar wani ɗan Nijar.
Ƙasashen Mali da Niger da Burkina Faso dai na zargin cewa babu abin da zamansu a Ecowas ya tsinana musu. Kuma yanzu dole sai Ecowas ta saurari wasu bukatun shugabannin sojin ƙasashen idan har tana son su dawo cikin ƙungiyar.











