Tarihin mutumin da zai zama sabon shugaban al-Qaeda Sayf al-Adl

Asalin hoton, Getty Images
Sayf al-Adl: Me muka sani game da wanda ake kyautata zaton zai zama sabon shugaban al-Qaeda?
Bayan mutuwar Ayman al-Zawahiri a wani harin sama da Amurka ta kai, kungiyar al-Qaeda na duba yiwuwar nada mataimakin al-Zawahiri domin zama sabon shugabanta.
An kashe al-Zawahiri ne a Kabul babban birnin Afghanistan, kuma yanzu hankula suka karkata kan wanda zai ja ragamar kungiyar mai da'awar Musulunci.
Ana kyautata zaton cewa za a nada Sayf al-Adl, wanda haifaffen dan kasar Masar ne, a matsayin sabon shugaban kungiyar.
Shi ne kadai ya rage cikin manyan 'yan al-Qaeda guda biyar da aka taba bai wa mataimaka ga al-Zawahiri, wanda kuma zai gaje shi.
Amma ana fargabar cewa akwai matsala.
Al-Adl na rayuwa ne cikin kasar Iran da aka sanya wa takunkumi - kasar kuma da al-Qaeda ke ganin a matsayin babbar abokiyar gabarta.
Shahararren dan jihadi
Al-Adl, babban na hannun daman Osama Bin Laden ne wanda kuma yake cikin wadanda suka kafa kungiyar - da ya shahara wajen da'awar jihadi
Mutumi ne kuma da kasar Amurka nema ruwa jallo, inda yake kan gaba a wadanda hukumar binciken cikin gida ta Amurka FBI ke nema a matsayin dan ta'adda. Ta kuma saka tukwuicin $10m ga duk wanda ya bayar da labarin inda yake.
Ana zarginsa da hannu a harin bama-bamai da aka kai ofisoshin jakadancin Amurka a Tanzania da Kenya a watan Augustan 1998, da ya hallaka sama da mutum 220.
Amma an ruwaito cewa bai goyi bayan hare-haren ranar 9 ga watan Satumba ba da aka kai biranen New York da Washington.
A wani kundi da aka fitar a Fabrairun 2021, masu bincike daga cibiyar sojojin Amurka da aka fi sani da West Point, sun yi zargin cewa al-Adl da wasu manyan 'yan kungiyar ta al-Qaeda sun shiga fargaba cewa manyan hare-hare kan Amurka za su fusata Amurkan wajen mayar da mummunan martani wanda ya hada da mamaye Afghanistan, mafakar mambobin kungiyar.

Asalin hoton, Getty Images
A baya, Al-Adl ya yi wasu rubuce-rubuce kan abubuwa da dama wadanda suka hada da kan 'tsaro da binciken sirri'', yaki da kuma sauye-sauye.
Shekarun farko
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Babu kwararan bayanai kan rayuwar wanda zai zama sabon shugaban al-Qaedan ya yi kafin ya shiga kungiyar.
A cewar hukumar FBI, an haifi al-Adl ne ranar 11 ga watan Afrilun 1963 ko kuma shekaru uku kafin haka.
Duk da matsayinsa a cikin kungiyar ta al-Qaeda, ba a san hakikanin rayuwar da yake yi ba sannan da wuya yake fitowa a sakonnin farfaganda da kungiyar ke yi.
Ana kuma nuna shakku kan asalinsa; sunansa Sayf al-Adl (da ke nufin makamin adalci).
Masu bincike a West Point sun yi zargin cewa ana yawan kuskure wajen bayyana al-Adl a matsayin Mohammed Ibrahim Makkawi, wani tsohon Kanal na dakaru na musamman na kasar Masar.
An fi saninsa da jajircewa da kuma fada kan mamayar Afghanistan da tarayyar Sobiyet ta yi a shekarun 1980 tare da Bin Laden, a lokacin ne kuma aka kafa kungiyar al-Qaeda.
Daga baya Al-adl ya tashi zuwa Somaliya, inda ya taimaka wajen horar da mayaka da ke yaki da Amurka kan taimakon ta a yakin basasar Somaliya.
Kamfe din ya samu karbuwa, inda aka wani makamin roka ya harbo jiragen Amurka masu saukar ungulu biyu MH-60, wanda kuma ya zama abin da aka shirya fim mai suna Black Hawk Down aka yi a masana'antar shirya fina-finai ta Amurka Hollywood a 2001
An yi imanin cewa wani mamban dakarun al-Adl dan kasar Tunisia, shi ya harba daya daga cikin rokokin .
Al-aAdl ya dawo Afghanistan a tsakiyan shekarun 1990 daidai lokacin da Taliban ke kokarin karfafaf ikon su a kasar.
Ya sake barin kasar jim kadan bayan mamayar Amurka a 2001 wanda ya janyo hadewar mambobin al-Qaeda a Iran ta hanyar samun gidajen buya.
An yi imanin cewa hukumomin sun kama shi a 2003 sannan aka ruwaito cewa an sake shi tare da wasu mambobin al-Qaeda da dama a wani sulhu ta fursunoni shekaru 12 baya.
Duk da cewa an tsare shi na tsawon lokaci, al-Adl ya zama mai karfin fada aji a kungiyar ta Al-Qaeda sannan ya taimaka wajen assasa al-Zawahiri a kan matsayinsa na shugaban al-Qaeda bayan mutuwar Osama Bin Laden a wani hari da sojojin Amurka na musamman suka kai Pakistan a 2011
Sai dai, nada shi sabon shugaban kungiyar zai zama da wahala: a cewar wani masani kan aikata muggan laifuka a Amurka, Collins P. Clarke, inda ya yi zargin cewa al-Adl na ci gaba da zama a Iran cikin kamen zama a gida.
Baya ga tunanin cewa al-Adl zai iya jagorantar kungiyar mai da’awar jihadi a duniya da ke rayuwa cikin kasar da aka sanyawa takunkumai ta ‘yan Shia, akwai kuma batun tsaro.
An kashe wani babban kwamandan kungiyar ta al-Qaeda, Abu Muhammad al-Masri, a wani harin sirri da ake zargin kwamandojin Isra’ila da kai wa a Tehran a 2020.
Idan ba al-Adl, to waye?
An bayar da jerin sunayen wasu mambobin kungiyar kamar yadda aka yi na Zawahiri a tsawon shekaru.
Zai iya tabbata cewa al-Qaeda za ta dauko sabon shugaba a daya daga cikin kungiyoyin da take alaka da su kamar al-Shabab ta Somaliya da AQAP a Yemen ko kuma JNIM da ke iko a Mali.
Yayin da hakan zai zama karon farko a tarihi, amma ba zai zo da mamaki ba ga kungiyar da ke samun koma baya a karkashin Zawahiri.
A shekarar 2013, an ruwaito cewa Zawahiri ya zabi shugaban kungiyar AQIM, Nasir al-Wuhayshi a matsayin mataimaki.
Wannan ka iya nuna cewa shugabannin kungiyoyin jihadi na shiya za neman mukamai a al-Qaeda – amma ba al-Wuhayshi ba, inda Amurka ta hallaka shi a wani hari ta sama a 2015.
Ko ma waye aka zaba domin gadar Zawahiri, zai fuskanci matsaloli na boye yadda yake gudanar da rayuwarsa saboda fargabar kai masa hari da Amurka za ta yi.











