Wane ne Ron DeSantis, mutumin da Trump ya yi barazanar tona asirinsa idan ya tsaya takarar shugaban Amurka?

DeSantis

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnan Florida Ron DeSantis ya sake lashe zaben kujerar gwamnan Jihar da gagarumin rinjaye inda ya samu kuri'a biye da miliya daya da rabi, abin da ya sa ake hasashen cewa dan jam'iyyar ta Republican zai iya neman kujerar shugaban kasar nan da shekara biyu masu zuwa.

Ana kallonsa a matsayin mutumin da ya fi samun nasara a zaben rabin wa'adin zango da aka gudanar ranar Talata a Amurka kuma ana ganin shi ne zai iya fafatawa Donald Trump a zaben fitar da gwani na jam'iyyarsu a takarar kujerar shugaban kasar da za a yi a 2024.

Mr DeSantis sabon shiga ne a harkokin siyasa amma ya yi fice a fadin kasar bayan ya zama gwamnan Jihar Florida a 2019.

Awanni kadan gabanin soma kada kuri'a a zaben rabin wa'adin zangon, Donald Trump ya gargadi Mr DeSantis da kada ya kuskura ya shiga takarar shugaban kasa a 2024, yana mai cewa hakan zai yi wa jam'iyyar Republican illa.

"Ina ganin zai yi kuskure. Ina tsammanin masu zabe ba za su so hakan ba," a cewar tsohon shugaban na Amurka a tattaunwarsa da Fox News.

Mr DeSantis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An haifi Mr DeSantis a garin Jacksonville da ke Jihar Florida a shekarar 1978, kuma ya yi digirinsa a fannin tarihi a Jami'ar Yale

Da alama ra'ayinsa nan manyan batutuwa masu jawo ce-ce-ku-ce irin su jinsi, koyar da wariyar launin jinsi a makarantu da kuma zubar da ciki, sun samu karbuwa a wurin masu kada kuri'a, domin kuwa rahotanni na cewa ya samu karin mutanen da suka zabe shi daga kowanne bangare na al'umma.

Daga Yale ya zama gwamna

A matsayinsa na dan shekara 44, Mr DeSantis sabon shiga ne a harkokin siyasar Amurka, bayan an zabe shi a karon farko a kujerar dan majalisar dokokin kasar a 2012. Shekaru shida bayan haka a 2018 - bayan ya sha kaye a yunkurin zama dan majalisar dattawa - ya zama gwamna.

An haifi Mr DeSantis a garin Jacksonville da ke Jihar Florida a 1978, kuma ya yi digirinsa a fannin tarihi a Jami'ar Yale University - inda aka nada shi a matsayin kaftin na kwallon kwando - sannan ya ci gaba da karatu a Jami'ar koyon aikin lauya ta Harvard Law School.

A shekararsa ta biyu a Harvard, ya zama sojan ruwan Amurka sannan aka ba shi mukamin mai kula da makaman da aka halasta rike su.

Ayyukansa sun hada da aiki tare da mutanen da aka daure a kurkukun Guantanamo Bay, da kuma matsayin mai bayar da shawara ga zaratan rundunar sojan ruwan Amurka da aka aika Iraki.

An sallami Mr DeSantis daga aikin soji cikin martaba a 2010, ko da yake ya ci gaba da aiki a matsayin sojan ruwan Amurka na ko-ta-kwana. A lokacin ne ya hadu da matarsa, Casey, wadda 'yar jarida ce a wani gidan talabijin kuma wacce ta warke daga cutar kansa, kuma ta taimaka wurin tara kudi don taimaka wa mutanen da mahaukaciyar guguwar Hurricane Ian a 2022.

Ron da Casey DeSantis a wurin wani taro a watan Mayun2022.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, DeSantis ya auri matarsa Casey, 'yar jaridar talabijin, a 2010
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jaridar the New Yorker ta bayyana ma'auratan da kuma 'ya'yansu a matsayin "wadanda suka shirya yakin zabe", kuma ta ambato wani abokin aikin Mr DeSantis yana cewa "sun yi kama da fitattun 'yan fim".

Bayan ya gama aikin soja, Mr DeSantis ya zama mai shigar da kara na gwamnatin tarayya. A shekarar 2012 ya shiga fafutukar neman kujerar majalisar dokokin jiha a Florida, daya daga cikin jihohin masu tsattsauran ra'ayi.

Lokacin da ya shiga harkokin siyasar Florida, Mr DeSantis ya fi mayar da hankali ne wurin ganin an kafa gwamnati "mara jami'ai da yawa" da kuma rage haraji - sannan ya bayyana adawarsa da gwamnati Obama administration. Kazalika ya soki abin da ya kira shirin gwamnati na tsoma baki kan "kusan kowanne al'amari".

"Babban burina shi ne na dakatar da Barack Obama," a cewarsa a wani jawabi da ya gabatar a wurin taron masu tsattsauran ra'ayi a Texas a watan Fabrairu.

A 2018, shekara biyar bayan ya zama dan majalisar dokokin Amurka - inda ya taimaka aka kafa kungiyar 'yan majalisu ta "Freedom Caucus" masu tsattsauran ra'ayi - Mr DeSantis ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna, inda ya samu cikakken goyon bayan shugaban kasar na wancan lokacin Donald Trump.

An rantsar da shi a matsayin gwamna a watan Janairun 2019.

Gwamna DeSantis ya fuskanci kalubalen annoba

Kalubale na farko da Mr DeSantis ya fuskanta a matsayinsa na gwamna ya faru ne a 2020, a yayin da annobar korona ta barke. A watan Afrilu ya bayar da umarnin rufe dukkan fadin jihar, ya kafa daruruwan cibiyoyin gwajin cutar sannan ya umarci miliyoyin mutane su rika sanya takunkumi - wanda a fili ya bayyana cewa "zai iya zama rigakafin kamuwa da cutar ga masu kasadar kamuwa da ita".

Sai dai a watan Afrilun 2020, Mr DeSantis ya soma dage takunkuman da ya sanya wa mutane kuma a watan Yuli - duk da kakkausar sukar da yake sha - ya bayar da umarnin sake bude makarantu.

"Ya yi suna ne sakamakon cutar korona, a matsayin mutumin da ya ja hankalin kasar baki daya," a cewar Sarah Longwell, wata mai tsare-tsare a jam'iyyar Republican wadda kuma ta kafa kungiyar da ke yaki da Trump ta Republican Voters Against Trump, a hirarta da BBC. "Mutane da dama a jihar sun ji dadin abubuwan da ya yi."