'Yan wasan da Barca ta dauka da wadanda suka bar Camp Nou a bana

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta daura damarar taka rawar gani a kakar bana, wadda ta yi cefanen fitattun 'yan wasa don ganin kwalliya ta biya kudin sabulo.
Bayan 'yan kwallon da ta dauka ta kuma sayar da wasu da bayar da aro ga wasu kungiyoyin a kakar nan.
Mohammed Abdu ya hada bayanai kan 'yan wasan da Barcelona ta dauka a bana da wadanda suka bar kungiyar ko ta bayar da aronsu kawo yanzu.

Asalin hoton, Getty Images
Tun farko Dani Alves ne ya bayyana cewar zai bar Camp Nou a karshen kakar da aka kammala, bayan karo na biyu da ya taka leda a Camp Nou.
Ya kuma bar Barca bayan wasa 408 a kungiyar, shi ne na biyu a yawan yiwa kungiyar tamaula, bayan Lionel Messi.
Mai shekara 39 ya koma Camp Nou da taka leda a Nuwamba, shekara biyar bayan barin Barcelona zuwa Juventus.
A zaman da ya yi a Barca, Alves ya lashe La Liga shida da Champions League uku da Copa del Rey hudu daga kofi 23 da ya dauka a kungiyar.
Haka kuma a ranar 30 ga watan Yunin da ta wuce yarjejeniyar Adama Traore da Luuk de Jong ta kare a Camp Nou, bayan wasannin aro da suka buga.
Adama Traore ya je buga wasannin aro a Barcelona a ranar 29 ga watan Janairun 2022 daga Wolverhampton Wanderers, wanda ta gabatar da shi ranar 2 ga watan Fabrairu.
Ya kuma buga wasa 21 a kakar da ta wacu ta 2021/22.
Shi kuwa Luuk de Jong shi ne na karshe da Barcelona ta dauka aro a bara daga Sevilla a karkashin koci Ronald Koeman.
Lokacin Barcelona ta yi fama da kalubale da yawa a wasanninta.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Cikin kakar bana da kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai ta bude, Barcelona ta cimma yarjejeniyar daukar Franck Yannick Kessier, wanda kwantiraginsa ya kare a AC Milan a watan jiya.
Dan wasan ya sa hannu kan yarjejeniyar da za ta kare ranar 30 ga watan Yunin 2026.
Haka kuma Barcelona ta sa farashin yuro miliyan 500 ga duk kungiyar da ke son daukar dan wasan, idan yarjejeniyarsa ba ta kare ba a Camp Nou.
Ranar Laraba 6 ga watan Yuli, Barcelona ta gabatar da Franck Yannick Kessie a matakin dan wasanta.
An haifi Franck Kessie ranar 19 ga watan Disambar 1996 a garin Ouragahio da ke Ivory Coast.
Mai taka leda daga tsakiya ko tsaron baya daga tsakiya ya fara tamaula a Stella Club d'Adjame ta Ivory Coast daga baya ya koma Atalanta a 2014.
Bayan da ya taka rawar gani a kakar 2016/17 a Atalanta, daga nan ne AC Milan ta yi zawarcin dan kwallo.
Dan wasan ya koma Milan buga wasannin aro a 2017 daga nan ta saye shi a 2019 kan yuro miliyan 33.
Kaka biyar da Kessie ya yi a Milan ya kara samun gogewa, ya kuma ci kwallaye, ya kuma bayar an zura a raga.
Dan wasan tawagar Ivory Coast ya taimakawa Milan ta dauki Serie A a kakar da aka Karkare, kofin farko da ta dauka tun bayan kaka 11.

Asalin hoton, Barcelona
Daga nan Barcelona ta sanar da daukar Andreas Christensen daga Chelsea, bayan da kwantiraginsa ya kare a Stamford Bridge a karshen watan Yuni.
Christensen ya amince da kunshin yarjejeniyar kaka hudu da dora farashin yuro miliyan 500 ga duk kungiyar da ke son daukarsa, idan wa'adinsa bai kare ba a Camp Nou.
Christensen dan kwallon tawagar Denmark ya zama na biyu da Barca ta dauka a bana, bayan Franck Kessie da ta sanar da daukarsa ranar Litinin daga AC Milan.
Tun farko Barcelona ta sanar da cimma yarjejeniyar daukar Franck Yannick Kessier, wanda kwantiraginsa ya kare a AC Milan a watan jiya.

Asalin hoton, Getty Images
A kakar nan Barcelona ta cimma yarjeniyar bayar da aron Francis Trincao da Spoting ta Potugal.
Dan kwallon zai buga wasannin aro zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2023 da yarjejeniyar sayar da shi idan ya taka rawar gani.
Trincao ya koma Barca daga SC Braga a kakar 2020 ya kuma fara buga mata tamaula a wasa da Ferencvaros a Champions League.
Ya yi mata wasa 42 a kakar farko da cin kwallo uku da bayar da biyu aka zura a raga a gasar Copa del Rey.
Dan kwallon ya buga wasannin aro a bara a Wolves mai buga gasar Premier League.

Asalin hoton, Getty Images
Daga nan Barcelona ta sayi dan wasan gaba na Brazil Raphinha daga Leeds United a kan farashin da ya kai fam miliyan 55.
An gabatar da dan wasan, mai shekara 25, ga magoya bayan kungiya a filin wasan Catalan ranar Juma'a.
Raphinha, wanda ya koma Leeds daga Rennes a kan fam miliyan 17 a 2020, ya murza leda sau 65 a Gasar Firimiya a kungiyar ta Yorkshire club, inda ya ci kwallo 17 sannan ya taimaka aka ci 12.

Asalin hoton, Getty Images
Daga nan kuma kungiyar FC Barcelona ta sayar da Moussa Wagu ga HNK Gorica ta Crotia.
Cikin kunshin yarjejeniyar Barcelona za ta samu wani kaso a duk lokacin da kungiyar ta Croatia za ta sayar da dan kwallon.
Moussa Wague ya koma Barcelona a 2018, ya kuma fara yi mata wasa ranar 13 ga watan Afirilun 2019 a fafatawa da Huesca.

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasa na hudu da Barcelona ta kammala daukar a bana shi ne dan kwallon tawagar Poland, Robert Lewandowski daga Bayern Munich kan yarjejeniyar kaka hudu kan fam miliyan 42.6.
Barcelona ta gindaya fam miliyan 429.9 ga duk wadda za ta dauke Lewandowski idan yarjejeniyarsa bai kare ba a Camp Nou.
Dan wasan ya koma Bayern Munich da taka leda a 2014 a lokacin da yarjejeniyarsa ta kare a Borussia Dortmund.
Ya ci kwallo 50 a wasa 46 a kakar da ta wuce, ya kuma taimakawa Bayern ta dauki Bundesliga na 10 a jere a kakar da aka kammala.
Lewandowski ya zura kwallo 344 a raga a wasa 374 a Bayern, shi ne na biyu a tarihin cin kwallaye a kungiyar bayan Gerd Muller.
Dan wasan ya lashe Bundesliga a dukkan kaka takwas da ya yi a kungiyar, ya kuma dauki Champions League a 2019-20.
Lewandowski shi ne na hudu da Barcelona ta dauka a bana, bayan dan kwallon Brazil, Raphinha daga Leeds United da Franck Kessie da AC Milan da Andreas Christensen daga Chelsea.
Haka kuma Bayern ta sayi dan wasan tawagar Netherlands, Matthijs de Ligh daga Juventus kan yarjejeniyar kaka biyar kan fam miliyan 65.6,










