Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa jami'an difilomasiyyar Koriya ta Arewa ke sauya sheƙa zuwa Koriya ta Kudu?
- Marubuci, Yuna Ku
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Korean
- Lokacin karatu: Minti 3
Wani babban jami'in difilomasiyya a ofishin jakadancin Koriya ta Arewa ya koma wajen Koriya ta Kudu a watan Nuwamba, kamar yadda hukumar leƙen asiri ta Kudun ta tabbatar wa da BBC a ranar Talata.
Sauya sheƙar da jami'an difilomasiyyar Arewa ke yi zuwa Kudu kan ɗauki tsawon watanni kafin ta fito fili saboda sai an ba su horo kafin a amince da su a hukumance.
Kafofin yaɗa labaran Koriya ta Kudu sun ruwaito cewa mutumin shi ne mai ba da shawara a ɓangaren siyasa a ofishin jakadancin Koriya ta Arewa da ke Cuba. Sai dai hukumar tattara bayanan sirri ta Kudun NIS ba ta faɗa wa BBC haka ba.
Jaridar Chosun Ilbo ta ce ta samu tattaunawa da jami'in difilomasiyyar, wanda ta ce sunansa Ri Il Kyu mai shekara 52.
A cewar Ma'aikatar Haɗinkai, kusan jami'ai 10 daga Koriya ta Arewa, ciki har da na difilomasiyya da ma'aikata da ɗalibai, su ne suka koma wajen ta Kudu inda adadin ya zama mafi yawa tun daga 2017.
Ana kallon jami'an difilomasiyyar Koriya ta Arewa a matsayin manyan jami'ai sosai na gwamnatin ƙasar, dalilin da ya sa ke nan sauya sheƙarsu ke jan hankali game da gazawar gwamnatin ƙasar.
Ofisoshin jakadanci na rufewa
Duk da abubuwan da suka faru kwanan nan, an ga yadda Koriya ta Kudu ta rurrufe ofisoshin jakadancinta.
Zuwa watan Janairu, Arewa na da ofisoshi 44 na difilomasiyya a ƙasashen waje (39 manyan ofisoshi, biyu ƙanana, uku kuma ofishin wakilci), wanda 53 ne a 2022, in da aka rufe a ƙasashen Nepal, Spain, Angola, Uganda, Hong Kong and Libya.
Hukumomin Koriya ta Kudu sun alaƙanta hakan da takunkuman da ƙasashen suke saka wa Koriya ta Kudu.
Sai dai wasu masana na ganin hakan na faruwa ne da gangan, inda Arewa ke sauya salon zamantakewa da ƙasashen duniya.
"Ofisoshin da aka rufe an kafa su ne a shekarun 1970 da 1960 lokacin da Arewa da Kudu ke neman ƙuri'u a Majalisar Ɗinkin Duniya [MDD]," a cewar Nam Sung-wook, shugaban cibiyar Institute for National Unification and Convergence da ke Jami'ar Korea.
"Amma yanzu ba haka abin yake ba, Arewa na sauya alƙiblar ƙawancenta zuwa ƙasashen da ke adawa da Amurka, inda za su samu kuɗi da kuma kauce wa takunkuman MDD."
Mista Nam ya ce jami'an difilomasiyyar Arewa kan ɗauki nauyin rabin ayyukansu da kansu amma takunkuman MDD ya sa da kyar suke samun kuɗaɗen ƙasashen waje "wanda hakan ya jawo matsin lamba daga gwamnatin ƙasar da kuma sauya sheƙa zuwa Kudu".
Matsin tattalin arziki da jami'an difilomasiyyar Arewa ke sha ya fito fili daga bakin jami'an da ke sauya sheƙar zuwa Koriya ta Kudu.
Cikin wata hira da jaridar The Chosun Ilbo ta Koriya ta Kudu, Ri Il-gyu da ya sauya sheƙa ya bayyana ƙarara yadda ma'aikatan difilomasiyyar Arewa suka zama "mabarata".
Fargabar ladaftarwa
Yayin da ake fama da wannan ƙalubalen, nauyin da ke kan jami'an difilomasiyya ma na ƙaruwa.
Kwak Gil-sup, shugaban cibiyar One Korea Center wanda kuma tsohon mai nazari ne a hukumar NIS ta Koriya ta Kudu, ya ce 'yan difilomasiyyar na fuskantar ƙarin sa-ido da kuma ladaftarwa saboda tsarin “Kim Jong Un na manufar Koriya biyu".
"Yanzu jami'an na jin suna cikin barazana kuma suna fargabar abin da ka iya faruwa da iyalansu nan gaba," a cewarsa.
Kafuwar alaƙar difilomasiyya tsakanin Cuba da Koriya ta Kudu a farkon wannan shekarar - karon farko cikin shekara 65 - ka iya ƙara ta'azzara lamarin jami'an na Arewa da ke Cuba. Kafin yarjejeniyar, Cuba na tare da Arewa ne tsawon shekaru a matsayin ɗaya cikin mafiya daɗaɗɗun ƙawayenta.
Thae Yong-ho, mataimakin jakadan Arewa a Birtaniya da ya koma ɓangaren Kudu a 2016, ya faɗa a Facebook cewa yana da alaƙa ta kusa da Ri Il-gyu.
Mista Thae ya rubta: "Aikin [Ri] na ƙarshe shi ne daƙile alaƙar Cuba da Koriya ta Kudu. Ya yi ƙoƙarin aiwatar da umarnin gwamnatin Arewa, amma ya ce ba shi da wani zaɓi saboda girman alaƙar Cuba da Kudun."
Tasirin sauya sheƙa
Sauya sheƙar da jami'an difilomasiyyar Koriya ta Arewa ke yi, sun fara ne tun daga shekarun 1990, inda adadin ka iya zarta wanda aka sani saboda ƙarancin samun labaran.
Dr. Kwak na ganin mutanen da suka fara sauya sheƙa kamar Young-hwan (tsohon sakatare na farko a ofishin jakadancin Arewa na ƙasar Kongo, wanda ya gudu zuwa Kudu a 1991), sun yi tasiri sosai ga waɗanda suka biyo baya.
"Idan jami'in Arewa ne kai, da wuya a ce ba ka taɓa ji ba [labarin Thae]," in ji Dr Kwak, yana mai cewa: "Ya nuna cewa ko da ya sauya sheƙa zai iya cigaba da aiki a Kudu har ma a zaɓe shi ɗanmajalisa da kuma shiga majalisar ƙoli ta jam'iyya mai mulki."
A wajen jami'an difilomasiyyar Arewa da ke ƙasashen waje yanzu haka, sun fi samun damar sauya sheƙar fiye da sauran 'yan ƙasa.
Sai dai kuma, kamar saura, suna cigaba da fuskantar ƙalubale game da lafiyar iyalansu a gida Koriya ta Arewa.