Raphinha ya fara El Clasico da cin Real Madrid kwallo

Raphinha

Asalin hoton, Getty Images

Raphinha, sabon dan kwallon da Barcelona ta dauka a bana, shi ne ya ci Real Madrid a wasan sada zumunta a Las Vegas din Amurka.

Karawar ta El Clasico, ita ce ta farko da kungiyoyin Sifaniya suka fara a bana tun kan fara kakar tamaula da za a fara a cikin watan Agusta.

Dan kwallon tawagar Brazil, ya koma kungiyar Camp Nou daga Leeds United kan kwantiragin da ta kai fam miliyan 55 a farkon watan nan.

Kawo yanzu dan wasan ya ci wa Barcelona kwallo biyu kenan a wasannin atisayen da take yi a Amurka.

Raphinha ya zura kwallo a ragar Real Madrid a minti na 27 a wasan farko da Robert Lewandowski ya yi wa sabuwar kungiyarsa Barcelona tamaula.

Real Madrid, wadda ta yi karawar ba tare da Karim Benzema ba, ba ta buga kwallo ya nufi raga ba ko sau daya a fafatawar.