Waiwaye: Cikar Najeriya shekara 64 da kifewar kwale-kwale a jihar Neja

Lokacin karatu: Minti 3

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

A ranar Talatar makon ne Najeriya ta cika shekara 64 da samun ƴancin kai, inda aka gudanar da shagulgula domin murnar ranar.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima sun yi bikin na Ranar Ƴancin kai ne a fadar shugaban ƙasa.

Cikin sauran waɗanda suka halarci bikin, akwai uwargidan shugaban Najeriya, Remi Tinubu, da Sanata Godswill Akpabio da kuma Nuhu Ribadu.

An yi zanga zangar matsin rayuwa a Najeriya

A ranar Talatar ne dai ƴansandan Najeriya suka tarwatsa masu zanga-zangar adawa da rashin shugabanci nagari a Abuja.

Dandazon matasa ne ɗauke da kwalaye da ƙyallaye suka taru a yankin Utako na tsakiyar babban birnin ƙasar suna yin waƙe-waƙen "yunwa muke ji", da "a kawo ƙarshen rashin shugabanci nagari".

Babu daɗewa ƴansandan da ke wurin suka fara harba musu barkonon tsohuwa.

Masu zanga-zangar sun tsara nuna ɓacin ransu ne a ranar da ake bikin cika shekara 64 da samun 'yancin kan Najeriya.

Kwale-kwale ya kife da mutane a jihar Naija

A ranar Talata ne wani kwale-kwalen ɗauke da mutane da kaya ya kife a madatsar ruwa ta Jebba a garin Gbajibo da ke ƙaramar hukumar Mokwa ta jihar Naira.

Kwale-kwalen wanda ya taso daga Mundi zai tafi Gbajibo domin halartar bikin Maulidi cike yake maƙil da mata da ƙananan yara.

Ko a watan Satumban 2023, an samu kwatankwacin irin wannan, inda kwale-kwale ɗauke da fasinja 50 ya kife kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 24 a jihar.

Abin da ya sa muka kori Seaman Abbas daga aiki – Rundunar soji

A cikin makon ne dai Rundunar tsaro ta Najeriya, ta yi ƙarin bayani game da dalilan sallamar sojan ruwan nan Seaman Abbas Haruna daga aiki.

A wajen wani taron manema labarai da ta kira a Abuja, hedikwatar tsaron ta ce an sallami Seaman Abbas daga aiki ne bayan wata kotun soji ta same shi da wasu laifuka uku da ake zarginsa da aikatawa.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar tsaron ta Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya shaida wa BBC cewa, Seaman Abbas, ya yi wasu abubuwa na rashin ɗa'a.

Shugaba Tinubu ya fara hutun makonni biyu

A ranar Laraba ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tafi ƙasar Ingila domin hutun mako biyu, wanda yana cikin hutunsa na shekara.

Mai bai wa shugaba Tinubu shawara kan harkokin watsa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya ce shugaban zai yi amfani da damar wajen yin nazari a kan muhimman matakan da ya ɗauki a gwamnatinsa, musamman ta ɓangaren inganta tattalin arziki.

Bayo Onanuga ya ce shugaban zai dawo domin cigaba da gudanar da mulki da zarar hutun ya ƙare.

Atiku ya buƙaci a mayar da mulkin Najeriya na karɓa-karɓa

A cikin makon ne dai tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya yi kira da a yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar garambawul domin mayar da mulki na karɓa-karɓa a tsakanin yankunan ƙasar guda shida.

Atiku, wanda shi ne ɗantakarar PDP a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi bara ya kuma yi kira da a mayar da shugabancin ƙasar ya zama zango ɗaya na shekara shida maimakon zango biyu na shekara huɗu-huɗu.

Atiku ya aike da buƙatar hakan ne ga kwamitin gyara kundin tsarin mulkin ƙasar na Majalisar Dattawa, wanda ya fara zama domin yi wa kundin na 1999 garambawul ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa sanata Barau I. Jibrin, kamar yadda muka kalato daga jaridar Daily Trust.

Haka kuma ya buƙaci a yi gyara a ɓangaren mafi ƙarancin matakin karatun masu neman shugabanci, da sauransu.