Abin da ya sake jefa 'yan Najeriya matsalar ƙarancin wutar lantarki

Asalin hoton, Reuters
'Yan Najeriya sun kara samun kansu cikin matsala ta karancin wutar lantarki sakamakon lalacewar da aka samu daga babban layin samar da lantarki na kasar, a ranar Litinin.
Kamfanonin raba wutar lantarkin sun sanar da katsewar wutar a ranar Litinin din da misalin karfe biyu na rana.
Wannan matsala ta sake kunno kai a Najeriyar bayan watanni da ta auku a watan Satumba.
Da yake tabbatar da matsalar, a wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na X, kamfanin samar da lantarkin na yankin babban birnin tarayya Abuja (AEDC), ya bayyana wa wadanda yake bai wa wutar cewa, matsalar ta faru da misalin karfe 02:02 na ranar, lamarin da ya janyo daukewar wutar a fadin yankunan da yake ba su lantarkin.
Kamfanin ya roki jama'a tare da ba su tabbacin cewa yana aiki da dukkanin masu ruwa da tsaki domin mayar da wutar, da zarar lanyin na kasa ya gyaru.
Ya ce zai rika ba masu mu'amulla da shi bayanai akai-akai game da halin da ake ciki kan lamarin.
Shi ma kamfanin samar da lantarki na Eko (EKEDC), ya fitar da irin wannan sanarwa ga wadanda yake bai wa wutar.
Ya tabbatar wa da wadanda yake bai wa wutar cewa yana aiki tare da abokan huldarsa don ganin ya dawo da wutar cikin gaggawa.
A shekarun baya-bayan nan bangaren samar da wutar lantarki na Najeriya ya gamu da matsaloli da dama, wadanda suka hada da tilasta aiwatar da tsare-tsare da manufofi da suka jibanci wutar lantarkin, da rashin tabbas na hukumar kula da bangaren, da karancin samun iskar gas da sauran matsaloli.
Duk wani kokari da aka yi na ji daga bakin hukumomin da lamarin ya shafa game da matsalar ya ci tura.
'Yan Najeriya da dama musamman masu kananan sana'o'i da suka dogara da wutar lantarkin wadanda ba su da wata hanya ta samun wutar lantarkin na kokawa a kan matsalar ta rashin wutar lantarkin.
Ko da ma kamfanoni da saunran wadanda ke da wasu hanyoyi na samun wutar na kokawa game da sayen mai na injinnasu na samar da lantarkin.











