Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ina samun miliyan huɗu duk wata a TikTok - GFresh
Fitaccen ɗan TikTok kuma mawaƙi a arewacin Najeriya, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da GFresh Al'amin ya ce shi ko kaɗan ba ya jin komai a irin yanayin yadda gudanar da harkokinsa a kafofin sadarwa, domin a cewarsa yana nishaɗantar da kansa, yana nishaɗantar da wasu, sannan kuma yana samun kuɗi.
Gfresh ya bayyana haka ne a zantawarsa da da shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, wanda ya zo tare da matarsa, Maryam Ahmad Yola.
A game da yadda ya fara samun ɗaukaka, mawaƙin ya ce da wahala ya fara harkokinsa har ya kai matakin da yake kai na ɗaukaka.
''Ni ne mawaƙin da yake waƙa ya haɗa kaset na CD ya bi tituna yana tallatawa. Dama can ina da masoya waƙoƙina, da TikTok ta fito kawai sai na ɗaura daga inda na tsaya, inda na cigaba da soki-burutsuna."
Ya ce duk da cewa an fi ganinsa a TikTok a yanzu, ba ya daina waƙa ba ne, "amma kin san ni waƙar gambara nake yi, kuma salon waƙar bai karɓu sosai ba a arewacin Najeriya. Shi ya sa na ga ya dace yanayin ɗaukaka ta in riƙa yin abin da duk duniyar Hausawa yara da manya za su kalla ko su ji su samu nishaɗi, ba sai kananan yara ko matasa ba kawai. Shi ya sa na fara soki-burutsu, ina nishaɗantar da kaina, sannan ina nishaɗantar da miliyoyin mutane."
Al'amin ya ƙara da cewa shi yanayinsa ba mutum ba ne da yake so ya ga an zauna shiru, "ko bakina da wahala in zauna ba na cin komai."
Ya ce ko matarsa a TikTok suka haɗu, "ta ce ina birge ta, na ce ta buɗe bidiyonta, da na ganta na ga tana da kyau sai muka fara magana, a haka muka shirya, har aurenmu ya ƙullu."
Da aka tambayi matarsa kan yadda yake gudanar da harkokinsa a gida, ta ce a gida mutum ne mara fushi, kuma ya iya tarairaya, "ko da ni na yi laifi sai ya ce in yi haƙuri rayuwa sai a hankali."
Kuɗin da yake samu
Gfresh ya ce ba ya jin kunyar komai a bidiyon da yake yi saboda yana samun kuɗi, kuma yana samun nishaɗi.
"Har Fatakwal na je na tallata kaset ɗina. Idan ban ji kunyar tsayar da mota in tallata kaset ɗina ba, me zai sa in ji kunyar yin abin da zan samu kuɗi in rufa wa kaina asiri?"in ji shi.
A game da irin kuɗin da yake samu, Gfresh ya ce yana samun miliyoyin naira, amma ya ce matarsa ta zo masa da farin ƙafa, "domin tun bayan aurenmu, samuna ya ƙaru sosai," in ji shi.
Ya ce kafin su yi aure yana samun kamar naira miliyan biyu duk wata a TikTok, "amma tun da muka yi aure, yanzu ina cire kimanin naira miliyan huɗu ko sama da haka a duk wata."
A game da batun cewa ko zai rage wasu abubuwa ganin yana da iyali, sai ya ce yana da yaro Khalid, "kuma a wasu lokutan ma shi yake riƙe min kyamara idan zan ɗauki bidiyo. Ina yi muna wasa da dariya."
Ya ce shi tsiraici ne kawai bai yarda ya nuna ba, amma shi ba ya jin komai wajen gudanar da harkokinsa.
Ku latsa nan domin kallon cikakken shirin a dandalinmu na YouTube.