Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mata masu shayarwa da ke fafatawa a gasar Olympic
- Marubuci, Nishat Ladha
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
- Marubuci, Marina Daras
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
- Lokacin karatu: Minti 6
“ Na yi kuka sosai a lokacin da aka ɗauke mu a motar bas zuwa sansanin ƴan wasa. Ba abin da nake yi sai kallon bidiyo da hotunan ƴata. Da na isa sansanin ba na iya bacci ba tare da ita ba.”
Lokacin da ƴar tseren yada-ƙanin-wani Aliphine Tuliamuk ta tashi zuwa gasar Olympics ta Tokyo a 2021, abu ɗaya da yake a zahiri shi ne cewa - ba za ta je sansanin gasar da ƴarta ƴar wata shida, Zoe, ba.
Gasar ta kasance a lokacin da ake tsaka da annobar Korona, kuma gasar da Tuliamuk za ta yi za ta kasance ne a birnin Sapporo na arewacin Japan.
Hakan na nufin Tuliamuk za ta iya kasancewa da iyalinta - sai dai kawai lokacin da ta kasance cikin damuwa shi ne, daren farko da ta kasance a sansanin da ƴan gasar suka zauna a Tokyo inda aka haramta zuwa da yara.
Saboda haka ne aka raba ta da jaririyarta mai wata shida wadda take shayarwa
“Karon farko da na yi bacci ba tare da Zoe ba shi ne a sansanin.
Zoe da mijna sun zauna a otal. Wannan abu ne mai wahalar gaske," Tuliamuk ta bayyana a hirarta da BBC.
"Na damu sosai - na kira su sai na ji tana ta kuka, saboda ba ta san dalilin da ya sa babarta ba ta nan ba."
Wannan ne dalilin da ya sa ƴar tseren ta Amurka haifaffiyar Kenya ta yi maraba da tsarin da aka ɓullo da shi na barin mata masu shayarwa da masu kula da jariransu su halarci gasar Paris 2024, ciki har da samar da wani waje na yadda mata za su iya ganawa da jariransu a sansanin.
“Ina matuƙar farin ciki cewa cikin shekara huɗu kawai daga lokacin da ba zan iya kasancewa da jaririyata ba, an samu sauyi inda yanzu za ka iya kasancewa da su. Wannan babban cigaba ne."
Me gasar Paris 2024 ta sama wa mata masu shayarwa da masu kula da jariransu?
Batun lokacin da mace da ke gasar za ta daina shayar da jaririnta na ɗaya daga cikin abubuwan da Tuliamuk, da ire-irenta suka yi fama da shi.
Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta bayar da shawarar bai wa jariri nonon uwa zalla tsawon wata shida na farko, sannan a ci gaba da shayar da shi haɗi da isasshen abinci har zuwa shekara biyu ko sama da haka.
"Zan shayar tsawon wata uku ko huɗu, wanda wannan zai ba ni kusan wata biyu da rabi kafin gasar Olympics," in ji Tuliamuk.
"To amma ina haihuwa sai na fahimci cewa dakatar da shayarwa ba abu ne da zan iya ba. Abu ne da nake matuƙar so."
Wannan na daga cikin abubuwan da suka sa hukumar wasan Olympics ta duniya da masu shirya gasar ta birnin Paris ta shekarar nan, a karon farko a tarihin Olympic suka samar da waje na musamman na zuwa da yara gasar.
“Mun yi nazari sosai daga abubuwan da suka faru a gasar Tokyo da sauran waɗanda aka yi a baya, muka yi tunanin kawo wani sauyi mu inganta gasar,” kamar yadda Emma Terho, ta hukumar gasar ta Olympic ta sheda wa BBC.
Muna da tarin mata matasa da ke da jarirai ƙanana, da kuma mata da ke ci gaba da sana'arsu ta wasan bayan sun haihu.
“Mun lura cewa za su fi mayar da hankali sosai a gasar idan akwai wuraren da za su iya ganin jariransu da masu kula da jariran a wajen gasar.”
Saboda haka ne aka samar da wani waje na musamman a sansanin gasar, inda mai shayarwa za ta iya samun ganin jaririnta a keɓe, ta tatsi nono a ajiye domin bai wa jaririn da dai sauran abubuwa na kula da jaririn.
Akwai damar ma da mai shayarwa za ta iya kwana a wajen tare da jaririnta, idan har hukumomin shirya gasar na kasashe suka yarda su samar da kuɗaden gudanar da su.
Tsohuwar ƴar gasar Olympic ta huturu, Terho, ta ce akwai tsarin da mai shayarwa da ke matuƙar buƙatar wajen za ta iya nema a bata.
