Mece ce ƙirƙirarriyar basira ta AI da hatsarinta?

Fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta Artificial Intelligence (AI) tana habaka cikin sauri, kuma tana canza yadda ake gudanar da abubuwa da dama na rayuwar zamani.

Duk da haka, wasu masana na gargaɗin cewa za a iya amfani da shi don dalilai na keta, kuma yana iya yin barazana ga ayyuka.

Menene AI kuma ya yake aiki?

AI yana bai wa kwamfuta damar yin tunani, aiki, da ba da amsar tambayoyi kusan kamar yadda Dan Adam zai yi.

Ana iya sanya bayanai a cikin kwamfutoci da yawa da kuma horar da su don gano yadda tsarin abubuwa su ke, ta hanyar yin hasashe, da warware matsaloli, har ma su iya nazari daga nasu kura-kuran.

Fasahar ta dogara ga wasu bayanai da ake kira, algorithms - wadanda wasu jerin dokoki ne da dole ne a bi su a daidai yadda aka tsara don a sami kammala aiki.

Fasahar ita ce tushen mataimakan kama-da-wane masu sarrafa murya kamar su Siri da Alexa.

Yana bai wa Spotify, da YouTube da BBC iPlayer daman ba da shawaran abin da za ku so ku saurara a gaba, kuma yana taimaka wa Facebook da Twitter wurin ba da shawarar abin da kafofin sada zumunta za su nuna wa masu amfani da su.

Fasahar na bai wa Amazon damar nazarin halayen saye-saye na abokan ciniki don ba da shawarar irin sayayyar da za a iya yi a gaba - kuma kamfanin yana amfani da fasahar wurin dakile bayanai na karya.

Menene ChatGPT da My AI na Snapchat?

Manhajoji biyu da suka samu karbuwa kuma suka yi suna cikin watannin baya- bayan nan su ne ChatGPT da My AI na Snapchat .

Wadannan su ne abin da ake kira "generative" AI.

Suna amfani da tsarin da ke bincika dimbin bayanai don samar da sabbin bayanai na asali wanda za a ga kamar Dan Adam ne ya kirkire su.

Fasahar na amfani da tsarin kwamfuta da aka sani da chatbot, wanda ke "magana" da 'yan adam masu amfani da su.

Mahajojin na iya amsa tambayoyi, da ba da labari, kuma su na iya rubutu da yaren kwanfuta.

Amma mahajojin wani lokaci kan ba da amsoshi da ba daidai suke ba ga masu amfani da su, kuma suna iya amfani da son zuciya da aka saka cikin asalin yadda aka kera su, kamar nuna bambanci jinsi ko wariyar launin fata.

Me yasa wasu ke tsoro, kuma mene ne hadarin ta?

Da yake ka'idojin da ke tafiyar da yadda ake amfani da fasahar AI ba su da yawa a halin yanzu , masana sun yi gargaɗin cewa saurin habakarsa na iya zama hadari.

Wasu ma sun ce ya kamata a dakatar da bincike kan fasahar ta AI.

A watan Mayu, Geoffrey Hinton, wanda aka fi sani da kasancewa daya daga cikin ubangidan fasahar, ya yi murabus daga aikinsa a Google, yana mai gargadin cewa nan ba da jimawa ba AI na iya samun basira fiye da mutane.

Daga baya a wannan watan, Cibiyar Tsaro ta AI ta Amurka ta buga wata sanarwa da ke samun goyan bayan manyan kwararrun masana fasaha.

Suna jayayyar cewa za a iya amfani da AI don samar da bayanan da ba daidai ba wanda zai iya lalata al'umma.

A cikin mafi munin yanayi, sun ce kwamfutoci na iya zama masu hankali har su karbe komai, wanda zai haifar da shafewar bil'adama baki daya.

Sai dai shugabar bangaren fasaha ta tarayyar Turai Margrethe Vestager ta shaida wa BBC cewa yiwuwar AI na kara nuna son kai ko wariya shi ne abu mafi tashin hankali.

