Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ina fatan ba ɗiyata ce ta haihu a hannun ƴan bindiga ba'
Ɗaya daga cikin iyaye mata na ɗaliban kwalejin gwamnatin tarayya ta Yawuri da suka rage a hannun masu garkuwa da mutane, ta ce tana roƙon Allah Ya sanya ba ƴarta ce ta haihu a hannun ƴan bindiga ba, bayan da labari ya ɓulla cewa ɗaya daga cikin ɗaliban ta haihu.
Ta faɗi hakan ne lokacin da ta tabbatar wa BBC an shaida masu cewar ɗaya daga cikin ƴayan nasu ta haihu daji.
A watan Yunin 2021 ne wasu ƴan bindiga a kan babura suka kutsa makarantar suna harbi da bindiga, inda suka kwashe ɗalibai kimanin ɗari bayan sun kashe malami ɗaya.
Wasu daga cikin ɗaliban sun dawo gida bayan danginsu sun biya kuɗin fansa, sai dai shekara ɗaya bayan lamarin har yanzu wasu daga cikin su na hannun ƴan bindigan bayan da iyalansu suka kasa biyan kuɗin fansa.
Mahaifiyar da BBC ta yi fira da ita ta ce yanzu mako biyu ke nan bayan da ta yi waya da ɗiyar tata, wadda ƴar SS2 ce a lokacin da aka sace su.
Ta ce “na ji labarin cewar ɗaya daga cikin su ta haihu, hankalina ya tashi. Abin tashin hankali ne a ce ƙaramar yarinyar da ya kamata a ce tana makaranta amma yau ita ce ta haihu. Ina fatan Allah sa ba ɗiyata ce ta haihu ba, duk da cewar ba ina yi wa ƴayan wasu mummunan fata ba ne.”
“Mu (iyayen yaran da har yanzu suke hannun ƴan bindiga) mun yi taro a ranar biyar ga wannan wata kan yadda za mu ƙara matsa wa gwamnati lamba domin ta taimaka mana, kamar yadda suka taimaka aka karɓo fasinjojin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna.”
Matar ta ce ba za ta iya ƙirga dararen da ta kwashe ba tare da runtsawa ba da kukan ta sha tun daga ranar da ta samu labarin cewa an yi garkuwa da ƴarta da sauran ɗalibai.
Yanzu dai an daɗe rabon da gwamnatin jihar Kebbi, ta yi bayani kan halin da ake ciki, wadda ita ce ke tattaunawa da ƴan bindigan.
Yadda aka sace ɗaliban Yauri
A ranar 17 ga watan Yunin 2021 ne ƴan bindiga a arewa-maso-yammacin Najeriya suka sace ɗalbai kimanin 100.
Yanzu haka an samu nasarar karɓo ɗalibai 86, yayin da har zuwa wannan lokaci ɗalibai 11 na hannun ƴan bindigan.
Kwalejin tarayya ta Yauri makaranta ce da ta ƙunshi maza da mata.
Ɗaya daga cikin ɗaliban wadda ta tsero daga hannun masu garkuwar da suka sace su ta shaida wa BBC yadda ta samu ta gudo har da wayar ƴan fashin.
Ɗalibar wadda ta kwashe wata biyu a hannun ƴan fashin ta ce yardar da ta shiga tsakanin ta da masu garkuwar ce ta sanya suka ba ta waya domin ta je neman inda za ta samu sabis ɗin waya ita kaɗai.
Ta ce a wasu lokuta sukan ba ta damar yin magana da iyayenta ta waya, a mafi yawan lokuta sukan umurci ɗaya daga cikin su ya bi ta wurin da za ta samu damar yin wayar, amma bayan wani lokaci sai suka amince da ita, sukan bar ta ta tafi ita kaɗai.
“Saboda haka, a ranar wata Asabar lokacin da na je neman sabis, sai ina ta tafiya, har na yi nisa da inda suka ajiye mu, daga nan sai na gudu na shiga garin Ɗansadau, a nan ne ƴan sanda suka gan ni.”
“Na faɗa wa mahaifina, sai ya ce min na miƙa wa hukuma wayar saboda su yi amgfani da ita wurin samun bayanai, abin da na yi ke nan.”
Ɗalibar ta kuma bayyana mana damuwar da ta shiga saboda mutuwar ƴar uwarta a hannun ƴan bindigan.
Ta ce “baƙin cikin ba zai taɓa fita daga raina ba, ƴar’uwata tana fama da ciwon Asthma (wahala wurin lumfashi), saboda haka tana buƙatar kula ta musamman. Yanzu dai kawai ina fatan cewa mutuwa ta zama mata hutu.”
Ɗalibar ta ce masu garkuwar suna ba su hijabi da abinci, kuma masu son yin salla da tabarmar da za su yi salla.
“A lokacin da suka gane cewa na iya karatun Qur’ani sosai, sai suka ce na rinƙa koya masu.”
“Wannan ne ɗaya daga cikin abin da ya sa suka aminta da ni har suke bari na ina ɗaukar wayarsu domin na yi waya.”
An saki dukkanin fasinjojin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna waɗanda aka yi garkuwa da su
A watan da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta samu damar karɓo sauran mutane 23 waɗanda mayaƙan Boko Haram suka sace lokacin da suke cikin jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris.
A wata sanarwa da ta samu sa hannun sakataren kwamitin da gwamnati ta kafa domin karɓo fasinjojin, gwamnati ta ce an karɓo su ne ranar Laraba, biyar ga watan Oktoban 2022, kimanin wata shida bayan yin garkuwa da su.
Sanarwar ta ce an samu nasarar karɓo su ne ta hanyar haɗin gwaiwa da aka samu tsakanin sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro, da kuma ma’aikatar sufuri ta ƙasar.