Yadda ya kamata ku wanke haƙoranku

Lokacin karatu: Minti 7

Wanke haƙora da kyau yana taimakawa wajen rage hatsarin kamuwa da manyan cutuka, da kuma inganta lafiyar haƙora da dasashi. Amma mafi yawa ba mu iya wanke haƙora ba, ko kuma muna yin shi yadda bai kamata ba.

Ga yadda ƙa'idojin wanke haƙora suke, kamar yadda ƙwararru suka bayyana.

Gashi dai abu ne da muka daɗe muna yi tun muna ƴan yara, amma har yanzu da dama bamu iya yin shi yadda ya kamata.

Wani bincike da aka yi a Sweden ya gano cewa mutum ɗaya ne kacal daga cikin kowanne 10, ya iya wanke haƙora da kyau. Wani kamfanin Inshoran lafiya na Birtaniya ya gano cewa daga cikin mutane 2,000 da aka y nazari a kansu, aƙalla rabinsu ba su iya wanke haƙora da kyau ba.

"Akwai yiyuwar duk mutumin da bai taɓa samun bayani ko shawara kai tsaye daga likitan haƙori ba, ba ya wanke haƙoransa da kyau,'' in ji farfesa Josefine Hirschfeld, wata ƙwararrar likitar haƙori a jami'ar Birmingham ta Birtaniya. Ta ƙara da cewa "Daga abubuwan da na ganewa idona, kusan mafi yawan mutanen kowacce ƙasa sun faɗa cikin wannan rukuni."

Wannan ba abin mamaki bane dan aka yi la'akari da ɗimbin bayanan da ake yaɗawa a game da yadda ake wanke haƙora. Wani bincike da aka yi ya gano aƙalla irin waɗannan bayanai har 66, wasunsu masu karo da juna.

"Ina ganin wannan wani abu ne mai rikitarwa ga jama'a,'' in ji Nigel Carter, shugaban gidauniyar kula da lafiyar haƙori ta Birtaniya. Ga kuma yawan sinadaran wanke baki da ake ƙara ƙirƙira a kullum, wani lamari da ke ƙara girman wannan matsala.

Shin menene bamu yi da kyau wajen wanke haƙora kuma ta yaya za mu gyara domin tabbatar da lafiyar haƙoranmu?

Wace hanya ta fi dacewa a bi wajen wanke haƙora?

"Mutane da yawa sun gane cewa abin da ya kamata su yi shi ne cire sauran abinci da ke maƙalewa a jikin haƙora,'' in ji Hirschfeld. "Wannan na da muhimmanci sosai saboda yana nufin an cire ƙwayoyin cutar da ke jikin haƙorin."

Waɗannan ƙwayoyin cuta suna taruwa a cikin bakin kowanne mutum kuma su haɗu da sauran ƙananan halittu , inda suke yin illa ga haƙori da dasashi,'' in ji Hirschfeld. "Idan suka taru a waje suna da wahalar fitarwa, asali ma sai an bi a hankali kafin fitar da su.''

Wajen da ya fi dacewa a duba domin fitar da waɗannan ƙwayoyin cuta, dasashi ne, musamman a daidai mahaɗar sa da haƙori. A nan ne ƙwayoyin cutar ke taruwa da kuma janyo ciwon haƙori da dasashi.

Hirschfeld ya ƙara da cewa ''Ka yi tunanin wanke dasashin ka da 'brush' a madadin wanke haƙoranka. Idan ka yi haka kai tsaye zai zama ka wanke haƙoran naka''

Wace hanya ta fi dacewa a wanke baki kenan??

Zagaye

Salon 'Bass technique' na nufin mutum ya riƙa wanke haƙoransa ta hanyar riƙa gurza burushi sama da ƙasa. Wato a ɗora burushin jikin haƙora sannan a riƙa goga shi ta hanyar turawa sama da kuma dawo da shi ƙasa da ci gaba da yin hakan. Ana kuma murzawa a riƙa zagaya burushin daga sama har ƙasa, har zuwa kan dasashi.

Shara

Wannan salon ya yi kama da na farkon, amma ya banbanta saboda a nan ana jan burushin ne kamar yadda ake shara da tsintsiya kuma ana nesanta shi da dasashi.

Na gwada wannan salo, amma na lura cewa ina sanya ƙarfi fiye da yadda ya kamata.

Wanke haƙora da ƙarfi sosai, musamman da burushi mai ƙarfi yana bayar da kafar da ƙwayoyin cuta ke shiga da samun wajen zama da kuma fara cin haƙori da ma dasashi.

Bincike ya nuna cewa mutanen da ke amfani da burushin hannu wajen wanke haƙaransu suna amfani da ƙarfin da ya zarce ƙaida idan aka kwatanta su da masu amfani da na'urar wanke baki mai sarrafa kanta.

Sama-sama

Na gwada salon Fones techniques na ƴan kwanaki, kuma salo ne da aka tanada saboda ƙananan yara da kuma mutanen da dasashinsu ba ya da ƙarfi sosai. A wannan salo ana nesanta burushin da haƙora...watau dai ba a dannashi a jikin haƙora ko dasashi, yayin da ake murza burushin ta hanyar zagaye tsakanin haƙora.

Tsawon wane lokaci ya kamata?

Wanke haƙora da burushi na tsawon minti biyu kai tsaye, kuma sau biyu a rana ya wadatar, kamar yadda ƙungyar likitocin haƙora ta Amurka da ta India da Australia da kuma wasu da dama suka tabbatar.

Matsalar itace mafi yawanmu ba mu iya tantance ko munyi minti biyu muna wanke bakin mu. Kashi 25 bisa ɗari na mutane ne kawai ke iya tantance ko sun cika minti biyu suna wanke haƙorin su, kuma a bisa tanadin da ƙwararu suka gindaya.