Musamman ta damu da rawar da AI za ta iya takawa wajen yanke shawarwarin da suka shafi rayuwar mutane kamar neman bashi, ta kara da cewa akwai "haɗari" da za a iya amfani da AI wajen yin tasiri a zabe.

Wasu mutane, ciki har da majagaba na fasaha Martha Lane Fox, sun ce bai kamata mu sami mummunan tashin hankli game da fasahar AI ba.

Misis Vestager ta yi kiran kiran samun yin tattaunawa mai ma'ana game da abubuwan da fasahar za ta iya yi da wanda ba za ta iya ba.

Wadanne dokoki ne ake da su a halin yanzu game da fasahar AI?

Gwamnatocin kasashe da dama na kokarin samu yadda za a gindaya ka'idojin amfani da fasahar AI.

Mambobin Majalisar Tarayyar Turai sun kada kuri'ar amincewa da kudurin dokar da za ta kiyaye yadda ake amfani da fasahar, wacce za ta kafa tsauraran tsarin shari'a kan fasahar AI, wanda za a bukaci kamfanoni su yi amfani da ita.

Margrethe Vestager ta ce ana bukatar "hanyoyin tsaro" don magance manyan hadarin da za a iya fuskanta daga fasahar AI.

Dokar - wacce ake sa ran za ta fara aiki a cikin 2025 - ta rarraba mahajoji cikin matakan hatsarin da masu amfani da su za su iya tunkara.

Manhajojin da ake ganin sun fi hadari ga ma su amfani da su sune kaman wadda ke iya tantance cancantar mutum ya samu bashin banki da kuma cancantar iya samun tallafin gida.

Su ne za a fi dora wa tsauraran matakai.

Wadannan dokoki ba za su yi aiki a Birtaniya ba, inda gwamnati ta shirya na ta tsare-tsaren kan makomar AI a cikin watan Maris.

Ta yanke hukuncin rashin kafa wani kwararren mai kula da AI, kuma tare da cewa a maimakon haka hukumomin da ake da su a kasa a halin yanzu ne za su cigaba da daukan nauyin sa ido.

Amma Ms Vestager ta ce ka'idojin tafiyar da yadda ake amfani da fasahar AI na bukatar su zama "al'amari na duniya", kuma tana son ta ga an samu yarjejeniya tsakanin kasashe masu ra'ayi iri daya.

'Yan majalisar dokokin Amurka ma sun nuna damuwa game da ko ka'idojin sa kai da ake da su yanzu sun kai ga aiki.

Kasar China kuma na da niyyar sanya kamfanoni dole su sanar da masu amfani da na'urorinsu duk lokacin da ake amfani da algorithm na AI.

Wadanne ayyuka ne ke fuskantar haɗari saboda AI?

Fasahar AI na iya kawo muhimmin sauyi a yanayin aiki, amma wannan yana haifar da tambayoyi game da irin ayyukan da zai a iya rasawa sakamakon fasahar.

Wani rahoto na kwanan nan na bankin zuba jari na Goldman Sachs ya ba da shawarar cewa AI na iya maye gurbin kwatankwacin ayyukan yi miliyan 300 a duk fadin duniya, yayin da wasu ayyuka suka zama masu sarrafa kansu.

Wannan ya yi daidai da kashi daya bisa hudu na duk ayyukan da dan adam ke yi a yanzu a Amurka da Turai

Rahoton ya nuna wasu masana'antu da ayyukan da lamarin zai iya shafa, ciki har da ayyukan gudanarwa, da aikin shari'a, da kuma gine-gine.

Amma kuma ya gano fa'idoji masu yawa ga sassa da dama, kuma ya yi hasashen cewa fasahar AI na iya haifar da habaka da zai kai 7% a arzikin da ake samu daga abubuwan da aka sarrafa a cikin gida, wato GDP na duniya.

Tuni dai wasu bangarori a fannin likitanci da kimiyya suka fara cin gajiyar fasahar AI, inda likitoci ke amfani da fasahar wajen gano cutar kansar mama, kuma masana kimiyya suna amfani da shi wajen samar da sabbin magungunan rigakafi.