Abin da ya sa samun nasarar Democrats a Majalisar Dattawan Amurka ke da muhimmanci

Asalin hoton, Reuters
Yunƙurin jam'iyyar Republican na samun rinjaye a majalisar dattawan Amurka ya gamu da cikas, yayin da jam'iyyar Democrats ta ci gaba da samun rinjaye a zauren majalisar.
Kwanaki huɗu bayan miliyoyin Amurkawa sun fito domin kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen rabin wa'adi, nasarar da Catherine Cortez Masto ta samu da ƙaramin rinjaye a jihar Nevada ranar Asabar da yamma shi ne ya kawo ƙarshen kokawar samun rinjaye a majalisar dattawan Amurka.
A yanzu Jam'iyyar Democrats na da rinjaye da kujeru 50, yayin da Republican ta samu kujeru 49 a Majalisar Dattawan Amurka.
A yanzu ko da Jam'iyyar Republican ta samu nasara a zaɓen kujerar sanata ta jihar Georgia da ba a kammala ba, ƙuri'ar mataimakiyar shugaban ƙasar Kamala Harris za ta bai wa Jam'iyyar Democrats rinjaye a majalisar.
Haka aka yi ta fama a shekaru biyun da suka gabata - kuma wannan zai buɗe wa shugaban ƙasa Joe Biden hanya wajen cika manyan kotunan ƙasar da mutanen da ya ga damar naɗawa ba tare da samun cikas ba.
Abu mafi muhimmanci shi ne idan alkalin kotun ƙolin ƙasar ya yi ritaya ko ya mutu, 'yan Republicans ba za su iya hana Shugaba Biden naɗa wanda yake so ba.
'Yan Jam'iyyar Democrats ba za su manta da shekarar 2016 ba, inda shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa na lokacin Mitch McConnell ya hana tantance mutumin da Barack Obama ya so naɗawa a matsayin alkalin kotun ƙolin ƙasar ba.
Nasarar Democrats a jihar Nevada ya nuna cewa zaɓen kujerar jihar Georgia da za a sake ranar shida ga watan Disamba ba shi da wani muhimmanci ta fuskar rinjaye a majalisar dattawan.
Mista Biden ya ce ''abu ne mai sauƙi'' ga Jam'iyyar Democrats ta samu kujeru 51. Abin da zai sa jam'iyyar ta ci gaba da riƙe rinjayen majalisar, hakan kuma zai taimaka wa jam'iyyar samun nasara a zaben 2024.
End of Karin labarai masu alaƙa
To sai dai duk da cewa babu tabbas, har yanzu akwai yiyuwar Jam'iyyar Republican ta samu rinjaye a majalisar wakilan ƙasar, abin da kuma zai ƙara kawo wa Shugaba Biden cikas a wasu ɓangarorin.
Ƙudurorinsa za su fuskanci cikas a majalisar, domin kuwa zai fuskanci ƙalubale mai yawa daga 'yan jam'iyyar Republican, to amma duk da haka zai samu sauƙi, idan 'yan jam'iyyar Republican suka kasa ɗinke ɓarakarsu ta cikin gida.
Sakamakon wannan zaɓe - na tsakiyar wa'adi mai cike da tarihi - na ci gaba da bayyana.
Kuma tuni wasu ke ganin an kassara siyasar Donald Trump, duk da cewa har yanzu akwai sauran rina-a-kaba.
Ƙimar Shugaba Biden a jam'iyyarsa ta ƙaru. Sannan yanayin siyasar Amurka ya sauya a kan yadda aka san shi a mako guda da ya gabata.