Saukin dai shi ne akwai hanyoyin magance wannan matsala da suka haɗa da amfani da wata manhaja wajen tantace lokacin da mutum ya ɗauka yana wanke haƙora, ko amfani da wayar salula ko kuma na'urar wanke baki ta zamani wadda ke da agogo a jikinta.

''Abu mafi muhimmanci shi ne a tabbatar an wanke kowanne sashi da ɓangare na haƙori, da lungu da saƙo, wanda kuma idan har za a yi to babu shakka sai an zarce minti biyu.'' in ji Hirschfield

"Tsawon lokacin da ake ɗauka wajen wanke haƙora ya danganta ne ga yanayin mutum da kuma yadda yake ganin akwai buƙatar ɗaukar lokaci wajen wanke haƙoran su fita tas''

Sau nawa ake wanke haƙora?

Shawarar da aka bayar ga mutane a Amurka da Birtaniya da kuma Australia ita ce ka kiyaye tsawon lokacin da ka saba yi kana wanke haƙora, kuma ka yi hakan aƙalla sau biyu a kowacce rana.

A India kuma ƙwararru sun bayar da shawarar wanke haƙori sau uku a rana, ciki harda wanda za a yi bayan cin abincin rana. Amma ga mutanen da basu da wata sananniyar matsalar cutuka a cikin baki ko haƙorin su, wanke haƙori sau biyu ya wadatar.

Kafin cin abinci ake wanke haƙora ko bayan an ci?

Daga masu samar da man wanke haƙora har zuwa ƙwararru a fannin kula da lafiyar haƙori duk suna bayar da shawarar cewa kamata ya yi mutum ya fara wanke haƙoransa kafin karin kumallo. Mafi yawa sun yarda cewa hakan ya ce fa'ida a kan bari sai bayan mutum ya ci abinci. Amma har yanzu wannan wani batu ne da ake ci gaba da muhawara a kai.

Amma za ka gane zaɓin da ya fi dacewa da kai ne idan ka yi la'akari da irin abincin da za ka ci, da kuma lokacin da za ka ci abincin.

Wani abin lura dai shi ne idan bayan cin abinci ne mutum zai wanke haƙoransa to ana buƙatar ya bayar da lokaci kafin wanke haƙoran. Kungiyar likitoci haƙora ta Amurka ta ce ya kamata a bayar da lokaci, aƙalla minti 60 bayan cin abinci kafin a wanke haƙora saboda akwai sinadarin abinci da ke maƙalewa a haƙori, wanda kuma idan ya haɗu da man wanke haƙorin zai iya janyo wata matsalar ta daban.

Wani abu mai muhimmanci shi ne wanke haƙora da dare, kafin mutum ya kwanta bacci. Ƙwararru sun ce ya fi dacewa ya zamo mutum ya wanke bakinsa kafin ya kwanta bacci. Kuma daga wannan lokacin miyon baƙinsa zai ci gaba da zama sinadarin da zai bai wa bakin kariya har zuwa safiya.

Wane irin burushi ya kamata a yi amfani da shi?

Matsakaicin burushi n ya fi dacewa da mutanen da shekarun su suka fara ja, ko kuma wanda ya girma. Sannan kuma burushi mai ƙaramin mai ya fi kyau saboda zai iya shiga lungu da saƙo. Haka kuma ''Ya kamata a kiyaye domin tabbatar da cewa ana canza burushi da zarar ya fara nuna alamun daɗewa, kodai yana wargajewa ko kuma ya fara yin zafi a baki,'' in ji Hirschfeld.

Asuwaki da ake amfani da shi a sassan Afirka da Gabas ta Tsakiya da kuma kudancin Asia suna da inganci sosai, amma suna da hatsari idan suka goge dasashin mutum, musamman ga ƴan koyo.

Wani burushi mai inganci kuma shi ne burushin laturoni, wanda ke wanke haƙora sosai da kuma cire abubuwan da suka maƙale a jikin haƙora, amma yana da tsada.

Wane man wanke haƙora ne ya fi dacewa?

Daga cikin jerin sinadaran da aka yi man wanke baki dasu, waɗanda aka rubuta a bayan kwalin man, akwai wanda ya kamata mutum ya duba domin tabbatar da cewa akwai shi a ciki. Shi ne sinadarin Fluoride.

Sinadarin Fluoride yana taimakawa sosai wajen bayar da kariya ga haƙora, musamman kariya daga sauran sinadarai da ƙwayoyin halitta da ke shiga cikin haƙoran da haifar da illa gare su.

Sai dai akwai bukatar yin hankali wajen amfani da wasu man wanke haƙori da ake iƙirarin suna ƙara lafiya da ingancin haƙora da kuma yaƙar ƙwayoyin halittu da ke rayuwa a cikin baki. Babu tabbaci a kan iƙirarin da ake yi cewa gawayi yana ƙara hasken haƙora, domin haka amfani da man wanke haƙora mai sinadarin gawayi yana iya kawo cinyewar haƙorin da ma sauran matsaloli.

Ƙwararru sun bayar da shawarar kula da tsaftar haƙori da kuma wanke baki a kai a kai, domin samun nagartar haƙora da kuma kiyaye cutukan baki masu shafar dasashi.

Alaƙar tsaftar baki da lafiyar sauran sassan jiki

Wanke haƙora da kyau yana da muhimmanci sosai domin kuwa yana rage hatsarin fama da warin baki, da dushewar haƙora da kuma hujewarsu. Haka nan kuma yana taimakawa wajen kare mutum daga cutuka irin su ciwon sikari da kuma bugun zuciya.