Ƴan sandan Kenya sun tono gawar mutum 21 da ake zargin Fasto ya sa su azumin mutuwa

‘Yan sanda a Kenya sun ce sun tono gawarwakin mutane 21 a yayin binciken da suke yi a kan wata kungiyar addinin Kirista, wadda aka yi zargin cewa jagoronsu ya bukaci mabiyan da su yi azumi har su mutu domin su hadu da Yesu Almasihu.

Gawarwakin da aka gano a wani daji a kusa da garin Malindi na gabar teku, sun hada da na yara kuma ‘yan sandan sun ce suna sa ran gano karin wasu.

Limamin cocin na Good News International, Paul Mackenzie, wanda ya musanta yin wani abu na ba daidai ba, yana hannu tun bayan da aka tsare shi mako guda da ya gabata.

Tun da farko an kama shi ne bayan da ‘yan sanda suka gano gawarwakin mutum hudu.

Hukumomin tsaro sun dukufa bincike ne bayan da allura ta tono garma kan wannan lamari, inda a tashin farko aka gano gawarwakin mutum hudu da suka rasu a sanadiyyar yunwa da ta hallaka su bi sa zargin umarnin da limamin cocin nasu ya ba su na kame bakinsu daga cin abincin don su mutu ta wannan hanya su samu haduwa da Almasihun.

A makon da ya gabata ne aka gano kaburburan da aka binne su a dajin Shakahola, inda a can ne aka ceto mutum 15 da ke da sauran numfashi.

Tun a wannan lokacin ‘yan sandan sun garzaya da mutanen asibiti a dalilin halin da suke ciki na kanjamewa saboda tsabagen azumin da suke yi da zai kai su ga mutuwa domin cimma wannan buri nasu na ganawa da Yesu, kamar yadda ake zargin jagoron ya bukace su da su yi.

Shi dai limamin cocin na Good News International, Paul Mackenzie, wanda ya musanta zargin da ake yi masa na dora mabiyan a wannan turba, ya ce bai yi wani abu da ya saba doka ba, sannan ya ce tun shekarar 2019 aka rufe majami’ar.

Yanzu dai jagoran yana ci gaba da zama a hannun hukuma ba beli har zuwa lokacin da za a gurfanar da shi a gaban alkali.

Kafar yada labaran gwamnatin kasar ta Kenya, KBC, wadda ta bayar da rahoton cewa zuwa yanzu an gano kaburbura 58, ta bayyana jagoron a matsayin shugaban wata kungiya ta tsafi.

Jaridar The Standard ta kasar ta Kenya ta ce, kwararru kan binciken gawa za su yi nazari domin gano ko lalle mutanen sun mutu ne a dalilin tsananin yunwa.

A ranar 15 ga watan Afirilu na wannan shekara ta 2023 ‘yan sanda suka damke Mista Mackenzie, bayan da suka gano gawarwakin mutum hudu da ake zargin sun mutu ne a dalilin kaurace wa abinci.

Victor Kaudo na cibiyar tabbatar da adalci ta garin na Malindi ya sheda wa tashar talabijin ta Citizen TV cewa, ‘’Lokacin da muka shigo wannan dajin muka iso wani wuri inda muka ga wani babban itacen gicciye mai tsawo, mun san cewa akwai mutane sama da biyar da aka binne a wurin."

Ana zargin limamin cocin da sanya wa wasu kauyuka uku sunaye Nazareth da Bethlehem da kuma Judea.

Sannan ya yi wa mabiyansa wankan tsarki a tafki kafin ya umarce su, su fara azumin, kamar yadda jaridar The Standard ta ruwaito.

Ita dai Kenya kasa ce da ke da mutane masu bin addini, kuma daman ko a baya ma an sha samun irin wannan abu inda ake yaudarar mutane a shigar da su coci-coci ko kungiyoyin matsafa masu hadari, wadanda ba a sa ido a kansu.