“Muna son mu tabbatar da cewa akwai wajen da masu shayarwa da ke gasar za su iya kasancewa cikin sirri, kuma su mayar da hankali a kan gasar," in ji ta.
To amma ina ga wuraren da ake gasar ta Olympic?
Tuliamuk ta ce wurin gasar tseren Sapporo a 2021 ba a tsara shi yadda mata masu shayarwa da ke gasar za su iya kasancewa da jariransu ba.
Bayan da aka samu sauyi saboda zafi, ba ta samu damar shayarwa a otal ɗin da jaririyarta da mai kula da ita da kuma mijinta suke ba.
“Na je inda za mu yi tseren inda muke da tanti na tawagar ƴan wasan Amurka, to amma ba wajen da za ka shayar da jariri ko inda za ka tatsi nono," in ji ta.
“Da zan so na je banɗaki na tatsi nonon, to amma lokaci ya ƙure.
"Da zai yi kyau a ce akwai wani waje na sirri , to amma ba wanda ya yi tunanin cewa za a samu mata masu shayarwa da ke gasar."
Fafutukar neman canji
Terho ta ce haɗin kai da aka samu tsakanin hukumar Olympic ta duniya da takwararta ta gasar Paris, shi ya taimaka wajen tabbatar da wannan sauyi, inda gwarzuwar tseren mita 200 ta gasar Olympic, Allyson Felix ta Amurka, wadda a yanzu ta yi ritaya, take kan gaba wajen tabbatar da waɗannan sauye-sauye.
Ita ma tauraruwar kokawar judo Clarisse Agbegnenou, wadda ta ci lambar zinariya biyu ta Olympic, ita ma ta nemi a samar da dama ga mata masu shayarwa, a garinta kasancewar ta shayar da jaririyarta, Athena, ita ma.
“Ba na jin daɗi idan na ji mutane na cewa 'Abu ɗaya kawai za ku iya yi a lokaci guda', 'Ba za ki iya kasancewa a gasa ba kuma kina shayarwa, Agbegnenou, na kokawa.
ba matan ba ne kaɗai ke wannan fafutuka ta neman canji.
Tsohuwar ƴar tseren Amurka, Alysia Montano na daga cikin masu wannan gwagwarmaya, kasancewar ta taɓa shiga gasar ƙasa a 2014 a Sacramento, lokacin tana da cikin wata takwas.
Montano ta bayyana irin nasarorin da ta samu tare da tawagar Amurka yayin da take da jaririya, da kuma iin matsaloli da ƙalubalen da ta fuskanta a wannan yanayi.
Sakamakon irin ƙalubalen da ta fuskanta da kuma na matan da take goya wa baya a wannan fafutuka, Montano, ta ce sauyin da aka samu a gasar Paris 2024, wani cigaba ne.
Ta farko a tarihin gasar Olympic - to amma hakan ya isa?
Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen mata masu shayarwa, da ke son amfani da wurin da aka samar na musamman da za su iya zuwa su kwana da jariransu shi ne yadda za su shawa kan hukumomin kasarsu su samar da kuɗin tafiyar da wurin.
Terho , ta hukumar shirya wasannin Olympic ta duniya, ta ce hukumar tana nazarin yuwuwar samar da hakan a wasannin Olympic nan gaba, amma da farko sai an ga irin yadda tsarin ya kasance a gasar Paris.
To amma ga masu fafutuka irin su Montano, akwai buƙatar ƙara azama kafin gasar Olympic ta gaba ta Los Angeles 2028.
Montano ta ce, za ta so ta ga an samar da wurare na sirri da suka dace a filayen wasanni, inda mata masu shayarwa za su iya zama cikin tsanaki su tatsi nononsu su ajiye domin amfanin jariransu.
Haka kuma tana son ganin an sama da damar da mata masu shayarwa za su iya kasancewa da masu kula da jariransu tsawon lokacin da suke gasar.
Tuliamuk, wadda ba ta samu damar shiga gasar Paris 2024 ba saboda rauni, wadda kuma take fatan zuwa gasa ta gaba ta birninLos Angeles, LA 2028, tana fatan ganin ta samu tallafin da take buƙata, idan ya kasance ta sake haihuwa a lokacin.
Ta ce kasancewar mace mai shayarwa tare da jaririnta, ba abin da yake sauyawa, hasali ma mace na kasancewa cike da ƙwarin gwiwa a gasa.
Ta ce: “Mun ga abin da uwaye mata za su iya yi idan aka ba su goyon baya ɗari bisa ɗari. Ya kamata mu ci gaba da wannan.”