Turai ta yi watsi da kuria'r raba gardamar shiga Rasha a Ukraine

Manyan shugabanni daga kungiyar tsaro ta Tarayyar Turai,OSCE sun yi Allah-wadarai da shirin gudanar da kuria’r raba gardama da za a yi a yankunan da Ukraine da Rasha ta mamaye.

A wata sanarwa ta hadin guiwa daga ofishin shugaban na OSCE, ministan harkokin wajen Poland Zbigniew Rau, da Babbar Sakatariya Helga Maria Schmid da kuma sauran jami’an diflomsaiyya suka yi sukan.

Jami’an da ke samun goyon bayan Rasha a yankunan Ukrine da Rasha ke iko da su sun ce suna son yin kuriar raba gardama kan shiga Rasha, wadda za su farad aga wannan makon.

Sanarwar wadda ta fito daga hukumar tsaron ta Tarayyar Turai ta ce kuri’ar raba gardamar da aka shirya yi ta saba wa doka.

Sanarwar ta ce hukumomin da suke da halarci na doka ne kawai za su iya shirya wannan kuri’a bisa tanadin dokokin kasa.

Hukumar ta ce yayin da yaki ke ci gaba da gudana duk wata kuria’r raba gardama da wadanda suka mamaye yankunan Ukraine za su yi, abu da ya sab awa dokokin duniya.

Ta ce kuri’ar za ta kasance ba ta da halarcin doka.

Jami’an da ke bin ra’ayin Rasha a Luhansk da Donetsk da Kherson da kuma Zaporizhzhia sun sanar da cewa za a fara kda kuria’r ne daga Juma’ar nan, wanda hakan zai ba wa Rasha damar mamaye yankunan na gabashi da kuma kudanci.

A ‘yan watannin nan mamayen da Rashar ke yi a Ukraine ya dakata inda dakarun Ukraine din suka yi nasarar sake kwato wasu yankuna da dama a yankin arewa maso gabas.

Rasha ta mamaye Crimea a 2014, bayan irin wannan kuri’ar wadda ta gamu da suka daga kasashe da hukumomin duniya.

An sa ran Shugaba Vladimir Putin na Rasha zai yi jawabi ga kasar ranar Talata amma sai wasu majiyoyi na fadar gwamnatin kasar suka nuna cewa ya dage yin jawabin ba tare da bayar da wani dalili ba.

Ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ya bayyana cewa kuri’ar raba gardama ta jeka-na-yi-ka ba za ta yi wani tasiri na sauya komai ba.

Kasashe da hukumomin duniya ba su taba amincewa da mamayar Crimea da Rsaha ta yi ba.

Amma kuma abu ne da ake ganin Rashar za ta sake yin irinsa a wasu sassan da ta mamaye, inda za ta nuna halarcin hakan.

Mamaye karin yankunan Ukraine zai sa gwamnatin Rasha ta yi ikirarin cewa ana kai mata hari da makaman Nato.

A ranar 24 ga watan fabrairu ne Rasha ta kaddamr da mamayar ta Ukraine.