Hukumar nukiliya ta duniya na fargaba kan tashar Zaporizhzhia ta Ukraine

Hukumar nukiliya ta duniya ta ce tashar nukuliya ta Zaporizhzhia da ke kasar Ukraine wadda ke karkashin ikon Rasha ta sake gamuwa da matsalar katsewar babban layin da ke ba ta wutar lantarki na karshe da ya rage.

A wata sanarwa hukumar ta IAEA ta ce a yanzu tashar ta dogara ne ga layin ko-ta-kwana wajen samun lantarkin da ke tafiyar da ita.

Wannan sanarwa da hukumar kula da nukiliyar ta duniya ta fitar game da wannan tasha da ke zaman mafi girma a Turai, na nuna cewa har yanzu halin da ake ciki a tashar wadda Rasha ta kame, abu ne mai hadarin gaske.

Domin samar da wutar lantarki ga tashar ba tare da wata fargabar katsewa ba abu nem ai muhimmancin gaske ba kawai domin samar da lantarkin da ita kanta tashar take yi wa.

A’a hatta zaman lafiyar ita kanta tashar ya dogara ga samun wutar, domin da lantarkin ne na’urorin da ke sanyaya tashar ke aiki, wanda kenan rashin wutar zai iya kasancewa babbar matsala.

Dan sauki-saukin abin dai shi ne kasancewar yanzu akwai jami’an hukumar nukiliyar ta duniya masu sa ido a tashar.

Abin da shugaban hukumar, Rafael Grossi, ya kira abu mai muhimmanci da ya sauya al’amura domin hakan ya ba su damar sanin halin da tashar ke ciki tare da yin duk wani abu domin daidaita ta.

Amma duk da haka Mista Grossi wanda bai dade da barin tashar ba shi kansa yana cike da damuwa kan wannan yanayi.

Ukraine ta dora alhakin katsewar layin lanatrakin na baya-bayan nan a kan makaman da Rasha ke harbawa.

Yayin da ita kuwa Rasha take zargin cewa a ranar Juma’a ta kawar da wani yunkuri na sojojin Ukraine na far ma tashar.

Tun farkon fara rikicin kasashen ne dai sauran layukan samar da lantarki ga tashar guda uku suka katse.

Tashar ta Zaporizhzhia, wadda ke kudancin Ukraine ta fada hannun Rasha ne jim kadan da kasar ta kaddamar da mamayen makwabciyar tata a watan Fabrairu.

Ma’aikatan tashar ‘yan Ukraine wadanda ke ci gaba da tafiyar da ayyukanta sun ce Rasha na amfani da ita a matsayin wani sansanin soji, kuma ma’aikata na aiki ne ala tilas kamar an ritsa su da bindiga.